← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 168

Sashe 6

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sam bata ma san time É—in da ta ce mishi "Same, you are very very beautiful, handsome guy, i really like your eyes color". ÆŠan zaro mata su ya yi. Da sauri ta runtse idanunta dan sun bata tsoro ganin yanda suke kyalli.

Muryarsa ta tsinkayo cikin kunnenta yana faÉ—in "I really like your eyes, your lips and your everything".

Waro idanuwan nata waje ta yi tana kallon yanda ya jingina kansa da jikin head na sofar yana binta da shanyayyun idanuwansa tamkar wanda ya yi shaye shaye. Abokan faɗa sun shirya yau kam, har ma suna ƙoƙarin zama cikakkun masoya na gaskiya.......KADA KU YI COMPARING RAYUWAR NAN NIGERIA DA NASU NA CAN, DAN AKWAI MUGU MUGUN BANBANCI, RAYUWARMU DA TASU BA ƊAYA BACE SAM, SO KU DAI'NA KALLON RAYUWAR TRIPLETS DA FAMILYNSU, MA'ANA SU DR WILLIAM KENAN, KU DAI'NA KALLONSU TA SIFFAR TAMU RAYUWAR, DAN BA HAƊI, AL'ADU DABAN DABAN!!.

Hannu ya miƙa mata a kan ta zo, bata musa mishi ba dan kada ku manta girman Russia ce ita ma, da ita da shi duk zani ne ta tadda muje, tafiyar duk ɗaya ce.
Miƙa mishi nata hannun ta yi. Cikin nutsuwa ya jawo hannun nata alamar ta zo gare shi. Miƙewa ta yi tare da nufarsa.

Tana ƙoƙarin zama a gefensa ya yi saurin zaunar da ita a saman cinyarsa. A tare suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya. Hannunsa dukka biyu ya ɗaura a saman shafaffen cikinta tare da ɗan jawota baya ta kwanta a saman kirjinsa.

Ɗan leƙo face nata ya yi yana faɗin "You are the best and you are special beb!, Kuma rigimammiya". Ɗan juyowa gare shi ta yi, suna ɗan fuskantar juna kafin ta ce "Why you say that?".

Ɗan shafa shafaffen cikin nata ya fara yi a hankali yana haurawa sama kafin ya ce "Ban taɓa tunanin zan kula mace ba a rayuwata, infact ni ban san menene ma yake sanyawa a so mace ba, bani da aboki, bani da kawa, only my brother Herry, shi ne kawai na kusa da ni, i have one sister, Josephine, even her ba zan ce maki ga yanda jikinta yake ba a yanzu, because in kin ganta a area da nake ma, to dad ne ya ce ta kirani or something like that".

Ɗan kwanciya ta yi a gefen kirjinsa tana faɗin "But why some peoples are calling you dangerous boss?. In the first place ka nuna mani you are the boss ɗin da gaske, and now kuma naga har da shagwaɓa ashe ka iya?".

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Ni ruwa biyu ne ai, a gida wajen mum da dad ina yi musu shagwaɓa, amma idan na baro wajensu, ba zaki taɓa cewa ma ina yin magana ba, bare shagwaɓa, kin taɓa kallona a class ina magana da wani ne? Or ina surutu?".

Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a.

Shafa gefen lallausan kumatunta da É—ayan hannunsa ya yi yana faÉ—in "Haka nake to, bana magana da mutane, kuma sunan dangerous, wait small, zaki san daga ina sunan ya samo asali kin ji?". Jinjina mashi kai ta yi tare da É—an yunkurawa zata bar jikin nasa.

Da sauri ya riketa yana kallon face nata. "Where are you going?". Da hannu ta nuna mashi saman sofarta ba tare da ta yi magana ba.

"Saman jikina É—in babu daÉ—in kwanciya ne?". Ya tambaya yana mai do da ita jikin nasa.

Girgiza mashi kai ta yi kafin ta ce "Akwai daÉ—i, amma ai kaga babu kyau ko? Mum ta hanani yin hakan". "Why mum zata hanaki kuma? Is there any problem akan hakan?". Ya yi tambayar da mamaki bayyane karara a saman face nasa, dan su rungumar juna, kiss, da sauransu ba wani abin bane a wajensu, shi ne yasa yake mamaki da ta ce zata bar jikin nasa.

"No any problem, kawai dai yin hakan kuskure, mum ta ce addini ya yi hani da hakan, so ni ba wani ilimin addinin nake da shi sosai ba, amma na iya karatun Alkur'ani mai girma sosai, saboda shi mum ta fi koya mini, amma dai koma me, is better na yi abin da ta ce koma yaya ne ko?".

Maimaita kalmar addini ya yi kafin ya tambayeta ita a wace addin take.

"I am a Muslim, what about you?". Ta bashi amsa with her full confidence.

Murmushi kaɗan ya yi, wanda da ka gani kasan dole ya ƙaƙalota, dan murmushi bata da gurbin zama a face nasa, duba da yanayinsa ba mutun ne mai fara'a ba sam sam.

"Am a Kristen, my name is William". A hanzarce ta miƙe daga jikinsa jin abin da ya ce, bata taɓa tunanin shi krista bane, duba da yanayin irin fuskarsa, yana da face mai kyalli sosai, idan ka ganshi, zaka yi tunanin yana sallah.

"Why are you avoiding me like that dan na ce am a Kristen? Shin da kika ce mini ke musulma ce did i do something like that to you?".

