Sashe 52
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A lokacin da na fita gida, hotel na fara kamawa, ina shiga ɗakin nawa, na zauna na ci kuka na son ra'ina, a wannan rana na kwana ban yi barci ba, sai dai kuma na kudurci niyar duk wuya duk daɗi ba zan koma gida ba, ba zan sake waiwayar kowa ba, na kudurta a zuciyata zan yi rayuwata ni kaɗai'na, zan kuma tsaya tsayin daka na nemi ilimi, zan shiga siyasa, daga karshe kuma ina rokon Allah da ya bani iko da dama na samu na taimaki ƴan uwana a duk in da za su kasance, yin wannan tunani yasa ya sami karfin gwiwa, dan haka sai na tashi na yi wanka, na daura towel ɗin hotel ɗin na ɗan kwanta na huta, sai dai tunanin mummy da cikinta ya hanani sukunin, haka dai a daure ina yi mata addu'a. A washegarin ranar na nemi gida na saya, kuɗin da Mommy ta bani suna da mugun yawa sosai, da su na cigaba da yin rayuwata, na koma makaranta, na kuma fara sana'a, ko kaɗan bana tunanin komawa gida, a duk abubuwan nan da na saya kuma ko rabin kuɗin da mum ta bani ban taɓa ba, saboda kuɗin dollars ne, idan na canza kaɗan suna da yawa a kuɗin Nigeria, haka na cigaba da rayuwata ni kaɗai tsawon lokaci, ina zuwa makaranta, kuma ina juya kuɗina, akwai lokacin da ta kama dole na je gida, haka na shirya na je gidan, sai dai ban bari kunsan naje ba, takardun makarantata na je na ɗauka, a lokacin na sami mum tana zaune a garden, na tsaya tsawon lokaci ina laɓe ina ganinta, sai dai ita bata ganni ba, daga karshe na ɗauki abin da zan ɗauka na fita gidan, haka na kammala karatuna ni kaɗai na, ina kuma bibiyar ƴan uwana, ranar da aka ce daddy ya rasu, har gida nazo dan na tabbatar, amma babu wanda ya ganni, komai da yake wakana a gida ina sane da shi, har auren yaya babba duk ina sane da komai, kuma na tura mashi da gudumawata, sai dai bai san cewa ni ne na bashi ba, auren yaya Deen duk ina sane da su, har haihuwar Imran da matar yaya babba ta yi, duk ina sane, kafin haihuwar Imran ma korin Aunty Aisha da babban yaya ya yi daga gidansa duk ina sane, shi ne na je na ɗauketa, amma fa kafin na yi rayuwa da Aunty Aisha, na ruke Maik tukun nan, lokacin da naje gida dan tabbatar da mutuwar daddy, a lokacin na samu labarin cewa har da mum suka rasu, maganganun mutane ya kasu kashi biyu ne a lokacin, wasu sun ce ban da ita, wasu kuma sun ce har da ita, to ni dai da ban ganta a gidan ba, sai na ɗauko Maik muka dawo da shi gidana, ya yi rayuwa mai ɗan tsawo a wajena, ina ganin su baban yaya suka rinƙa nemansa, amma naki bayyana masu yana wajena, sai da ya ɗauki tsawon lokaci a wajena, sai tafiya ta kamani zuwa Dubai a kan harkar kasuwancina, bani da zaɓi dole na mayar da Maik gidan yaya babba, haka na shirya na ɗauke shi zuwa gidan, na bawa mai gadi shi, sannan na juya na koma, sam ban so rabuwa da Maik ba, na so na rene shi ne ya taso a hannuna, amma ba hali, da na tafi Dubai na ɗauki tsawon shekaru uku a can, a lokacin ne kuma Allah ya kara bunkasa mani arzikina, komai na taɓa kuɗi, har mamaki nake yi, abubuwa suka kara haɓaka, lokacin da Aunty Aisha ta baro gidan yaya babba ta suma a kan hanya, a lokacin ina Dubai, amma na sami labari ta hanyar security dana sanya yana yi mani gadin gidajen ƴan uwan nawa, dan ya gaya mani me yake faruwa, ina daga can nasa aka kai mani ita asibiti, satin ta ɗaya a asibiti na diro Nigeria, ni na cigaba da kula da ita na tsawon shekara ɗaya, bayan ta sami lafiya, sai na ɗauketa muka je har Washington, dan ta bani labarin abin da ya faru da ita, da muka je bamu sami waɗan da muke nema ba, sai na wuce da ita Dubai, a nan muka cigaba da rayuwarmu, ina sane da duk irin nemana da ƴan uwana suke yi, amma ko kaɗan ban ji cewa zan koma cikinsu ba, mun yi rayuwa mai tsawo a Dubai da Aunty Aisha, rabon auren Maryam ya dawo damu Nigeria, kafin mu dawo na sa an shifiɗa mana shinfiɗaɗɗen gini na alfarma, gini na gani na faɗa, muna dawowa na cewa Aunty Aisha zan je Niger in duba yanayin yanda ƙasar take, dan ina son buɗe company a can, a lokacin ina da wani aboki ɗan Niger ɗin, shi ne yake yawan bani labarin kasarsu, a makaranta muka haɗu, shi ne nace to bari naje ziyara na duba mu gani, ashe rabon auren Maryam ne ya kai ni, a hanyata muka haɗu da Shitu wanda ya kasance ɗan uwane ga ita Maryam ɗin, in takaice maku labari da na je ƙasar Niger, na so mu sauka a hotel, amma abokina ya nuna baya son hakan, ya nuna ba zai ji daɗi ba