← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 168

Sashe 89

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

***
Washe gari kamar wasa mutanen nan suka ce yaje Aroma cafe, nan yai shigarshi cikin hadadiyar shadda wanda ta sa kyansa kara fitowa, hula ya saka ya sa agoggo da takalmi, nan fa ya fito Muhammad Baqeer dinsa, Salim cikin atamfa ya shirya kasancewar ba mota a hannunsu yasa Salim yace zai tambayi Zainab, sai dai Baqeer kai tsaye ya hanashi yace gwara su nema ko suyi haya amma ba gunta ba, dariya Salim yai yace “Naga fa alama ƴar kunya kukeyi yanzu fisabillahi da mu samu motar bati gwara a sa mu biya?”
Gefe Baqeer ya kalla yace “Kuma ko kunya mu kuma sai mu tabe da aran motarta, to Allah a’a ko kuɗin iya kacinsu kenan gwara mu bada.” Baki Salim ya buɗe yace “Hmmm ai sai muyi kallo daga gefe tunda kunfi kusa.” Baqeer sam bai maida hankali kan me yace ba sai da wasu dakiku suka wuce sannan ya fahimta da sauri yai gyaran murya yace “Munfi kusa a ina kenan?”
Waya Salim ya ɗauka ya fito yana cewa “Wai a duba a gani ko?” Yana kaiwa nan yai waje, Baqeer yai dan tsaki yace “Shidai kullum in baiyi zolaya ba baijin dadi,” sai kuma yai jimm da gaske sunfi kusa kamar yanda Salim yace? Baisan sanda ya dan motsa leɓensa ba, Salim bai da de sosai ba ya dawo nan sukawa Dada sallama suka fita dan ita kanta bai faɗa mata inda zasuje ba.
Sunje cafe ɗin suka tarar bai zo ba, minti biyar sukai Baqeer jiki a sanyaye yace “Salim mu tafi dan Allah.” Kallanshi yai yace “Ko mu ɗan jira?” Kai ya girgiza yace “Ba amfani dama can ban yarda zasuzo ba ko ka manta me ya faru?”
Salim jiki a sanyaye ya kalleshi zaiyi magana sai ji sukai ance “Muhammad?” Kallansu yai dan haka yake amfani a IG saboda baisan a ganeshi, matashin saurayin ya ƙara so ya mika mai hannu suka gaisa yace “Sunana Nasir, wanda mukai magana.” Zama yai suka ƙara gaisawa sannan Salim ya gabatar da kanshi akan shine manager na Baqeer, haka suka zauna akai reviewing contracts ɗin, Baqeer yace a canza wasu abubuwan nan shima Nasir ya ƙara gyara abinda suke so, a ƙarshe Baqeer yace sai sunsa contracts din na shekara ɗaya sannan in za’a sake renewing dole sai dai in su duka bangarorin biyu sun yadda za’ai, nan suka amince aka sa hannu, Nasir sosai ya ƙara gamsuwa da Baqeer dan yanda yake magana kaɗai zakasan yanada talent sosai, anan ya fito da wayarshi ya sake nuna musu wasu zanuka da yai aka ɗin ka, sannan yace dan yana basu zane bazai hana wasu ba, suka amince akan sai dai kar ya bawa wasu irin nasu, cike da jin daɗin handa komai ke tafiya daidai Salim ke kallansu sai hamdallah yake a cikin ranshi, a kuma nan suka biya Baqeer 50k ɗinshi na duk wata sannan suna jiran zane guda goma, zasu bashi rabi in yai zana 5 sannan su bashi ragowar kudin in ya zana ragowar, nan sukai order na drinks suka sha sannan sukai sallama kowa hankalinshi a kwance.
Salim yana ajiyeshi ya juya dan yabar shago a kule, Baqeer ne ya kalli Dada sannan ya sanar da ita abinda ke faruwa, guda ta shiga yi ji take kamar ba wanda yakaisu farinciki tace “Baqeer lalai idan Allah ya tsara bawa zaiyi arziki ko mutane zasu haɗu su hanashi sai Allah ya tada shi.” Murmushi yai yace “Dada ba komai kaddara ce sai dai a yanzu na gane kaddarar nan itace tasa na gane kaina, na gane mutanen dake tare da ni sannan na tashi na nemi abu da kaina bawai da taimakon Baba ba, ada na ɗauka yafi sona akan kowa na duniyar nan, wanda har nake shakkar san da yake min yayi yawa yana rufemai ido da bai ganin laifina sai dai yanzu na gane.” Tausayin Baqeer ne ya kamata tana gani ya wuce ɗaki, laptop ɗin daya siya ya buɗe irin ta zane mai pencil a jiki, bai ma da de da siyanta ba, har zai fara sai kuma ya ciro wayarsa, number Zee ya kurawa ido haka kawai yakeji yana san sanar da ita abinda ya faru, shiru yai yana tunanin ta yanda zai fara sai ya mata text ‘A dawon da abuna da aka ɗauka." A lokacin Zeey na kwance kan cinyar Mumy suna kallo ita kuma tana daddana waya, Nabeela na zaune daga gefe tayi shiru tana tunani. Ganin sakon Baqeer yasa ta mike zaune da sauri ta karanta, murmushi tai ta rubuta “Nace sai an ban hakuri.”
“To ai laifin hakurin ne ban san nayi ba.”
Ɗaki ta shige ta faɗa kan gado tace “Ka ƙira na faɗa ma mai kai.” Kallan wayar yai ta turo “Allah ka ƙira!” Yanzun ma kallan wayar yai kai ya girgiza sannan yace “Reason?”
Smiley’s ta turo na rike baki tace “Haka kace? Shikenan.”
Kiranshi tai ya girgiza kai yana murmushin da shi kanshi bai sani ba ya ɗaga “Inalilahi!” Kawai abinda tace kenan ta kashe, hankalin Baqeer ne ya tashi cikin sauri ya ƙirata, tana ɗagawa yace “Lafiya? Meya faru?murmushi tai tace “Hmm haka ake so.” Sai a lokacin ya gane me yake nufi kamar zai yi magana sai ya fasa “Me ya sani a kanta? Shi komai nashi ta sani shifa? Ko cikaken sunanta bai sani ba, kawai jiyai bai kamata ya faɗa mata ba, cikin wata murya yace “Ke kaɗai ce a gida?” Hankali a kwance tace “A’a yayana baya nan, to ni da Mumy na ne sai sister ɗinta, Dady ma bai nan.”
Kai ya jinjina yace “Ku biyu ne kenan?” Nan ma tace eh daga ni sai shi, Mumy tace mun isa. Shiru suka ɗan yi tana mamakin tambayar datazo kai tsaye, zatai magana taji yace “Maryam fa? A makaranta kuka haɗu?” Gabanta ne yai wani irin faduwa me Ya Baqeer yake tambaya? Me yake san tace? Kalamansa ne suka sake katse ta dayace “Secondary ko FCE?” Muryarta ce ta ɗan sarke………