Girgiza mashi kai ta yi, sai kuma da ya yi magana ta fahimci ta yi kuskure na irin gudunsa da ta yi lokaci guda haka, yin hakan zai sanya ko da yana son shiga addinin musulunci ma, sai ya fasa, saboda zai ce dama haka musulmai suke? Dama basu son wani addini idan ba nasu ba?. Bai san mu musulmai kowa ma muna kaunarsa ba, kuma muna zaman lafiya da shi, addininmu mai sauki ne, addininmu mai ni'ima ne wanda ya bamu damar zama waje É—aya da wanda ba musulmi ba, mu yi zaman mutunci, kamar da Æ´an uwanmu musulmai muke tare, musulmai ne kawai za'a ci hakkinsu kuma su hakura, su yafe, su cigaba da zama da mutun, ai addinin musulunci babu biyunsa a duniya, ya yi ne kawai babu mai musawa sai dai wanda baya son gaskiya.

Shiru ta É—an yi tana Æ´an kame kame, ta rasa abin yi. A lokacin sam bata da wani ilimin addini sosai, haddan Alqur'ani mai girma ne kawai gareta, shi É—in ma ba dukka ba, kuma bata san fasarar ko sururori biyu daga ciki ba, so hakan yasa ta rasa me zata ce mishi, sai dai Æ´an kame kame, ilimin boko ya fi yawaita sosai fiye da misali a kanta sama da na addini, matsalar da aka samu kuma shi ne, ita bata wani zauna da su Brr Naurat sosai ba, secondarynta ma, boarding school ta yi, so bata sami lokaci da iyayenta sosai ba, shi ne yasa.

Ganin haka yasa shi ya miƙe ya koma saman sofar da take zaune. Kusa da ita ya zauna tare da ɗan riko hannayenta, cikin sanyin murya ya ce "Please kada ki gujeni, kin ji? I really love you the way you are, please love me the way i am, don't be angry because am a Kristen my angel, you hear?".

Wani sanyi ta ji a ranta na jin kalamansa, ta ji daɗi sosai, hakan yasa ta ji cewa zata iya janyo shi a jiki har ya karɓi addinin musulunci. Dan haka sai ta juyo da kyau suna fuskantar juna, cikin sanyin murya ta ce "I really love you the way you are, so don't worry!".

Sakin hannayen nata ya yi tare da buÉ—e mata hannu alamar ta zo gare shi. Ba musu ta faÉ—a jikinsa tana É—an murmushi, shafa bayanta a hankali ya fara yi yana mai jin daddaÉ—ar yanayi a tattare da shi.

"What is your name?". Muryarsa ya daki dodan kunnanta.

"A'isha". Ta bashi amsa, ɗan ɗago haɓarta ya yi yana faɗin "Nice nema, but can i call you my angel or my beauty?". Jinjina mashi kai ta yi alamar e. Ɗan kara matseta a jikinsa ya yi tare da sumbatar goshinta.

Haka suka kasance suna ta hira dan sanin juna har wajen karfe É—aya na dare. A nan ne ta ce mishi barci take ji, zata je ta kwanta. A kunne ya raÉ—a mata a kan cewa tare zasu kwanta a gado É—aya, Okey ta ce mishi.

Miƙewa ya yi da ita a jikinsa a in da ya gyara ɗaukarta da ya yi, ya zamana ya ɗaurata a saman kirjinsa, suka nufi cikin bedroom ɗin nata. Bai sauketa a ko'ina ba, sai a saman gadonta, murmushi ta sakar mashi kafin ta ce ta gode.

Hayewa gadon shi ma ya yi, daga É—an gefen da shi ta kwanta, ya so tambayarta me yasa har yanzu take gudun shi, amma sai kuma ya basar bai tambaya ba, sai ma ya juya mata baya, dan ya lura tamkar tana cikin damuwa na kwanansu gado guda.

A can gidansu kuwa, su Uncle Herry sai neman shi suke yi, sun je bedroom nasa baya nan, hankalin daddynsu ya tashi, ga shi ya bar musu wayarsa ma a gidan, mum ɗinsa har da kuka ta rinƙa yi, tamkar yaro ne karami William ɗin, mutumin da ya kai 24 years a duniya, amma sun ɗaga hankalinsu har haka, da yake shi gaskiya ba mai yawan fita bane na farko, na biyu idan ma zai je party ko gidan rawa, yana gayawa mum ɗin nasa shi fa ya tafi waje kaza, kuma ba zai dawo ba sai time kaza, idan ya ce hakan, to time ɗin na yi zai dawo abinsa, hakan tasa suka ɗaga hankalinsu sosai da basu gan shi ba.

Shi kuwa shiru ya kwanta ya kasa yin barci, baya son gaya mata ne or ta gane, amma ji yake yi tamkar a cikin keji yake, gidan nata ya yi mishi ƙarami over, duk ya takura, dan fa su gidansu, gida ne na madarar kuɗi, babban yayan daddynsu shi ne president mai ci a yanzu, ga uban kuɗi da suke da shi na wuce misali, gidansu aljannar duniya ce guda, bedroom nasa kawai ya kai girman gidan nata gabaɗaya har da palo da kitchen, so bai saba da ƙaramin waje haka ba, duk sai ya takura.

Ita ma ta kasa barci saboda tsananin tsoronsa, sai taga kamar idan ta yi barci, zai yi mata wani abin, dan fa gani take yi kamar fyaÉ—e ya zo yi mata kamar yanda ya nuna mata tun farko.
Chapter 6 · 0% Book details