Sashe 40
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin wulaƙantaccen kallo tayi mishi tare da sakin tsaki, ita duk sai taji ranta ya ƙara ɓaci ma ajinta ya zube ƙasa warwas idan har wannan mahaukacin zai iya tararta ya buɗe baki yace yana sonta ba tare daya duba ɗumbin tazarar dake tsakaninsu ba. Cikin fusata tace "Dallah mallam bana son hauka, tun wuri gara ka kauce ka bani wuri na wuce ko kuwa kaga nayi maka da mai taɓin ƙwaƙwalwa irinka da zaka zo ka tareni a titi kana yi mini soki burutsun zance mara kai bare ƙafafu?"
Shi kuwa duk hargagin da take yi bai ma san tana yi ba sai ma kallonta yake yi cikin shauƙi yana jin wata iriyar soyayyarta na ƙara ratsa dukkanin wasu sassa na jikinshi. Yau dai gashi ga Roshni a tsaye, sakarar zuciyarshi ma sai take ayyano mishi ai kallon soyayya take jifanshi dashi don haka yake ta washe mata haƙora shi a dole murmushi yake yi. Ganin ɓata lokacin ta kawai take ƙara yi da tsayuwa a wajen wannan mahaukacin yasa ta koma cikin motarta ta tasheta da nufin idan har bai matsa ba tabi ta kanshi kawai ta wuce sai dai duk abinda zai faru ya faru amma ba zata tsaya tana cigaba da jin zantukan bakin mara hankalin nan ba.
Sai da yaga ta nufo kanshi gadan-gadan kamar zata bugeshi sannan ya matsa yana cewa "A’a Roshni ya zaki tafi kuma bayan muna hirarmu ta soyayya gwanin daɗi?" Bin bayan motarta yayi da kallo yana jin tamkar ta tafi da wani ɓangare na zuciyarshi, sai da ya daina ganinta sannan ya nufi motar Baba da Abu tasan ƙulunboton da tayi har ya bashi aro ya buɗe ya shiga yana jin kanshi on top don yau yayi dacen haɗuwa da Roshni don ma basu samu sun zanta sosai kamar yadda shi yaso ba amma dai babu damuwa zuwa anjima zai je gidansu ya sameta yadda zai ƙara kafa kanshi sosai.
*****
Bayan wucewar Zainab ne Dada ta ƙara ɗauko abincin Baqeer data mayar kitchen ta ajiye ganin yaƙi buɗe ƙofa ya karɓa ta nufi ɗakin da yake. Ƙwanƙwasa ƙofar tayi tace "Yanzu saboda Allah Baqeeru ba zaka buɗe ƙofar nan ka fito ba? Ga abincinka nan tunda zafinshi nake bin kan ka kazo kaci gashi yanzu har ya huce, ayi rayuwa a haka ace bawa yayi ta zama da yunwa, shikenan don Allah ya jarabceka da wata ƙaddara sai ka shige ɗaki ka ƙuntata rayuwarka maimakon ka gode mishi bisa tarin ni'imomin da yayi maka sai kuma kake nema ka butulce mishi saboda ya jarabci rayuwarka don ya gwada imaninka, wannan wacce irin rayuwa ce da bawa ba zai karɓi ƙaddara a duk yadda tazo mishi ba?”
Ga mamakinta sai gani tayi Baqeer yazo ya buɗe ƙofar ɗakin ya miƙo hannu ya karɓi kwanon abincin nashi da tuni ya huce. Miƙa mishi tayi ta juya tana cigaba da ƴan mitocinta akan rufe kanshi a ɗaki da yake yi.
Shi kuwa maganganun yarinyar nan ne suka tsaye mishi a rai yake ta faman juyasu a cikin ranshi inda take cewa "Haka zaka cigaba da rayuwa baka duba mutanen dake rayuwa tare da kai suka damu da damuwarka? Sai maganar wasu ƙalilan da basu san ciwon ka ba basu damu da kai ba zaka ɗauka ka saka a rai?" Shi yasa yaji ba zai iya ƙyale Dada tana maganganunta ba shine kuma yasa shi buɗe ƙofar ba tare daya shirya wa hakan ba. Gara kekenshi yayi ya koma cikin ɗakin ya tasa abincin a gaba yana kallo, tun asali shi ba mai son cin kowanne irin abinci bane shi yasa ma Umma ke yi mishi girkin shi daban don baya iya cin girkin su Abu saboda daga ita har Jamila basa iya tsayawa su gyara girkinsu saboda maigidan ba wani kuɗin cefanen kirki yake bayarwa ba su kuwa kowacce na ƙyashin ta cire daga aljihunta ta ƙara yadda za'a yi wadataccen abinci mai kyau, dama Umma ce bata ƙyashin gyara girkinta bare kuma da Baqeer ɗin yake tsaye akan al'amuranta bata nemi komai ta rasa ba shi yasa yaran gidan har ɗokin zagayowar ranar girkinta suke yi don sun san zasu ci abinci mai daɗi ba kamar na iyayensu ba.
