← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 168

Sashe 62

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta buɗe baki zata bashi amsa kenan Salim ya turo ƙofar office ɗin ya shigo don haka ta mayar da bakin ta rufe. Sai da ya karɓi file ɗin sannan ya juya ya kalli Baqeer daya cika yayi fam yake ganin kamar da gayya Zeey ta kawo shi wajen saurayinta suna soyayya a gabanshi, yace mishi "Ina fatan dai kana yin exercises ɗin kamar yadda na nuna maka?" A cunkushe yace mishi "eh" yana jin kamar ya janyo shi ya tsokane idanun nan masu yawan kallon mata (mu kuma muka ce masu yawan kallon Zeey dai ko Mallam Baqeer). Sai da yayi ƴan rubuce-rubuce akan folder ɗin sannan ya tashi ya zagayo wajen Baqeer bayan ya fito da wasu machines ya ɗora akan table, da taimakon Salim suka ɗora shi akan gadon da yake duba marasa lafiya sannan yaja labule ya rufe wajen saboda samun privacy, ɗaya daga cikin machines ɗin ya ɗauka yana daddana mishi akan ƙafafun nashi tun daga gadon bayanshi, haka yayi ta amfani da machina kala-kala a jikin Baqeer idan ya gama da wannan sai ya ɗauki wannan kuma har aka ɗauki wani lokaci mai tsawo, kafin kace miye wannan kuwa Baqeer ya haɗa gumi kashirɓan a dukkanin gaɓɓan jikin shi. Shi da kanshi yaji daɗi a jikinshi daga yadda treatment ɗin nasu ya kasance. Fitowa yayi ya barshi a wurin yana mayar da kayanshi don kafin a fara treatment ɗin sai da ya rage kayan jikin shi ya zama daga shi sai boxer short, wajen sink ɗin dake gefe guda daga cikin office ɗin ya nufa ya wanke hannayenshi bayan ya cire handgloves din ya zuba a dustbin sannan ya dawo ya zauna.

Har ya gama saka kayan yana tunanin ta yadda zai yi magana azo a taimaka mishi ya sauko daga kan gadon don yayi mishi tsawo ba zai iya daddafawa ya koma kan wheelchair ɗin tashi ba, jin shirun shi yayi yawa yasa Salim ya taso don yasan halin Baqeer ba zai taɓa cewa yana buƙatar taimako ba sai dai suyi ta zama a haka. Da taimakon Salim ɗin ya koma kan wheelchair ɗin Salim ya tura su zuwa gaban table ɗin Junaid a wannan lokacin kuwa hira suke yi da Zeey yana tsokanarta wai ba zai barta ta fita daga cikin asibitin ba sai yasa anyi mata allura don ya santa da tsoron allura tana kuka tun da can idan za'a yi mata sai anyi daga da ita, ita kuma tana cewa "Da kenan wallahi yanzu wuce nan na tsaya ina kuka akan allura" shi kuma yana cewa "A’a fa Zeey gara dai ki daina cika baki kada kizo kina jin kunya.”
“Allah ya sauwaƙe wallahi,” tace tana murguɗa mishi baki. Wani abu Baqeer yaji ya tokare a makoshin shi, haka nan shi dai baya son ganin Zeey tana yiwa saurayin nan fara'a duk kuwa da bai san miye a tsakaninsu ba, bai san lokacin da ya saki siririn tsakin da a tunaninshi a cikin zuciyarshi yayi ba sai da yaga duk sun zuba mishi ido sannan yasan a fili yayi, kawar da kai yayi kamar bai lura da kallon da suke yi mishi ba ya kalli Salim da fuskar da babu ɗigo na fara'a ko kaɗan a ciki yace "Mu wuce ko?" Ɗaga kai kawai yayi alamun amsawa don haka nan yaji kamar Baqeer bai kyauta ba da yadda yake ta cika yana batsewa kamar wanda aka yiwa wani abu bayan duk ƙoƙarin da Zeey take yi na ganin ya samu lafiya abinda mahaifin da yake tutiyar yafi kowa son shi ya kasa yi mishi.

