← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 168

Sashe 147

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A yanzu haka ƙoƙarin buɗe wani branch ɗin yake yi. Shi dai a rayuwa babu abinda zai ce sai Alhamdulillah, yasan da ace har yanzu yana gaban Badaru ba lallai ya tsaya da ƙafafun shi yadda yake a yanzu ba, watakila da har yanzu yana nan yana paintings ɗin da kaso saba'in cikin ɗari na abinda yake samu na Badaru ne, abinda yake bashi bai wani taka kara ya karya ba wanda a ciki yake yin duk wasu buƙatun shi har ma ya ɗauki nauyin Umma da kuma ƙannenshi.
Abu ɗaya ya kasa mantawa a cikin shekara ɗayar nan data wuce shine Zainab da soyayyarta, har yau ya kasa cireta daga cikin ranshi gashi ko kiranta yayi a waya baya samunta, ba sau ɗaya ba dau biyu ba yaje har gidansu sai mai gadi yace mishi bata nan tayi tafiya idan kuma ya tambayeshi inda ta tafi sai yace shima bai sani ba sai dai har yau bai cire rai da sake dawowarta cikin rayuwarshi ba hakan nema yasa ya kasa bawa wasu matan damar shiga rayuwarshi don a yanzu da Allah ya azurtashi sai ya zamanto ko nakasar tashi ba'a kalla shi ɗin dai kawai matan suke kallo ko kuma yace ƴan canjin hannunshi suke kallo, sai dai kuma sun makaro domin babu wani sauran gurbin ƴa mace a cikin zuciyarshi gaba ɗaya Zeey ta kankane tayi kaka gida, babu wata ƴa mace da yake iya kallo da sunan soyayya.

Ƙarfe huɗu yake tashi daga shagon yana tattare cinikin da suka yi a ranar saboda ya kai banki kafin ya wuce gida, duk da mafi yawancin customers ɗin sun fi yi musu transfer akwai waɗanda suke basu cash to baya son barin kuɗi a shago shi yasa duk yamma sai ya fara biyawa banki ya ajiye kuɗin kafin ya wuce gida shi da Tanimu da yake tuƙa Baqeer ɗin duk inda zai je a motar Baqeer ɗin, sai ya kai shi gida sannan ya koma shagon sai wajen ƙarfe tara sannan ya rufe gaba ɗaya a tashi daga aiki.
Shi Baqeer baya zama ya kuşan dare idan ba aiki ne dasu da yawa ba saboda bai cika son yana yin nisa yana barin Dada ba saboda tsufa da take ƙara yi kullum abubuwa da yawa da take iya yin su a da yanzu bata iyawa.
Baqeer ya gyara gidan Dada sosai ya ɗaukar mata mai aiki da take yi mata ƴan aikace-aikacen gida tana kuma zama da ita kada kaɗaici ya daneta bare da ba cika zama yayi a gidan ba. Haka nan ya wadata Umma da duk wani abu da zata buƙata sai dai gidan ne tunda ya bar shi ko layin gidan bai ƙara taka ƙafarshi yake ba, su Abu da Jamila suyi ta surutun a ina Umma take samun kuɗin da take kashewa bayan ita ba sana'a take yi ba, wani lokacin idan gulmar ta ciyo su sai suce suna ganin kuɗin filin da suka sayar ne har yanzu basu gama cinyewa ba suke ci da kaɗan-kaɗan shi yasa kullum bata rasa abun ɓatarwa. Ita dai tana jin su ko kallonsu bata yi domin bata da lokacin tsayawa biyewa shirmensu. Babu yadda Baqeer bai yi ba ta bar gidansu taƙi sai dai akwai plans ɗin da yake yi yana kammalawa zai je ya ɗauketa daga gidan dan yasan tun tasowarsu take haƙurin zama a ciki ba ga mai gidan ba ba ga abokanan zamanta ba kowa ba daɗinsu take ji ba.

