← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 168

Sashe 33

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baqeer kuwa har suka isa gidan baice komai ba don shi kanshi bai son zama a gidan su kuma yanzu ya tattara rayuwar ya ajiyeta, me zai yi a cikin duniyar nan? Baba ya juya mishi baya, zanenshi ya tafi, Asiya daya gina rayuwa da ita ta juya mishi baya, Bello amininshi, sannan Salim dake rage mishi radadi an rabasu to me yayi saura?

😪
Wannan lamari

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*

*BAQEER*
     *NA*
*UMM ASGHAR*
"DA*
*AYUSHER MUHD*

*PAID BOOK*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN*

*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯

08142800199
07068558096

{20}
Dada a garin Mariri take wanda ɗan gefe ne kaɗan da cikin garin Kano, tana zaune a waje tana tsince ragowar shinkafar da take dashi zata ɗan dafa, mace ce mai yawan kyauta wacce duk sanda kaje gidanta zaka taddata bata rabuwa da yan matan dake shigowa suna tayata aiki tana basu dan wani abin, hakan yasa kayan abincinta basa daɗewa, sai dai bata kuma rasa kayan abinci, yayyen Umma maza suna ƙoƙarin haɗa mata kayan abinci bakin gwargwado yadda zai isheta, tunda ta fahimci matan su ba so suke su zauna da ita ba shi yasa tace su barta a gidanta, to da yake suma duk maza ne Umma ce kawai mace sai suka ɗauka kayan abincin kawai da suke bata ya isheta, gashi dama dukkansu babu wanda yayi aure a Kano.
Kamar daga sama ta jiyo muryar Hadiza hakan yasa ta miƙe a hankali tana cewa “Yau kuma Dijangala ce a gidan namu?”
A tsaye ta ganta da gudu Hadiza ta taho ta rungumeta, bayanta ta shiga shafawa tace “Meya faru? Ko mijin naki ne har yanzu abun bai daidaita ba?”
Ta girgiza kai tana share kwalla tace “Dada ya zamu yi?”
Da mamaki take kallonta tace “Name kenan?”
Ta ƙarasa maganar tana leƙa waje kaɗan, a cikin mota ta hango Baqeer a zaune yana kallon ƙofar gidan, tace “Da Baqeer kuke tafe?”
Kafin Hadiza ta samu damar ba ta amsa taga Maryam na buɗe keken guragu, da mamaki take kallonta sai dai haka kawai taji jikinta yayi sanyi, don Baqeer ba zai taɓa ganinta a tsaye ba tare da ya fito da sauri ya gaisheta ba, balle yadda ya kalleta kallo ne na wanda kamar baya cikin ma hayyacinshi, kallo ne na wanda damuwa da takaicin rayuwa suka ma yawa.
Maryam tasa keken daf da gefen inda zai fito tare da buɗe ƙofa, bai ko tanka ba Hadiza da Maryam suka taimaka mishi ya hau kan keken, da sauri Dada tayi baya tana girgiza kai, wannan wace ƙaddara ce ta samesu haka? Kasa motsi tayi har suka ƙaraso dashi cikin gidan, Dada da sauri ta rungume Baqeer ta sa wani kukan tausayi wanda hakan ya ƙara saka Baqeer cikin wani kunci shi kenan kai daga an ganka sai kowa ya hau kuka? Wannan wace irin rayuwa yake ciki? Hannu yasa ya toshe kunnenshi kawai ya fara sakin wani irin kara wanda yasa hankalinsu duka ya tashi, da sauri Dada ta sake riƙeshi tace “Baqeer menene haka? Meya sameka wai?”
Jikinshi ne kawai yake rawa yana sake toshe kunnuwanshi, ganin haka yasa tace akai shi ɗaki, suna hawaye haka Maryam ta tura keken zuwa ɗakin suka fito cike da tausayi, a nan tsakar gida suka zauna a tabarma suka sanar da Dada duk abinda ke faruwa, hankalinta yayi mugun tashi sai dai takaicin Badaru yafi komai damunta, sam dama kowa yasan rashin mutunci da wulakancinshi amma bata taɓa tunanin zai yiwa Baqeer haka ba.
Tace su barshi anan ita batada matsalar mai gyara mata gida don yaran layin har rububin zuwa gyara mata gida suke yi.
Maryam ta buɗe jakarta ta ciro dubu biyun da mai gidanta ya bata tayi cefane ta miƙawa Dada tace “gashi ku sayi wasu abubuwan kafin muga yadda hali zai yi.” Nan ta amsa suka fito bayan sun mata sallama don tace kada su leƙa ɗakin Baqeer don da alama hankalinshi tashi yake yi in yaga an damu da halin da yake ciki.