Kallon Zeey Salim yayi sai ta miƙe tana cewa "Thank you J, ka dai ƙi muyi maganar nan amma In Sha Allah ina komawa gida zan kira ka, please kada kace a'a" ta ƙarashe maganar tana langaɓar da kai gefe, shi Junaid ya fahimci maganar payment da yaƙi suyi ranar take yi mishi don haka yayi murmushi kawai yace "Waiting for your call with pleasure," yayi winking mata idonshi ɗaya. Takaici ne Baqeer yaji ya lulluɓe shi matsawa yayi kusa dashi ya ajiye wayarshi yace “Sorry ba kuɗi a hannuna ka riƙe wannan In Sha Allahu in na samu kuɗi zan kawo maka.”
Zeey ce tayi mishi alama wanda yasa Junaid yin murmushi yace “Kar ka damu, sabon asibiti ne sai muke trial na 30days, so after 30days in dai kazo you have to pay.”
Da mamaki Baqeer ya kalleshi Junaid ya nuna mishi wani flyer dake wurin wanda ya bawa Baqeer amsa, ganin da gaske yake yasa yace “Thank you” ya gara kekenshi da sauri ya bar office ɗin yana jin kamar zuciyarshi zata buga tsabar kishin da yake ji wanda tunda yake bai taɓa jinshi akan wani ba, da sauri Salim yabi bayanshi bayan ya yiwa Junaid godiya, Zeey ma tabi bayanshi suka fita tana jaddada wa Junaid zata kirashi idan ta koma gida.
Bayanta yabi da kallo har ta fice yana sakin wani malalacin murmushi, har cikin zuciyarshi yasan yana son Zeey sai dai ta kasa ɗaukar shi da muhimmanci ita kallon aboki kawai take yi mishi gashi yaga alama shima wannan gurgun kamar son ta yake yi don yana lura da yadda yake harararshi a fakaice, shi dariya ma abun ya bashi don dai yasan idan har da gaske shima son Zeey ɗin yake yi to haukarshi kawai yake yi don kuwa babu abinda zai haɗata da nakasashen mutum, maza masu lafiya masu ji da class da kuɗi ma basu isheta kallo ba bare wani gurgu sai dai kuma deep down yana jin shakku na yadda Zainab ta ɗauki al'amuranshi da girma don shi dai zai iya cewa bai taɓa ganin Zeey ta damu da wani mutum kamar yadda ta damu da Baqeer ba.

*****
Kamar yadda suka zo haka suka koma babu mai yin magana a cikinsu har Salim da a zuwa yake jansu da hira jefi-jefi. Motar na tsayawa a ƙofar gidan ta buɗe mota ta fice ta barsu anan Salim na kicin-kicin taimakawa Baqeer ya zauna akan wheelchair ɗin shi. Da fara'a Dada ta tareta tana cewa "Har kun dawo?" Zama tayi akan tabarma kusa da Dada tace "Wallahi kuwa Dada, mun daɗe ko?"
"Kun yi sauri dai" Dada ta amsa mata tana ajiye flask ɗin data zuba mata ƙosai a gabanta. Buɗe flask ɗin Zeey tayi tana cewa "Kai Dada amma wallahi yau kin biyani, har na manta yaushe rabon da naci ƙosai.” Ta ɗauki ɗaya ta dangwala yajin Dada mai ɗan karen daɗi ta kai bakinta tana lumshe ido. A daidai wannan lokacin Salim da Baqeer suka shigo, kallon flask ɗin gabanta yayi ya kawar da kai cikin ranshi dai yana tsegumin sai da Dada dai tayi mata ƙosan nan hankali ya kwanta. Gefe guda yayi da wheelchair ɗin shi a ƙarƙashin inuwar umbrella dake shigowa daga gidan maƙota. Salim ma wuri ya samu ya zauna yana cewa "Hajiya Zainab abun ƴar haka ce babu ko tayi?” Ƴar dariya tayi cikin jin kunya tace mishi "To Bismillah," Shima dariyar yayi yace "A’a ci kayanki ni bazan ci ƙosai yanzu da tsakar rana ba sai dai ban sani ba ko Baqeer zai ci.”

Ɗaga kai tayi ta kalleshi sai aka yi dace shima kallonta yake yi a lokacin don haka a tare idanunsu suka shige cikin na juna. Wani irin kallo yake yi mata da ta rasa a wane aji zata fassara shi, ita ta fara janye idanunta ta mayar kan kwanon ƙosanta murya ƙasa-ƙasa tace "Idan zai ci gashi nan da yawa ai zai ishemu.” Shi dai bai saka musu baki ba har ta gama cin ƙosan ta tashi ta wanko hannunta ta dawo ta zauna, sai sannan tace mishi "Yauwa Ya Baqeer zaka zana mini style ɗin?" Yi yayi tamkar bai jita ba kawai sai ya fito da wayarshi daga aljihu yana daddannawa. Haushi ne ya kama Dada don tana ganin yadda mafi yawan lokuta yake yiwa Zainab alhalin bata nufin shi da komai sai alheri don haka cikin faɗa-faɗa tace mishi "Kai kuwa dai Baqeer ban san irinka ba wallahi, Allah ya wadaran halinka na baƙar zuciya mai manta alheri, haba yarinyar nan binka take yi tana tsaye akan komai naka abinda take yi maka wani ɗan uwan na jini ma ba lallai ne yayi maka irin shi ba amma baka da abar wulaƙantawa sai ita, wallahi ka sake halinka don dai ba halin mutanen kirki bane wannan, ah to" ta tashi tayi shigewarta ɗaki ta bar su anan. Duk sai yaji babu daɗi don shi ba da nufin wulaƙanci yake yi mata hakan ba kawai dai mafi yawan lokuta bata samunshi a lokacin da yake cikin yanayi mai daɗi ne.
Chapter 62 · 0% Book details