Haka nan ya daure ya tuttura abincin gashi aka yi rashin sa'a wake da shinkafa ba cimar da yake so bane sai dai kuma a yanzu dole yayi haƙuri da duk abinda ya samu tunda dai bai kawo ya ajiye ba bare yayi zaɓen abinci. Ko rabi bai ci ba ya mayar da murfin ya rufe ya samu wuri ya ajiye kwanon, ƙishirwa yake ji sai dai duk ɗakinshi babu ruwa shi kuma yana jin ƙyuiyar ya buɗe baki yayi magana bare ya cewa Dada ta kawo mishi ruwan. Kallon tsakar gidan yayi ya hango randar ruwan Dada mai ɗan karen sanyi daga can hanyar fita daga gidan sai dai baya jin zai iya kai kanshi tsakar gidan bare ya ɗebi ruwa ya sha. Rufe idanunshi kawai yayi ya buɗe yana ƙara kallon wajen da randar take yana ƙara ganin nisan wurin daga nan inda yake zaune, kamar Dada tasan ruwan yake da buƙata sai gani yayi ta nufi wajen randar ta ɗebo ruwan ta kawo mishi. Karɓa yayi ya kafa kai ya sha bai ajiye ba sai da ya shanye ruwan nan tas dama ya daɗe yana son shan ruwan ya buɗe baki yayi magana ne yake ganin asara. Hannu yasa ya gara keken wajen katifar da yake kwanciya sannan yasa hannayenshi duka biyun ya daddafa ya sauka daga kan keken ya koma kan katifar ya kwanta yana murza hannunshi na dama inda ya samu karaya, duk da likita yace hannun ya warke zai iya yin komai dashi kamar da har yanzu yana jin ciwo a wurin bare daya kasance har aikin da ƙafarshi zata yi yanzu hannayen ne ke yi.
*****
Tana ji tana gani haka ta cire kujerunta ta sayar, sauƙinta ma ƙawarta data saya ta sayesu da daraja. Tunani ta zauna tana yi to yanzu wacce sana'a ya kamata ta kama don fa ba zai yiwu ta saka kuɗi a gaba su cinye ba alhalin basu da mataimaki sai Allah, duk da ƴan uwanta na cikin wadata tasan zai yi wuya su tallafe ta don dukkansu daga su sai iyalin su sai ko Dada da suke yiwa aiken kayan abinci lokaci zuwa lokaci, tun can asalinta ma Allah bai yita mai kwaɗayin abun hannun wasu ba shi yasa bata taɓa nufar ƴan uwan nata da nufin su taimaka mata ba sai kuma tayi dace da samun ɗa ɗaya tamkar goma daya ɗauke mata dukkanin wasu larurorinta yake yi mata hidima bakin gwargwado daga ita har ƴan uwanshi basu nemi komai sun rasa ba sai fa yanzu da Allah ya jarrabce shi da larura duk da ma dai akwai kuɗaɗen shi a wurin Mallam don duk abinda ya samu shi yake karɓa yana juyawa don yace ba zai yiwu abar kuɗaɗen haka ba a juyasu ba, a yanzu kuwa tasan bata isa ta tambaye shi batun waɗannan kuɗaɗen ba don tasan dai ba bayarwa zai yi ba sai dai ma ranta da zai ɓaci a banza.
Wayarta ta ɗauka da nufin kiran Hadiza suyi shawarar yadda za'a yi da kuɗin da irin sana'ar daya kamata ta fara sai kuma ta tuna ashe fa babu waya a hannun Hadizar tunda tata ce ta barwa Baqeer ba kuma lallai ne ta samu ta sayi wata ba tunda tasan halin matsin da take ciki gashi sanda Maryam taso bata daga komawa gida tasan mijin ne ya hana. Maryam ta kira a maimakon Hadizar sai taji muryarta tayi sanyi ƙasa-ƙasa kamar wacce ke cikin damuwa. Hankalinta ne taji ya tashi ta hau jerowa Maryam ɗin tambayoyin ko lafiya suke? Jin muryar mahaifiyarta kawai sai tasa kuka, yi take yi babu ƙaƙƙautawa Umma na jinta bata katseta ba sai dai yanayinta gaba ɗaya ya canja ta tsinci kanta cikin damuwar itama. Sai da tayi kukanta ya isheta sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya. "Ki cigaba da haƙuri Maryam komai mai wucewa ne watarana sai kiga kamar ba'a yi ba sai dai a labari, kin ji?” tayi mata maganar cikin tausasawa ba tare data buƙaci jin abinda yasa ta kukan ba tunda dai tsakanin harshe da haƙori ma ana saɓawa tasan ba zai wuce tsakaninta da maigidanta bane.
Ajiyar zuciya ta sauke tana share hawaye tace "Umma zaman gidan nan ya isheni, ana samun matsala da uwar miji ni uban miji ne matsalata, babu dama ya ƙyalla ido yaga muna zaman lafiya da Baban Aareef sai yasan yadda yayi ya wargaza zaman lafiyar nan, ko wani alheri Baban Aareef yayi niyyar yi mini sai ya hana yanzu motar da aka saya mini saboda kai Aareef makaranta da ɗaukoshi yasa ya karɓe saboda wai idan yasa ƙafa ya fita yawona nake ficewa nima bana zama ko Aareef ɗin ma bana zuwa na ɗauko saboda kawai rannan nazo na ɗauki Yaya Baqeer na kai shi wajen Dada kuma wallahi Umma daya dawo sai da nayi mishi bayanin abinda ya faru amma mutumin nan ya juyar da magana ya zuge ɗanshi ya karɓe makullin motar daga hannuna, da nace mishi to Aareef ɗin fa ya za'a yi da kai shi makaranta da ɗaukoshi sai cewa yayi wai ai makarantar bata da wani nisa sai na dinga zuwa a ƙafa ina kai shi ina ɗaukoshi don nace ni dai gaskiya ba zan iya ba sai dai ko ya ɗaukar mishi mai napep shine yace ai gidanmu ma dai yaga ba motar ce damu ba da har zai ce ga yadda za'a yi zan yi mishi gardama saboda na samu wuri.”