← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 168

Sashe 98

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Harara ya wurgawa Areef É—in kafin ya ce "Meeshar ce so silent?". "Yeah Lion, Meesha she is so silent girl, ga hankali, ko da baka yi sex da ita ba, zaku yi wasa, zata na rage maka abin da kake ji sosai, ni bana goyon bayan ka sake kusantarta a yanzu, because idan ka sake kusantarta nan kusa zaka kasheta ne kawai, amma ka É—aukota dan ta rage maka feeling da kake ji ta hanyar wasa".

Har lokacin harararsa ya sake yi, sannan ya É—an yi shiru na tsawon mintoci kafin ya ce "Meesha she isn't like you're thinking, she isn't silent at all, and them I can't control myself idan na ganta a kusa da ni, you can't understand anything Areef, you can't understand who is Meesha, even if i explain to you, you can't understand anything, what i know dai shi ne Meesha ce kawai zata iya kashe mani abin da nake ji that's all".

"Lion why are you saying I can't understand who is Rimsha? I think na fika ma sanin wacece ita, kai fa baku jima da fara shiri ba, bata jima da fara zama kusa da kai ba, she is so silent, very very cute and smart girl".

Girgiza kai kawai Lion ɗin ya yi, Areef fa ba zai gane komai ba, she a wajensa Rimsha ba shiru shiru bace, su ne take yi wa shiru shiru, shi a wajensa banda kuka da shagwaɓa babu abin da take yi mashi, and then yadda ya ɗanɗani zumar nan tata ba zai iya hakura ya kyaleta kamar yadda Areef ɗin ya faɗa ba, ba zasu gane me yaji ba, kawai su kyale shi da abin da yake ji, shi kaɗai yasan wace duniya ya shiga, shi kaɗai yasan wacece Rimsha, a yanzu ko iyayenta sai dai ya kallesu da ido, amma ba dai su gaya mashi sanin wacece Rimsha ba, saboda Areef bai san komai bane yake wani cewa ya fishi sanin Rimsha, to abin da bai sani ba ita dai Rimsha kamar mutun biyu ce a jikin mutun ɗaya, saboda acting biyu take yi, a wajensu Areef tana nuna masu true colornta, shi kuwa Lion ko magana zata yi mashi na serious a kan abu, ba zaka taɓa jin ta buɗe murya ko kuma ta yi magana da asalin voice nata ba, cikin shagwaɓa take yi mashi magana, yanzu da za'a cewa Areef tana da saurin kuka, ba zai taɓa yarda ba, saboda bata taɓa yi masu ba, amma shi kuma Lion, da ya yi mata abu kaɗan zata sa mashi kuka, sai ya yi ta aikin rarrashi, so sanin da Areef ya yi mata ya mata ne a kan Rimshar ta na ainahi, shi kuma Lion Meesha uwar shagwaɓa da soyayya ya sani, suna da banbanci sosai.

"Areef you don't know who's Rimsha, that's all kawai". Ya faÉ—a tare da jawo wayarsa dake É—aure a saman bedside drawer tana ringing.

Shiru Areef É—in ya yi yana tunanin halayen Rimshar, shi dai yasan shiru shiru ce Rimsha, ga shiga hankali sosai.

Ganin kiran mommansa ne yasa ya katse kiran tare da gyara kwanciyarsa haÉ—e da jawo pillow izuwa saman Lion chest nasa, sannan ya bi kiran. Bugu É—aya suka É—auka. Cikin sanyin murya ya ce "Assalamu alaikum, good evening Momma".

Daga ɗaukar ɓangaren ta amsa mashi da "It's not Momma, it's Meesha, wai Noorish ina ka tafi ne? Tun ɗazun gwaggo ta ce ka fita, kuma baka dawo ba, ni fa gaskiya........" Dakatawa da yin maganar ta yi sakamakon jin yanda ya ambaci sunanta da ɗan sauti kuma cikin sarkewar murya, yana daga kwance bai san time da ya miƙe zaune ba, kwata kwata bai kawowa ransa cewa ta farfaɗo ko zata farfaɗo a yanzu ba, kuma dole ya shiga mamaki na jin yadda ta kirashi babu wata alama da take nuna cewa ya yi mata laifi, ko tana fushi da shi, bai san ita bata san komai da ya faru ba, bai taɓa tunanin zata farfaɗo ta yarda da shi ba, bai taɓa tunanin zata yarda ko a waya su yi magana ba, abin ya yi matuƙar bashi mamaki.

Love period ❤️🥲😌

"Noorish lafiya kuwa?". Ta faÉ—a a É—an tsorace.

A hankali ya koma ya kwanta tare da kara jawo pillown nasa ya rungume yana faÉ—in "My Meesha is it you?". Ya faÉ—a cikin wata iriyar murya da take nuna tsantsar kaunarta da yake yi.

Mamaki ne ya kamata, ita tarasa wannan abin da me ya yi kama, su mummynta sai su rinƙa lallaɓata suna ta ce mata sannu, sannu yaki karewa, ga maganganun da zasu kwantar mata da hankali wanda gwaggo da mum ɗin suke gaya mata, sannan ga kula na musamman da suke bata, sun hanata zuwa ta je ta yi wanka, da ta motsa za su ce mata sannu tana bukatar wani abin ne? Yanzu ta ce zata yi magana da Noorish gwaggo ta kira mata shi a waya, shi ma yana ɗaukar kiran ya ruɗe daga jin voice nata, tunani ta fara yi anya wani gagarumin abu bai faru ba kuwa? Anya babu wani abin da suka ɓoye mata kuwa? Tasan cewa gwaggon da mum ɗinta duk tun fil azart suna nuna masu kauna da kulawa, amma ta yau ɗin nan ta yi yawa over, sun saka mata kai a duhu, sun kuma saka mata kwakwalwa a cikin tunani.

