← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 168

Sashe 20

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
A hankali Zainab ke buɗe ido tana rufewa, kallon agoggo tayi ganin azahar har tayi yasa ta yin miƙa sannan ta mike, wayarta ta duba ganin missed calls tayi kusan guda goma, tsaki tayi sannan ta duba text ganin saƙo ne daga number ta duba, da alama yaron jiya ne dan bakaken maganganu yake faɗa mata akan ta zubar mishi da mutunci tasa yanzu ana yi mishi dariya.
Baki ta taɓe sannan ta kira number, bugu ɗaya ya ɗauka tana jiyo alamun mutane daga gefe ana cewa "Yess karka barta."
Nabeela ce ta shigo ɗakin ɗauke da kayan da aka aiketa ta siyowa Zeey na lotions ɗinta wai ta manta da nata acan, Zeey tana kallon Nabeela tace "Yes Jamal inaji!"
"Najib!"
"Oh Alhaji Najib!"
"Ki bani haƙurin abinda kika yi mini sannan ki faɗawa friends ɗina wasa muke yi bawai da gaske muke ba."
"Wai dama shine dalilin kiran? Okay! Friends hope kunji? Sannan please Jamal next time in zaka wurin budurwa dress properly, I mean dress like a real guy please." Tana kaiwa nan ta kashe wayar tare da blocking number ɗinshi.
Nabeela ta girgiza kai tana ajiye kayan kan dressing mirror tace "Zeey please ki bar wulakanta mutane."
"Wai gaskiya ce ban isa na faɗa ba? Ni ban wulakantashi ba abinda ke raina kawai na faɗa bana ji kuma laifi ne don nayi hakan"
Shiru kawai Nabeela tayi don tasan ba'a cin Zeey a magana, miƙewa tayi tace "fita zan yi idan nayi sallah, bani car key ɗinki please bana so Dad yasan bana nan ba dadewa zan yi ba."
Kamar zata musa sai kuma ta bata, da sauri ta shiga toilet bata dade ba ta fito ta shirya cikin English wears riga doguwa har gwiwa da wando, tayi sallah sannan ta miƙe tace "Ki zauna a ɗakin please kafin a nemeni in kika ga zata kwaɓe ki faɗawa Mum da wuri, bye."
Bata ko jira taji amsarta ba ta fice. Saman kanta kawai Nabeela ta shafa. ita kam tasan watan maida ita baiwa yayi don Zeey maidata take kamar wata ƴar aikinta bayan ita kanwar mahaifiyarta ce kawai dai Zeey ɗin ta girmeta ne da wata shida.
Zeey tana fara tafiya suka yi kiciɓis da wata mota, kallin juna suka yi cike da mamaki wanda hakan yasa kowa yaja gefe yayi parking, da sauri Zeey ta fito ta ƙara so jikin motar ɗayar, itama ta fito suka rungume juna cikin jin daɗi cike da mamaki tace "Wai ya aka yi kika ganeni? Ashe rai kanga rai?"
Zeey tana dariya tace "Maryama Daso tawa, da gaske dai kece ni kuwa in ban ganeki ba a duniya ai duka za ayi mini, daga ina kike?" Tayi maganar tana kallon bayan motar ganin yaro a ciki yasa ta buɗe baki tace "What?"
Maryam tasa dariya tace "Ehen ke fa?"
"Inalillahi yaushe kika yi aure har dasu haihuwa?"
Dariya tayi tace "Kinsan last mun haɗu dake sanda naje graduation na brother ɗina a Buk to lokacin ban ƙara 1year ba nayi aure."
"Inalillahi I just can't believe it, how?"
"How kamar ya? Ke fa? Kina nan kina neman maganar taki da kika saba?"
Zee zata yi magana suka ji horn daga bayansu sai a lokacin suka kula da yanda Zeey tayi parking, dariya suka yi Zeey tace "I just hate naga mutane ba haƙuri, ya ɗan jira kaɗan mana."
"Madam kin san uzurinshi ne? Halinki na nan dai ashe."
"Hmm share kawai kin ji, Umma fa? Ina Umman mu?"
"Tana nan bayan sam kin manta da ita tunda kuka tashi ko leƙota bakya yi."
Fuska ta tsuke tana juyawa alamar zata tafi tace "Kin dai san dalili ai daga nan kuma ban san ya akayi ba zumunci ya watse."
Dariya sosai Maryam tayi tace "Wai har yanzu baki manta ba? To kizo muje am sure Ya Baqeer na gida ku gaisa shi ya manta."
Tsaki taja tace "Allah ya sauwake ni yaushe rabon dana ganshi ai ko a lahira kowa ya kama gabanshi, nifa banda yayanki ne da ɗan Umma wallahi da...." Sai kuma tayi shiru tana cewa "Zan aika a amsomin numberki wurin Umma tunda muna kan hanya."
Kai Maryam ta gyada nan ta tuno abubuwan da suka faru shekarun baya wanda yasa ta murmushi da girgiza kai kafin ta shiga mota.
Areef ne cikin gwaranci yace "Mamy itama ƙawar kice?"
Ta ɗaga kai tana dariya tace "ƙawata ce sai dai ƙawancen da bai yi nisa ba." Ta ƙarasa tana tada mota cike da mamakin yadda aka yi Zainab ta ganeta da wuri haka wasu abubuwa na sake dawo mata waɗanda ta tabbatar nisantar junansu shine abinda ya kamata.
Nan ta ƙarasa gidansu....

