← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 168

Sashe 17

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tamkar jira take yi wani sabon kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro ne ya kubce mata. Zafafan hawaye ne wasu suna bin wasu a kuncinta. Hakika an cuceta ba kaɗan ba, an cutar da rayuwarta ba karya, kuma a duk wannan abin da ya faru, sam bata da laifi, duba da yanayin karantar shekarunta a lokacin, ga ƙarancin ilimin addini, sannan bata wani rayuwa da mahaifiyarta sosai ba, bata taɓa haihuwa ba sai a kan TRIPLETS ɗin, a lokacin da ta mayarwa da Dr yaran, bata gama sanin zafinsu ba, sannan zuciya ce ta ɗebeta, wanda kuma dama wannan dole ce, tama yi namijin kokarin da ta hakura ta haife cikin, duk cin amanar da ya yi mata, ta daure ta haife cikin, gaskiya ta yi namijin kokari, abin a jinjina mata nema!!.

Ganin haka yasa ya ɗan raba jikinsu kaɗan tare da ɗan duƙawa ya ɗauketa cancak tamkar karamar yarinya, ya nufi bedroom nasa da ita. Gabaɗaya palon binsu da kallo suka yi, shi ma Areef binsu da kallo ya yi ya kasa motsawa, dan shi kaɗai yasan raɗaɗin da yake ji a cikin zuciyarsa. Shi dama Aseef bawan Allah sam bai ɗago kai ba ma, bare yasan me suke yi, yana kife yana kuka, Allah sarki bayin Allah!.

Ita ma Brr Naurat sai bin su da idanu take yi, tana jin abin tamkar a mafarki ne!.

Lion bai sauke gwaggo a ko'ina ba, sai a bakin katafaren bed nasa da yake shinfiɗe da white bed sheet mai matuƙar kyau da tsada, kamar yanda kuka sani ne, sai zuba uban daddaɗar kamshi bedroom ɗin nasa yake yi, ko'ina a gyare tsab, tsab, fes, fes!!.

A gefenta ya zauna tare da É—an juyowa suna fuskantar juna. Hannayenta ya riko cikin nasa, har lokacin zubar da hawaye take yi tamkar famfo aka bude. Cikin nutsuwa da sanyi murya ya ce "Ba zan hanaki kuka ba, ki yi sosai, dan yana rage raÉ—aÉ—i, na san duk raÉ—aÉ—in da muke ji a yanzu, ba mu kai kwatan naki ba, so just cry, cry more!". Ya kai karshen maganar tare da sakin hannayen nata ya rungumota a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya.

Kankame shi sosai ta yi tana mai cigaba da kukanta yana sauraronta, dan yasan kukan shi ne zai sa ta sami sassaucin abin da take ji a cikin zuciyarta, yau ta tuna baya, an cutar da ita over baiwar Allah.

A haka gabaÉ—aya familyn suka shigo bedroom É—in suka samesu, har da su Rimsha da Brr Naurat, duk sun biyo sahunsu, sun baro Dr William da yake sume, sai dai Areef ya É—auke shi ya kwantar da shi a saman sofa, sannan suka biyo Lion É—in. TGA da Uncle Herry suna wajen Dr William É—in, su kuma su John wucewa suka yi nasu bedroom É—in, wai ba za su zo É—akin ba!.

A É—ayan gefen gwaggon Areef ya zauna, ya zamana sun sakata a tsakiya. Shi kuma Aseef saman bed É—in gabaÉ—aya ya haye, ya kwanta, kansa tamkar zata fashe mashi saboda ciwo, har wani jiri yake gani, yana ganin dishi dishi.

ÆŠago kai daga saman kirjin Lion É—in ta yi tare da juyowa zuwa ga Areef dake gefenta. Hannu Areef É—in ya kai ya fara goge mata hawaye yana faÉ—in dan Allah ta yi shiru, kukan ya isa haka nan, ba ya son ganin kukan nata, dan ba zai iya jura ba, zuciyarsa tana yi mashi zafi sosai idan yana ganin kukan.

