Sashe 34
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A hankali ta waro idanun bata tare kumbura kumatu. Zubawa juna idanu suka yi, yau É—aya ta iya dakewa ta kalli cikin kwayar idanunsa, anya ita ce ta iya wannan juriya na kallon cikin idanunsa kuwa? Anya babu sa hannun Malika a ciki kuwa? Shi ma ya É—an yi mamakin yanda ta zuba mashi idanu tana kallon shi, babu ko kyaftawa.
"Noorish meyasameka?". Ta yi maganar tana kai hannunta a saman kumatunsa. Riko hannun nata ya yi tare da manna shi da jikin kumatunsa ba tare da ya saki ba, ya haÉ—e hannayen nasu waje guda a wajen, shiru bai yi mata magana ba, ita kuma sai kallon mamaki take yi mashi, taga ya yi wani irin rama ne, ita dai tasan kafin ta yi barci, ba haka ta barshi ba, ga idanunsa sun kara girma, alamar ya rame kenan.
Baki É—auke da sallama Aseef ya shigo cikin É—akin. Juyawa ta yi tana kallonsa, sai kuma ta yunkura zata bar jikin Lion É—in, sai dai bai sake ta ba, yana rike da ita, yana ta kallon face nata, shi kaÉ—ai yasan me yake ji a duk lokacin da yake kallonta.
Sam Aseef bai bi ta kansu ba, saman bed ya haye abinsa, ya kwanta tare da ciro wayarsa ya fara aikin latsawa, sai dai fa ya sha ruwan mamakin na ganinsu a manne da juna, kawai baya son ya yi magana ne, dan kada ya katse masu jin daÉ—insu.
Mark ne ya sake shigowa cikin É—akin, kallo É—aya ya yi masu ya kawar da kansa gefe, sannan ya wuce dan ya yi aikin da ya kawosa.
"Meesha zaki raka ni ƙasar China?". Ya faɗa a sanyaye, tamkar bai san da Mark da kuma Aseef a cikin ɗakin ba.
Jinjina mashi kai ta yi tana faÉ—in "E zan raka ka".
Shiru ya yi yana tunanin a ina zai sami Cherish? Dan ba shakka duk yadda aka yi, tana da sa hannu a duk abubuwan da suke faru, saboda very close friend ɗin gwaggo ce, ya za'ayi daga haihuwar gwaggon shikenan ace Cherish ta ɓace? Ko dai dama ita ma ba mutun ba ce? Wannan abin da akwai ruɗani, dole ya nemo jigon haɗa wannan rikicin dukka.
Sallamar Areef ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka, tun da Areef É—in ya shigo, ya tsare shi da idanu har ya kariso cikin É—akin, a saman bedside drawer ya zauna yana faÉ—in "Kai Aseef momma tana nemanka kana nan ko?".
Turo baki ya yi yana faÉ—in "Ni ba zan je ba, kuma fushi nake yi da su, saboda sun ce wai ba zan yi punishing na Heartbeat ba, a kan me zata fita bata tambaye ni ba? Ni gaskiya ba zan kyaleta ba!".
Sake Rimshar Lion É—in ya yi yana mai dawo da kallonsa a kan Areef dake kare mashi kallo shi ma. "Me kake zuwa yi a wajen Josephine time da kake zuwa wajenta?". Shi ne tambayar da Lion É—in ya wurga mashi.
Miƙewa daga jikinsa Rimshar ta yi, sannan ta nufi kofar fita. Hannunta Areef ɗin ya riko yana tsokanarta "Sister yau kin mance da ni ko? Wato ma fita zaki yi kamar baki ganni ba ko?".
Katse shi Lion É—in ya yi da cewa "Saketa ta wuce, sannan ka juyo ka bani amsa ta".
Kasa sakin nata Areef É—in ya yi, dan shi ya ji ne ma kamar bai san wacece Josephine É—in ba, baya son a kawo mashi maganarta, dan haka sai ya ce "Wai kai Lion ka bari mu gaisa da ita mana".
Sosai Aseef ya yi mamakin abin da Areef ɗin ya yi, shi dai a iya saninsa ya san cewa Areef ɗin yana yawan tsawatar mashi a kan kada ya kuskura ya rinƙa rungumar Rimsha, or ya kamata hannunta a gaban Lion, idan ba haka ba, to za su yi babu daɗi da Lion ɗin, dan wannan uban kishin nasa, to ya aka yi yau shi kuma Areef ɗin da kansa ya rike mata hannu, kuma har Lion ɗin ya ce ya saketa, amma yaki, anya kuwa babu wata alamar tambaya a nan?.
Shi kuwa Lion ɗin sam bai ɗauki zafi ba, saboda ya lura, yanzu koma ta halin ƙaƙa, so ake a kai shi ƙasa, so ake a rinƙa fusata shi, yana ɗaukar zafi, har ta kai ta kawo zuciyar ta kasa ɗauka, ta buga ya mutu kowa ya huta, tun da ya fahimci haka kuwa, to ba shakka zai yi taka tsantsan wajen ganin ya danni zuciyarsa ba zai ɗauki zafi ba!! Wannan shi ne yaki sunkuru, Lion dai yana faɗa da aljani, shi baya ganinsu, amma su kuma suna ganin duk wani motsinsa.