"Meesha meyasa kika yi shiru?". Ya faɗa yana kallon Areef da ya tsare shi da ido. Sai mamakinsa Areef ɗin yake yi, bai taɓa tunanin ko da sunan wasa zai ga Lion cikin zumuɗin jin muryar mace irin haka ba.

Hannu ya kai ya kyastawa Areef É—in kyawawan yatsunsa a dai'dai saitin face nasa yana sauraron abin da Meeshar tasa take faÉ—a.

Kasa sosai ta yi da murya, dan gwaggo tana a cikin É—akin nata, mum ta koma nata É—akin zata je ta yi sallah, so bata son gwaggon ta ji hiranta da mijin nata, dan wani azababben kunyar gwaggon take ji a yanzu.

"Noorish kafaÉ—a mani me kayi mani please? Naga su mum sai sona suke kara yi".

(Rimsha zata kashe mutun da dariya, wai su mum sai kara sonta suke yi😂)

Shiru ya É—an yi, sai yanzu ya gane dalilin da ya sanya ta yarda ta kira shi a waya, wato bata san abin da ya faru ba? No wonder mana, da ta sani ai da sun yi hannun riga kenan.

Nisawa ya yi tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya kafin ya fara magana in a cool voice. "Meesha babu abin da na yi maki face soyayya kawai, know lest do a video call, I want to see your beautiful face my life".

Shi kam Areef ai gabaɗaya Lion ya kwance mashi lissafin ƙwaƙwalwa, ko da sunan wasa bai taɓa tunani Lion ya iya kalamai masu daɗi haka ba, basu taɓa jin sa ko da sunan wasa ya furta makamantansu ba, ko a mafarki basu taɓa zaton ganin irin wannan rana ba.

"Noorish Allah kunyarka nake ji, ni kawai ka dawo gida sai muga juna". A shagwaɓe sosai ta yi maganar.

Kamar zai ce mata baya kasar, amma sai ya tuna da cewa ta ce mashi gwaggo ta ce mata ya fita yana zuwa, hakan na nufin sun ɓoye mata baya nan kenan, tuna hakan yasa ya ce mata "Meesha ba zaki yi mani abin da nake so ba? Ina son kallon face naki fa na ce? Before na dawo ɗin ne nake son ganinki, do you know how much i love? Do you know what am feeling about you now danaji voice naki kuwa?".

Kwace wayar Areef ya yi tare da sanyata a hand-free, dan ya tabbatar wa da kansa Rimshar da ya sani ce, ko dai wata ce, so yake ya ji yau dai ya suke magana, me Rimsha take gayawa Lion da har shi ma yake gaya mata kalamai irin haka.

(Areef akwai shegen son jin gulma, ga sa ido, ko ina ruwansa da su?🤔 😂 Amma dai gara ya jiyo mana me suke faɗa da kyau 😂)

"Noorish kome kake so zan yi maka mana, in dai bai saɓawa Allah, ka manta cewa kai ne farincikina? Amma dai ni gaskiya sai ka rufe ido, idan na kalli kyakkywar face ɗin nan naka da kyau da kyau, sai na kawar da kallo na, sai ka buɗe idon, dan ina jin kunyar ganin cikin idonka ne fa". Ta yi maganar a shagwaɓe sosai.

Salati Areef ɗin ya fara yi a cikin zuciyarsa, yana mamakin yaushe Rimsha ta zama haka shi bai da labari? E lallai dole Lion ya rinƙa zuba mata kalamai ba tare da ya san yana zuba su ba, irin wannan zallar madarar shagwaɓa da kalamai da take zuba mashi, ga muryarta a kwance kasa kasa, idan ba ka yi mata farin sani bama, ba zaka taɓa cewa ita bace, gaskiya bai ga laifin Lion ba, dole ne ma ya shiga zuba kalamai ba dan ya shirya ba. Daga kasan zuciyarsa kuma tunani yake yi ko yaushe shi kuma zai sami irin wannan soyayya haka? Yaushe Jehan zata fara nuna mashi soyayya haka?. Bawan Allah duk sai ya ji babu daɗ, Rimsha dai har da wani sunan soyayya mai azababben daɗi tasakawa mijinta, wai Noorish, Noorish ɗin ma idan zata kira da salo mai matuƙar jan hankali take kira, amma shi ƴar diramar nan tasa tasan komai, kuma ta iya komai sai wahalar da shi take yi, kuma a haka saboda rashin adalci irin na zuciyarsa kara sonta ma yake yi, baya son ya ji an faɗi laifinta, bawan Allah.

Karɓar wayar tasa daga hannun Areef ɗin ya yi tare da katse kiran ya kirata video call.

Bugu É—aya ta É—auka.
Wani irin doguwar numfashi ya ja lokacin da idanuwansa suka sauka a kanta, a hankali ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya. Ita ma tana É—aukar kiran ta sauke idanunta a saman face nasa, wani irin daddaÉ—ar ajiyar zuciya ta sauke, sai dai kuma ta canza fuska sosai na ganin shi kwance a saman bed, ina yake to? Ta tambayi kanta.

Ganin ta É—aure fuska sosai ne yasa ya É—aga mata gera É—aya alamar lafiya?.
Chapter 98 · 0% Book details