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

#Baqeer 🦼
#MBB
#Asiya
#Rayuwa da Kaddara
#Nakasa
#Hawayen rayuwa

Na Ummu Asgar
Da Ayusher Muhd

*BAQEER*
     *NA*
*AYUSHER MUHD*
           *DA*
*UMM ASGHAR*

*ƊANDANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA UKU*

https://www.tiktok.com/@maims_kiddies
"Lallai Dr irin wannan kyau haka tamkar kunzo daga ƙasar UK? Gaskiya kayan jikin su Hanan sunyi matukar kyau, amma dai ba'a ƙasar nan kuka siya ba?" Cikin dariya Dr Aisha tace. "A ƙasar nan muka siya, sai dai kamar yadda kika ce ɗin haka ne, duk wannan kayan da kika gani a jikin yaran nan na ƙasar UK ne da *@Maims_kiddie* take sai da su a cikin Nigeria, muma a wajanta muka siya kuma ba tare da munje inda take ba, kayan na gani a Instagram account ɗin ta na *KIDS THRIFTY/OKRIKA STORE.* Kayane masu kyau da kwari daki bari kenan malam Khadija dan tun da na fara siyan kayan yara a wajanta shikenan na dena ganin kyawun na ko'ina. Kema/kuma zaku iya nemanta a Instagram link ɗin dake sama. Za kuma ku iya samunta a WhatsApp ta wannan link ɗin dake ƙasa. Ko lambar wayarta.
https://Wa.me//08101378616

Maryam sai data kusa isa gida ta duba jakarta, takaici ne ya kamata ganin naira ɗari biyar ce kaɗai a ciki, ajiyar zuciya kawai tayi tare da yin parking sannan ta fito da Areef suka nufi cikin gidan, tun daga soro zaka jiyo hayaniyar Baba yana magana cikin faɗa, da yake tasan halin Baba sai bata yi wani mamaki ba, ta tabbatar Kamalu ne ko Bashir ko kuma Salihu wani a cikinsu ne ya taɓoshi tunda yara matan gidan daga wanda yayi aure sai wanda suke boarding school. Ta ƙara yin taku ɗaya taji Baba ya ambaci sunan Baqeer, cike da mamaki ta shiga cikin gidan, Hadiza ta hango jikin bango banda hawaye babu abinda take yi, Abu da Jamila suna tsaye daga jikin ƙofar ɗakunan su suna kallon abinda ke faruwa, Umma ce a gaban Baba wanda hakan ya tabbatar mata da Umma ake faɗan, mamaki ne ƙarara ya bayyana a fuskarta jin Baba yace “Kin san Allah Fatima ki fita idona, idan har kika bari na sake magana to tabbas zaki tsinci kayanki dana ɗanki a waje, ni zaku maida soko? Kuna nufin ni da gidana ban isa inyi hukunci ba? To ni nace Baqeer ya tattara ya koma ɗakin Kamalu ya zauna shi kuma Bashir da Salihu su dawo nan, hakan ba adalci bane?”
Fatima ta share kwallarta tace “Bance ba adalci bane amma sai yanzu Malam? Ka manta sanda kasa aka gina ɗakin nan da kaina nace ka haɗa mazan nan bibiyu wuri ɗaya me kace min? Cewa fa kayi Baqeer ba zai haɗa ɗaki ɗaya da kowa ba, kai baka son a dinga ɗauke mishi hankali da shirme gwara yayi zamanshi shi kaɗai zai fi maida hankali akan zanen shi, ko ka manta tsakar gidan mu ka rage ka gina ɗakin saboda shi shi kaɗai? Kayi mishi ban ɗakin shi a ciki?”
“To nace yanzu na janye? Ko ke kika bani kuɗin dana yi ginin? Tunda har yaron nan ya tozartani ya wulakantani kema ai kinsan dole ku kwashi kayanku a hannu ko?”
Zata sake magana ya ɗaga mata hannu yace “Na dai faɗa miki, kima barni naji da yanda zanyi na maidawa Yallabai kuɗin shi da muka cinye, sannan ki barni da dana sanin yanda na sadaukar da rayuwata kan yaron da ba wata rana da zai yi mini.”
Cike da mamakin kalaman da Maryam keji take shigowa cikin gidan tace “Baba? Ya Baqeer ne fa?”
Wani mugun kallo yayi mata ya maida kallonshi kan Umma da banda hawaye babu abinda take yi ya cigaba da cewa “Ki kuma sanar da yaranki wallahi duk wacce tayi gigin dawo mini gida da sunan yaji ko mutuwar aure sai dai ta shiga duniya ba dai ta zauna a gidana ba, sannan kafin naje na dawo ku tabbatar kun ɗauke shi daga ɗakin.” Yana kaiwa nan ya juya ya fita yana balbala masifa, ranshi gaba ɗaya yau a ɓace yake tunda ya kunna radio yaji ana maganar gasar da za’ayi gobe a Abuja da yanda masu gasar suka hallara suna masaukinsu. Ji yake yi zuciyarshi kamar zata fito saboda ɓacin rai, shekara guda kenan da turawan suka shigo da maganar gasar kuma shekara guda kenan yana shirin gasar nan amma gashi da ranshi da lafiyarshi abu ya gagara.
Chapter 20 · 0% Book details