Umm Asgar Ce
Da Ayusher Muhd

*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA BIYAR*

{55}
Ta buɗe baki ta rufe ta sake buɗewa ta rufe ta rasa ma amsar daya dace ta bashi, to ita a yanzu tace mishi a ina tasan Maryam bayan har yau bai gane wacece ita ba. Kasa bashi amsa tayi sai cewa tayi "kun yi waya da Umma?" Tana lafiya dai ko?" Ɗan murmushi yayi yana jin wata irin nutsuwa tana ratsa zuciyarshi, yadda Zeey ta damu da Umma abun yana yi mishi daɗi. A shagwaɓe tace "Ya Baqeer," sai da yaji ƙiran sunan nan har tsakar kanshi. Gyaran murya yayi yace "tana nan lafiya, baki je kin ganta ba?" "Na kwana biyu ban je ba amma In Sha Allah zan samu time naje na dubata, kasan fa yanzu mune idanunka dole mu dinga kai ƙafa akai-akai tunda mun san yadda Umma take a wurinka," ta ƙarashe maganar cikin kwantar da murya kamar tana gabanshi. Haka nan take jin wani farin ciki yana ratsa zuciyarta, ta rasa lokacin da hakan ya faru amma a yanzu ta tabbata ba zata iya rayuwar da babu Baqeer a cikinta ba. Sun daɗe suna hira wacce fiye da rabinta tsokana ce suke yiwa junansu. Bayan sun gama wayar Zainab ta kwanta rigingine tana kallon ceiling tana sakin wani ƙayataccen murmushi, so kawai take yi ta ganta a gaban Baqeer sai dai bata cika so tana yawan zuwa wurinshi ba a yanzu kada ya zamanto kullum ita take kai ƙafa ya kamata ace ko yaya ne shima yana kawo mata ziyara idan fa har suna son taking relationship din su to another level. Kaji Zainab dai wai relay, dama kuna relationship ne? Tayi wa kanta tambayar data kasa bawa kanta amsa tunda dai tasan Baqeer bai taɓa furta yana sonta ba yanayinshi ne yasa take ganin kamar shima yana sonta kamar yadda take son shi.

*****
Chapter 89 · 0% Book details