*****
Sosai Zainab take jin daɗin zama a wajen Ummi bare da Ummi take janta a jiki, duk wani aiki idan zata yi zata sakata a gaba suyi tare, tun tana kwaɓawa har da kaɗan-kaɗan tazo ta fara iyawa. Sabuwar tarbiyya Ummi ta yiwa Zeey duk da take da kyakkyawar zuciya tana da rashin tsoro da faɗin duk abinda yazo bakinta bata duba girma ko shekarun mutum duk yadda magana tazo bakinta haka zata kwaɓa mishi ita. Akan haka sai da Ummi tayi da gaske da yawan faɗa da nasiha kafin ta samu ta daina.
A harkar kitchen ma babu laifi ta iya abubuwa da dama don a yanzu wai har Ummi ta fita ta bar mata girki tayi kuma ya ciyu babu wani gyara, haka nan ɓangaren kula da gida da tsaftarshi yanzu duk Zainab ta iya. Sai take jin rayuwarta wata daban da wacce take yi da, ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali komai tana yin shi cikin ɗa'a bata yin abu da graje kamar yadda take yi ada. Tunani ɗaya ne ya kasa barin ranta shine na Baqeer, duk tsawon wannan lokacin bata manta dashi ba haka yasa taƙi bawa duk manemanta dama, har a cikin cousins ɗinta da yawa sun ce suna sonta taƙi amincewa saboda ta riga ta ƙudurce a ranta idan har ba Baqeer ba bata ga wanda zata aura ba, akan hakan ne ma suke yawan samun saɓani da Ummi don a yanzu burinta taga auren Zainab ɗin ita kuma tace idan har ba za'a aura mata Baqeer ba ta haƙura da auren.

Lokaci zuwa lokaci take ƙiran Daddy a waya amma daga gaisuwa babu abinda ke ƙara shiga tsakaninsu, ko ta neme shi da hira ma baya amsawa haka zata yita takale-takalen zancenta ta haƙura saboda baya amsa mata saboda haushin yadda ta kunyata shi a wajen mahaifin Junaid bayan sun gama magana tasa ƙafa ta bar gidan ta kuma cewa Junaid ɗin lallai yaje ya faɗawa Babanshi ya janye don baza ta aureshi ba, mahaifin nashi da kanshi ya kirashi yace abar maganar kasai tunda dai yarinya bata so.
Shi kuwa Kabir kota ƙira shi ma baya amsawa saboda haushinta da yake ji na yadda ta zaɓi Ummi akan Mummy da tasha wahalarsu a faɗarshi, yadda Mummy take langwaɓe mishi tana nuna shi da Zainab ne farin cikinta don Allah kada ya guje mata kamar yadda Zeey ta gujeta hakan yasa yake ƙara jin haushin Zeey ɗin akan abinda tayi shi yasa ko ta ƙiranshi a waya tai baya amsawa.

Zaune akan doguwar kujera a parlour tana danne-danne a waya, Instagram ta shiga tana kallon hotunan ɗinki da Baqeer ya ɗora a pg ɗin shi, bi take yi tana scrolling through wani farin ciki na ratsata idan ta kalli hotunan taga wai wannan aikin Baqeer ɗinta ne, Baqeer ɗin da ake yiwa kallon nakasashe wanda ba zai iya amfanar kanshi da komai ba yau gashi yayi setting up business ɗin da ba kowa ne zai iya ba. Wani alfahari take ji ganin yadda kullum ƙara haɓaka yake yi yana samun karɓuwa kamar shi kaɗai ne tela duk wani mai ji da kanshi a kuɗi da harkar gayu to kayan *MOHBAQ* ne abun tu'ammalin shi. Manyan mutane da yawa a wurin shi suke ɗinki, wannan kaɗai abun farin ciki ne a wurinta na ganin yadda rayuwarshi tayi changing for the better.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar*
Da
*Ayusher Muhd*

*BAQEER*
*NA*

*UMM ASGHAR*
DA
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA ƊAYA*

{91}
Chapter 147 · 0% Book details