Hannun Rimshar ya riko tare da jawota ta dawo jikinsa, cikin sanyin murya ya ce da Areef É—in "Now amsa me".
Ita dai Rimsha yau tana ganin abin mamaki, ta lura yau gabaÉ—aya TRIPLETS É—in a tsai tsaye suke magana da junansu, kamar ba lafiya ba, magana suke yi kai tsaye kawai.
"Saif ni ba wani abin da nake zuwa yi gidanta face gaisuwa, shi kawai nake zuwa yi".
Aseef ne ya amsa da cewa "Ba wani gaisuwa, akwai dai abin da yake kaika, Allah gara ma ka rabu da matar nan, duk da cewa ta taimakawa Momma a baya". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa zaune yana wani yamutse fuska.
"Anywhere zamu koma Washington gobe idan Allah ya kai mu, kuma gabaÉ—ayanmu zamu tafi, saboda mun gama abin da ya kawo mu Naija, so idan mun bar Naija, mun barta kenan har abada!". Cewar Lion.
Da sauri Rimsha ta É—ago kai tana kallonsa, da mamaki fal a face nata ta ce "Noorish to ita kuma gwaggo fa?".
Shiru ya yi bai amsa mata ba. Areef ne ya amsa mata da cewa "Da Momma da ke da my baby, Heartbeat, dukka zamu tafi da ku mana, ai ku kun sallami Naija kenan".
Zaro dara daran idanuwan nan nata ta yi, a tsorace ta ce "To daddyna da mummyna fa?".
Aseef ne ya amsa mata da "A nan zaki barsu mana".
Sam bata san time É—in da ta furta, "Na shiga uku na! Wlh ni ba zan je ko'ina ba, sai dai ku tafi ku barni". Bata san time É—in da ta furta hakan ba, sai da ta ga irin kallon da Lion ya wurga mata ne, nan ne ta fara tunanin wai shin me ta faÉ—a nema?.
Gwaggo ne ta katsesu ta hanyar shigowa cikin É—akin bakinta É—auke da sallama. Ita ma tun da ta shigo Lion ya tsareta da idanu yana kare mata kallo, wani irin tausayinta ma yake ji a yanzu, an cuceta ba kaÉ—an ba.
Da sauri Rimsha ta bar jikinsa, ta nufi gwaggon tana dariya. Rungume juna suka yi, a tare suka kariso cikin É—akin. A gefen gado kusa da Lion ta zauna, ita kuma Rimsha ta zauna a gefenta tare da kwanto da kanta a saman kafaÉ—unta.
"Saif kuzo muje palo, akwai maganganu da zamu tattauna da su Abban Imran and Brr". Cewar gwaggon kenan.
Jinjina mata kai ya yi yana faɗin "Ki shirya gobe zamu koma ƙasarmu".
Har tana haɗe word wajen cewa "Wace ƙasa kuma?!". Shiru ya yi bai bata amsa ba. Areef ne ya amsa mata da kasar da ake nufi, wato Usa.
"A'a ni zan zauna a cikin Æ´an uwana, ku dai ku koma, duk time É—in da kuka sami lokaci, sai ku kawo mani ziyara".
Miƙewa Lion ɗin ya yi ba tare da ya sake yin magana ba, ya nufi waje abinsa, dan ya san babu abin da zai hana su tafi da ita, ta gama zantukanta dukka, Nigeria kam sai ta barta..........Babbar magana.
Miƙewa suka yi dukkansu suka rufa mashi baya. A palo suka isko su Abba gabaɗaya, sai hira suke yi, amma ga dukkan alamu, suna cikin matsananciyar damuwa.
Saman sofa Lion ya zauna yana kallon baban Muneer dake a tsakiyar palon, Areef ya É—aure shi da igiya kamar ba lafiya ba, ga bakinsa a kumbure suntum. Da kallo É—aya ya yi wa baban Muneer É—in ya fahimci koma me wannan dai ba mai laifi bane, amma sai bai tambayi meyayi suka É—aure shi haka ba, ya zuba idanu kawai yana kallonsu, dan shi ciwo ma kansa take masa.
Tun É—azun Akila sai jin sautin Muryar Ablah kanwar Haroon take yi ana kiranta, tun ana kiranta daga nesa har ta ji an matso kusa, sai ta ji kamar a harabar gidan ma ake kiranta.
Mikewa ta yi tare da gaya masu tana zuwa, tana fita daga palon shikenan ɓat ta ɓace tamkar wata aljanna, an ɗauketa. To fah.
Su kuma jama'ar cikin palon, Brr Naurat ce ta yi gyaran murya tare da fara yin magana cikin dattaku da nutsuwa. Nasiha ce mai ratsa jiki ta yi wa Ummin Dr Nawid, sannan ta ce mata ko sun ɓuyo mata yanzu, gaba dole zata sani, to gara su gaya mata kawai, ta yi hakuri Allah ya yi wa Dr Nawid rasuwa.