← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 168

Sashe 68

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 3 min read

"Magana ta gaskiya dai, na farko a nan shi ne, da gaske mahaifiyarku ce ta bamu yaro É—aya, babu wasa a cikin wannan maganar, shi kuma maganar Anderson, ba shakka Anderson yana raye kamar yanda ka yi hasashe, maganar É—an uwanka cikon TRIPLETS naka kuma, i don't know har yanzu yana raye or not, wannan shi ne iya gaskiyar da na sani".

Shiru Lion ɗin ya ɗan yi na ɗan lokaci kafin ya sake cewa "Tun ainahi menene matsalar, and meyasa kuka karɓi cikon TRIPLETS nawa?".

A tsananin razane tare da kiɗima kakan nasa ya fara magana "Please Romeo don't ask me this questions! I don't want to die, i have alot of things da nake son cinmawa, idan har na gaya maka gaskiya, to ba shakka zan mutu a yau, please save my life, leave me like that!". Ya kai karshen maganar yana zare idanu kamar an tare ɓera a tarko.

Nisawa ya yi nafin a takaice ya ce "I don't want all this miscellaneous excuse, just amsa me, meyasa suka É—auki cikon TRIPLETS nawa? Me kuka yi da shi?".

Allah sarki Lion bawan Allah, yasan cewa baba shakka gwaggo da bakinta ta bada ɗaya daga cikinsu, amma shi ba hakan ce a gabansa ba, dan ya san wlh gwaggo ba zata bayar da su haka kawai ba, dole da kawai kwakkwaran dalili, shi yanzu so yake yasan menene yasa aka yi hakan dukka, ba damuwarsa wanda ya bayarba, a gaskiya sai mai karfin Imani mai kuma tawakkali da yarda da ƙaddara ne kawai zai iya ɗaukar abin da Lion yake ɗauka, bugu da kari shi duk abin da zaka gaya mashi sai ya yi doguwar nazari a kan maganar, shiyasa yana da matuƙar wahala kaga ya yanke kuhunci ba dai'dai ba, saboda aiki da kwakwalwa da basira, a yanzu da wani ne ya ji abin da kakan nan nasu ya ce, to ba shakka da ba zai yi wani dogon tunani ba, kawai zai ɗauki karan tsana ne ya ɗaurawa gwaggo ɗin, alhalin kuma dole da akwai dalilinta na yin hakan, Allah ka bamu ikon yin amfani da kwakwalwarmu wajen yin tunani a koda yaushe.

"Romeo it's a long story, please and please let me go........" Kasa karisa maganar ya yi saboda wani irin kallo da Lion É—in ya wurga mashi, hakance tasa ya haÉ—iye maganar.

"Uncle you know that bana repeating na word ko? And them bana cancel na magana idan nayi ko?".

Jinjina mashi kai kakan nasa ya yi, ba shakka yasan da cewa Lion ba zai canza maganar nan ba, ya gaya mashi gaskiya shi ne kawai zai zama mafi a'ala a garesa, idan ba haka ba, wlh Lion zai gana mashi azabar da sai ya gwammaci mutuwa a kanta, dan haka sai ya fara magana cike da iya gaskiyar da ya sani kamar haka.
Chapter 68 · 0% Book details