Yana magana yana goge mata hawaye, shi kuwa Lion ya dukar da kansa kasa yana tunani a kan abubuwan da gwaggon ta faÉ—a daga farko har karshe, yana nazari a kansu.

Muryar gwaggon ne ta daki dodan kunnuwansu, a in da ta ce "Ina É—ayan É—ana? Ina cikon TRIPLETS É—in?". Juyawa Areef ya yi izuwa ga Aseef dake kwance tamkar zai mutu, idanunsa sun yi jajir kamar jini. A sanyaye ya ce mata ga shi nan.

Cikin ruɗu ta ce "Me ya same shi ya kwanta haka?". Ta yi maganar tare da kai hannu tana taɓa kansa. Turo baki ya yi tamkar yanda kuka sani ne, gidan shagwaɓa ba, ko a gadon asibiti yake sai ya yi ta, yanzu ma dai cikin shagwaɓa ya ce "Please ku dai'na taɓani, Allah idan ba haka ba in na fara kuka ba zan dai'na ba!". Shiru kawai gwaggo ta yi, dan kuwa yanda Aseef ya yi maganar sak Dr William time da suke zuba soyayya, sai ya tuna mata da baya.

"My son mommarka ce fa take taɓaka, tashi ka gaya mini menene yake damunka?". Cewar gwaggon. Kara turo baki sosai ya yi yana faɗin "Ni momma to ki barni mana, bana so ne a taɓani".

Girgiza kai kawai Areef ya yi, yanzu ya dai'na mamakin halin Aseef, tun da ya ji cewa daddynsu ruwa biyu ne, ɗan shagwaɓa ne ta wani fannin, ta wani fannin kuma ɗan bala'i, mafaɗaci, to kun ga kuwa shi Aseef ai shi ya yi gado, dan kuwa shi ma ruwa biyu ne, idan ka taɓo shi, ya iya faɗa, sai dai kawai ya fi Dr yawan shagwaɓa ne, dama kuma, ɗan na gada, ya fi ɗan na koya.

"Tashi to ka zo na goyaka". Cewar gwaggon, ta yi maganar cikin zolaya. ÆŠan É—ago kansa ya yi. A hankali ya matso kusa da ita yana faÉ—in "Kwanciya a saman cinyarki ma is okey my Momma".

Matsa mashi waje kaÉ—an Areef ya yi, a nan ne ya samu dama ya kwantar da kansa a saman cinyar tata yana mai cigaba da turo É—an bakinsa abinsa.

Shiru bedroom É—in ya yi na É—an tsawon lokaci kafin Brr Naurat dake zaune saman sofa ta ce "To yanzu ina son sanin wani abu guda a kan wannan case É—in".

ÆŠago kai dukkansu suka yi tare da kai kallonsu gareta. Lion ne ya amsa mata da cewa "No, just ki bar maganar nan a yanzu, ki bari sai gaba". Jinjina mashi kai ta yi, dan ta lura dukkansu basu a cikin nutsuwarsu.

ÆŠago idanu da gwaggon zata yi ne idaunta suka sauka a kan chain dake wuyar Lion É—in, wani irin nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke wanda yasa TRIPLETS É—in suka É—ago suna kallonta. Su daddyn Rimsha har suna rige rigen haÉ—a baki wajen tambayarta lafiya.

Cool murmushi ta sakarwa daddyn Rimsha tana faÉ—in "Ina Jehan?". Da hannu daddyn ya nuna nata Jehan É—in dake zaune kusa da Rimsha dake kusa da Brr Naurat.