*****
Maryam a gidan Hadiza ta ajiyeta sannan ta wuce ta makarantarsu Aareef ta ɗaukeshu, ta san tayi lattin zuwa ɗaukarshi shi yasa take ta sauri, tana isa makarantar aka sanar da ita ai mahaifinshi ya ɗaukeshi, ajiyar zuciya tayi sannan ta fito daga ciki ta shiga mota ta koma gida fuskarta sam babu walwala don tasan tabbas yau akwai ɓacin rai, tana shiga ta hango surukinta a zaune a harabar gidan yana karanta jarida, parking tayi sannan ta ƙaraso ta gaisheshi da gida tana cewa “Baffa shan iska kake yi ne?”
Kallonta yayi yace “Kin dawo?”
Ta miƙe tana cewa “Abban Areef fa? Naga banga motarshi ba.”
“To ke da mijinki ni ina zan san inda yake?” Yayi maganar tare da cigaba da karatunshi, miƙewa tayi ta koma ciki, a kitchen ta tsaya ta sauke ajiyar zuciya tana tunanin yadda zata yi girki ba nama tunda dai kuɗin ta ɗauka ta bawa Dada, da sauri ta fara dafa shinkafa da wake, ta yanka kayan miyan da take dashi ta ɗauko kifin gwangwani na mackerels tasa tana yi tana addu’ar Allah yasa kada yayi maganar nama. Daga waje ta jiyo ƙarar buɗe gate ta gyara da sauri tare da ɗan jingina da kofar kitchen tana murmushi, Areef ne ya shigo da gudu ya rungumeta yace “Ummy yau ina kika je baki zo da wuri kin ɗaukeni ba?” Ta shafi kanshi tace “Ka manta Uncle ba lafiya? Naje na dubashi ne, a  ina kuka tsaya naga baku dawo da wuri ba?”
Kafin yayi magana mahaifinshi ya shigo tana murmushi tace “Gwaskana sannu da dawowa.” Babu alamun zai tanka ta a fuskarshi kawai ɗaki ya wuce, bin bayanshi tayi tana tsokanarshi “Yau ka tashi da wuri nayi mamaki da akace ka ɗauki Areef daga school.”
“Don me na saya miki mota?” Kalmar da taji ya faɗa kenan, jikinta ne yayi sanyi tace “Kai Areef makaranta da ɗauko shi.”
“To akan me baza ayi abinda aka siya domin ta ba? Yanzu da Baffa bai kirani ya sanar dani kin fita ba da bazan taɓa tunanin ɗauko yarona daga makaranta ba, tunda dai  ke wayarki bata shiga, sam ni na kasa gane wannan halin naki.”
Zata yi magana taga ya shige toilet, kitchen ta dawo idanunta na neman cikowa da ƙwalla, babu shakka tasan tayi laifi da bata sanar dashi ba amma ya zata yi? Yanayin data shiga ne ya hanata ga wayarta ba charge.

******

Tunda su Daddy suka shigo da abokansa tana ɗaki a kwance, tanaji su Nabeela nata zaryar kai kayan abinci da tarar baki, kamar daga sama taji muryar Kabir yana kwalla mata ƙira daga bakin ƙofar ɗakin, taba daga kwance tace "Menene?"
"Dalla malama ki taso Dady yace kizo ku gaisa da bakin."
Baki ta turo sannan ta zura abaya a saman vest da short ɗin dake jikinta, Mumy ce ta ganta ta saki murmushi tace "Saki ranki mana auta."
Kabir ne ya cukume fuska yace "Karma ta saki ran ni ba sai na farfasawa mutum baki ba."
"Bro please chill kai meyasa kake abu kamar gangster?"
Ai kamar ta taboshi ya fusata yace "What? Wallahi yau sai na karya yarinyar nan."
Kai ta girgiza irin na takaicin halayensa ɗin nan, wannan abu ya tunzurashi sosai sai dai ba yanda zaiyi ya wuce ciki rai a ɓace.
Zeey shiga tai ta tsuguna ta gaishesu, bata wani kallesu ba dan ba kasafai take san kallan mutanen da bata sani ba.
Kamar daga sama taji wani yace "Ai wannan haɗin yayi daidai kaga ita dama bata saba da nan ba shima haka sai su saba tare."
Dady yai dariya yace "Sosai! Na tabbatar hallayarsu zata zo ɗaya in har ya dawo."
Wani ne yace "Wani satin ne ai insha Allahu."
Itadai kanta na ƙasa ta kuma tabbatar abinda take zargi shi suke yi, Dady ne ya sake cewa "Wai Zainab baki ganeshi ba? Mahaifin Junaid ne fa."
Taɗan saki fuska kaɗan tana sake gaisheshi ya amsa yana cewa "Kuna waya kuwa?"
Kai ta girgiza tace "Mun kwana biyu wlh tunda na zama busy shima haka muka daina."
"Masha Allah."
Mikewa tai dan zaman ya isheta, kalaman mahaifin Baqeer duk sun hanata sukuni, burinta kawai taji yanda ake ciki dashi, ba yanda zatai ta fita yanzu dole sai dai gobe, haka ko falo bata fito ba takaicin halin data shiga duk ya isheta, wai akan me ta damu da Baqeer? Kamar ta manta wani Baqeer ɗin ne? Wanda ko hanya ta taho ya taho ta gwammace ta koma? Duvets ɗin data luluɓa dashi taja ta rufe kanta tana ɗan bubuga ƙafa cikin takaici.
Chapter 33 · 0% Book details