idan har ban sauka a gidansu ba, dan yana bawa ƴan uwansa labarina, iyayensa duk suna son ganina, yin hakan yasa na ce mashi to shikenan mu je gidan nasu, haka kuwa aka yi, lokacin kankanin na yi sabo da Shitu, muka zama kamar ƴan uwa, yana da kirki sosai, har muka karɓi number juna. Saukata a gidansu abokina naga karamci, suna da karamci sosai, mutanen Niger adilan mutane ne masu kirki sosai da sosai, suna da karamci over, haka suka karramani, suka mutuntani, a tare da abokina muka kwana, washegari da safe, bayan na yi wanka na shirya zamu je yawace gari da motar abokin nawa, muka shiga wajen mahaifiyarsa dan mu gaisheta, a nan na fara ganin Maryam, tana zaune kusa da mahaifiyar abokin nawa, da alama aikota aka yi, tana sanye da hijabinta har kasa, duk da cewa hijabin da kuma kayan jikinta duk a koɗe suke, amma ta yi shiga ta mutunci wanda duk wani ɗa namiji mai hankali zai sota, kuma zai yi sha'awar ta zama matarsa. Muna shigowa ta ɗaga mana gaisuwa cikin sanyin murya tana sunkuyar da kai kasa, kyakkyawar gaske ce sosai da sosai, sai dai alama akwai wahala sosai a tattare da ita, dan duk fatar jikinta a koɗe. A gaban idanunmu maman abokina ta bata sakon da ta zo karɓa a leda, ta tashi ta tafi abinta, mu kuma muka gaisa da maman abokin nawa, sannan ta zuba mana adduo'i tare da fatan alkhairi, daga nan muka fito, muna shiga cikin mota abokina ya kai mani duka yana faɗin malam ya naga sai kallon Maryam kake yi? Dariya na yi ina cewa kai kuma sarkin sa ido ba, dan Allah ƴar wacece? Ko kanwarka ce?. Bai yi kasa a gwiwa ba wajen gaya mani cewa ita marainiya ce, kuma ga in da take rayuwa, ya bani labarin komai da irin wahalar da take sha a hannun ƴan uwan mahaifiyarta da sauransu, na ji babu daɗi sosai, kuma na tausaya mata sosai, dan haka sai nace to muje gidansu, ko da muka je sai muka tarar da Shitu a gidan, shi ma ashe ya je dubata ne, ɗan uwanta ne ta gefen mahaifinta daga Nigeria kenan, na ji daɗi sosai na ganinsa, a lokacin yarinya ce sosai, dan ba zata wuci irin 13 to 14 years ba, hakan ce ta bani kwarin gwiwar naji cewa ina son na aureta, dan na tsamota daga wahalar da take ciki, kuma bata wuce shiga school ba, in takaice maku labari zuwana Niger dai shi ne silar aurena da Maryam, Aunty Aisha da kuma abokan arziki sune suka tsaya mani akan komai, da yake a lokacin ba wani ɗaukar Maryam ɗin da muhimmanci ƴan uwan nata suka yi ba, saboda rashin iyayenta, sai suka bani aurenta ba tare da bincike ko bin diddigin wanene ni ba, na auri Maryam, bayan ganina da ita na farko da wata biyar dai'dai, sannan na dawo da ita Nigeria, na kuma kaita har garin Maiduguri wajen ƴan uwan mahaifinta, dan naji labarin komai a kansa daga bakin Shitu, daga nan muka sake komawa Dubai da zama, ban yi zaman Nigeria sosai ba, mun yi rayuwa cikin tsananin farinciki, na sanya Maryam a makaranta, ta yi karatu sosai, dan tana da kaifin kwakwalwa da basira, kuma nima ina kara koya mata karatu sosai, Aunty Aisha ma tana kara mata wani duk da cewa ita ma tana zuwa ismaliya sosai a lokacin, aurena da Maryam ya ɗauki tsawon lokaci kafin mu sami haihuwa, cikin mu na farko yaron bai zo da rai ba, mun ji tsananin rashin daɗi, amma mun fawwalawa Allah komai, haka muka cigaba da rayuwar farinciki, cikinmu na biyu yana da wata bakwai ta haife shi, shima ɗa namiji ne, ya zo da rai, an saka shi a kwalba kasancewar bakwaini ne, kwanansa uku a duniya ya koma ga mahaliccinmu, munji babu daɗi, saboda mun ɗauki son duniyar nan mun ɗaura mashi, amma ba yadda zamu yi tun da haka Allah ya ƙaddaro mana, a cikin Maryam na uku ma yana da wata uku cikin ya zube, daga nan na fara shiga damuwa sosai a kan hakan, na ce sai dai muje asibiti, ko da muka je ma babu wata matsala, kawai dai Allah ne bai kawo mai tsayuwa ba, haka Aunty Aisha ta rinƙa kwantar mani da hankali, da har na fara tunanin shikenan ni ba zan sami magaji ba, a lokacin fa Hassan na ma ya yi aure, ɗansa Feroz har yana gudu ko'ina, ya girma, ga su Imran ɗin yaya babba duk sun girma, amma ni kuma shiru, abin kullum da shi nake kwana da shi nake tashi, ita ma Maryam tana cikin tsananin damuwa a kan hakan, sai dai bata bari na gane ba, kullum sai ta yi kuka, bata san ina sane da komai ba, damuwar da take shiga ne ma yake kara tsananta mani tawa damuwar, haka na cigaba da ƙoƙarin faranta mata rai ko dan maraicinta, in takaice maku sai da muka sami ciki har