Alama ta yi wa Jehan ɗin da hannu a kan ta zo. Da sauri ta miƙe ta zo. Tsabar iya shege irin na Jehan ɗin a saman cinyar gwaggon kusa da Aseef ta gefe ta zauna tare da saƙalo wuyar gwaggon da hannunta ɗaya, tana wani kwaɓe fuska, tana kuma raɗa wa gwaggon magana a kunne. Binsu da idanu Areef ya yi yana tunanin irin tsiyar da ya rinƙa yi mata a kan daddynta a baya, yanzu reshe ta juye da mujiya kenan........ E NIMA PRINCESS TEEMA NA CE RESHE TA JUYE DA MUJIYA KUWA, DAN GWAGGO DA JEHAN 5 AND 6 NE, LALLAI JEHAN ZATA RAMA ABIN DA KA RINƘA YI MATA NA HANATA ZUWA WAJEN DADDYNTA😂 YANZU WASAN ZAI FARA😂 KAI ABUBUWA SUNA YI MANI DAƊI😂 AREEF KA JIRA ƊAUKAR FANSA😎🥳 DAN WLH GWAGGO DAI TANA BAYAN JEHAN💃🥳

Kome Jehan É—in ta raÉ—a mata sai ga gwaggon ta fashe da dariya tana kallon Areef. Daga gani yasan gulmarsa ta kai, da wani idanunta kamar ball a cewarsa. Hannu gwaggon ta kai ta ciro sarkar dake wuyar Jehan É—in, dama kun san nasu Jehan mai round ne, na su Lion kuma mai tambarin heart, sannan na su Jehan É—in yana da faÉ—i fiye da na su Lion É—in, kuma na su Lion zallar zinari ne, na su Jehan iya igiyar ce kawai zinari.

Ciro sarkar Jehan ɗin ta yi a in da ta sanya karfi cikin dabara ta buɗe kan round na sarkar. Nan take wani tambarin ɓari na heart ya bayyana a cikin round ɗin, sai kyalli yake yi har yana ɗaukar idanu. Ciro heart ɗin ta yi sannan ta mayar da sarkar ta rufe tare da mayarwa da Jehan ɗin abinta.

A hankali ta ambaci sunan Lion, ɗagowa ya yi yana kallonta. Kama sarkar wuyarsa ta yi tare da sanya ɓarin heart ɗin da ta ciro daga sarkar Jehan ɗin, ta mayar ta jona. Nan take chain ɗin ya koma tamkar ba'a taɓa raba shi biyu ba, ya zama kamar yanda yake. Sam Lion bai yi mamaki ba, dan yasan ita ce mahaifiyarsu, kuma dama yasan a wajenta kawai za'a sami rabin sarkar nan, dan har company ya je sun kasa buga mashi ɓarin da zai yi dai'dai da chain ɗin, daga karshe dai ya hakura ya bar zancen kawai, ashe yana jikin sarkar Jehan, gwaggo ta iya ajiya a in da kowa ba zai zata ba, kuma duk in da za su je yana tare da su.

Cikin shagwaɓa Jehan ɗin ta ce "Gwaggo dama ashe abu kika ajiye a ciki kenan? Shi ne har da wani cemini ko za'a kasheni kada na yarda na bada sarkar nan ko? Wato yanzu dama a kan wannan abin ne har da cewa ko za'a kashe ni ko? Allah na ɓata dake". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa dan ta bar wajen.

Sake baki Areef ya yi yana kallon ikon Allah, mamaki yake yi, ashe dama ƴar rigimar nan tasa ta iya shagwaɓa kenan? Ashe da gangan take yi mashi abu kamar wata boss? Ai kuwa zai yi maganinta, ya faɗa a ransa. Bai san cewa da iya gwaggo kawai take shagwaɓar ba, bayan gwaggon ba wanda yake ganin hakwaranta ma bare shagwaɓa, sai daddynta da shi ma ba koda yaushe ba, sun fi shiri da gwaggon, mum nasu kam dama kun sani basu wani shaku ba, dan ita ta gwaggo ce.

"Haba babyn gwaggo da daddynta, zo kiji wata magana". Cewar gwaggon. Kin zuwa ta yi ita a dole ta yi fushi, fuuu ta wuce zata bar wajen.
Chapter 17 · 0% Book details