← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 168

Sashe 46

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gida kuma, komawa cikin gida gabaÉ—aya family suka yi. A palon sama suka zauna, rarrashin Rimsha da Anaya suka hau yi, da kyar suka samu suka yi masu shiru, ita Rimsha ta tada kai da laps É—in gwaggo, barcin wahala da kewar mijinta ya É—auketa, ita kuma Anaya ta tada kai da laps É—in Brr Naurat, sai tunanin Mark nata take yi, tana bin jama'ar palon da kallo, ita dama Jehan already tana barin wajen bedroom nasu ta koma, saman bed ta haye, haka ita ma ta murji kuka tamkar babu gobe, daga haka barci ya yi awon gaba da ita cike da tunanin mijinta kuma abokin diramarta, yau ina zata sanya ranta? Ya tafi ya barta, yau babu tsokana, yau babu rigima, Allah sarki, dukkansu gwanin ban tausayi.

Bayan ƴan kuka sun yi shiru ne Brr Naurat ta sami damar nuna masu Abba Alex, cike da murna suka rungumi ɗan uwansu, duk da cewa daddyn Rimsha da daddyn Anaya suna kama sosai da Brr Naurat, amma Alex ya fisu kama da Turawa sosai, shi ba zaka taɓa cewa Dr Salman bane ma mahaifinsa, saboda shi da su Trump wato kakan Mark ya yi kama, da su yake muguwar kama, duk cikin ƴaƴan Brr babu mai wani irin launin idanu irin na ƴan uwanta, sai shi Alex ɗin, shi kaɗai ne mai blue eyes irin nasu Trump, sai kuma a cikin jikokinta, kanwar Anaya Zaira, idanunta ash color ne, sune kawai masu wani launin idanu ta ɓangaren Brr.

Daddyn Anaya ne ya katse masu hiran da cewa "Daughter a ina kika san wannan mutumi da kika rike yanzu kina kuka?". Tana daga kwance, babu kunya ko ɗigo a idanunta, cikin tsantsar shagwaɓa ta fara magana. "Daddy Mark ne fa, kuma shi nake so, kuma shi ma yana sona, kullum ma yana yawan ce mani na gaya maka yana son kawo maka ziyara".

Cikin nuna ko in kula, bai É—auki zafi ko kaÉ—an ba, dan wayayyun mutane na wuce misali, sun kwankwaÉ—i boko, dan haka sai ya ce "To kin san shi ne? Su waye iyayensa? Kuma a ina yake?".

Turo baki ta yi tana faÉ—in "Daddy dukka wannan shi zaka tambaya mana, ni ban san kowa nasa ba bayan mijin Rimsha da yake ogansa, shikenan".

Salatin mummynta ta sanya tana faÉ—in "Yanzu daughter baki san iyayensa ba, baki san halinsa ba, kawai ke Æ´ar soyayya sai kika fara son shi ko? Wai ni yaushe ma kika girma ne? Yau ga ikon Allah, ko secondary school fa yanzu kika fara, amma kike zancen son wani?".

Kuka ta saka masu tana faɗin "Daddy baka ga mummy ba, yanzu zaki fara ko mummy? To ai shi yana da kirki, kuma ai kinga idan bashi da kirki ba zai zauna a gidan nan ba, ni mummy dan Allah ki bari mana, ke komai mutun ya yi sai kin yi complain, sai ki rinƙa cewa mutun yarinya, kullum ba'a kara girma a wajenki, kullum sai naci marking sosai a school, amma sai kice bana ƙoƙari, daddy ne kawai yake cewa ina ƙoƙari, shiyasa fa yanzu zan dai'na nuna maki papers ɗina, daddy da Yah Feroz kawai zan rinƙa nunawa". Ta kai karshen maganar tare da mikewa daga kwanciyar da ta yi, tana turo baki ta sa kai zata wuce izuwa ɗakinsu Rimsha.

Daddyn nata ne ya dakatar da ita ta hanyar cewa "Zo nan abinki my daughter, rabu da mummy, ni nasan yana da kirki sosai, yanzu dai zo ki gaya mani a ina yake aiki dan na binciko wanene shi?".

Ba musu ta nufi daddyn nata, a jikinsa ta kwanta tana tura baki tana faÉ—in "Daddy kai'na yana yi mani ciwo, ni ba zan iya jure Mark ya je wannan waje ba".

Dafa kan nata ya yi tare da fara ce mata sorry, Zaira ƴar auta tana zaune shiru kusa da daddyn Jelly, baiwar Allah sam bata da rigima, tamkar ba ƴar auta bace ita, Anayar da take babba ta fita yawan rigima da shagwaɓa.

Brr Naurat ce ta katse masu zancen da cewa "Mark dai jika ne ga babban yayanmu, haka jika yake a wajena kamar yanda kuke jikokina, so bana tunanin mutumin banza ne, tunda har yana tare da su Saif, to a gaskiya shi ɗin ba mutumin banza bane, a gabaɗaya su Saif babu na banza a cikinsu, kuma sai hali yazo ɗaya ake abota, dan haka ina kyautata mashi zato, kuma ina farinciki da Allah yasa jinin babban yayana zai auri nawa jinin, duk da sun gujeni, sun koreni a cikinsu, to ga shi Allah zai sake haɗa ni zumunci da su ta kan jikokinmu kuma, mu zamu aurawa Mark Anaya in har tana son shi yana sonta, shikenan sai ya karɓi musulci ayi masu aure".

Kusan a tare dayawa daga cikin jama'ar palon suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya, daddyn Anayar ya ji daÉ—i sosai, ita kuwa Anaya cool murmushi ta saki tana faÉ—in "Good Æ´ar tsohuwa that's why i like you, ashe gwara da baki mutu bama, ga shi kin yi amfani".

Ita dai mummyn Rimsha baiwar Allah, duk kunya ya rufeta, kunyar Brr Naurat ma take ji sosai, ga su Abban Imran dukka surakananta ne, hakan yasa duk ta takure waje guda,. A duk cikin palo ita da aunty matar Abbi ne kawai suka san menene kunya, sune kawai masu kunya, ita ma Ammien su Imran ba kunya ke gareta ba, kowa yasan kabilar igbo dai ba kunya ce da su ba. Duk Anaya ta san mummyn Rimsha ta ji wani irin kunya, ta kuma ga laifin mummyn Anayar sosai, dan kome Anaya zata yi a yanzu, to laifin mummynta ne, saboda Anaya yarinya ce, kuruciya na a kanta sosai, tun farko ya kamata mummyn nata ta koya mata kunya, kamun kai, kamala, da dai sauransu, amma ji yanda Anaya take magana abu sam babu tsari, iyayenta ne a cike a cikin palon nan, amma ita babu ruwanta, tamkar da sa'aninta ko kannanta or kawayenta take hira, abin sam bai yi wa mummyn Rimsha daÉ—i ba, bayan ita da Aunty kowa a cikin palon babu wanda ya ga aibin abin da Anayar ta yi, shi ma daddyn Rimshar bai ga aibin hakan ba, dan a cewarsa, ai yarinta ce kawai tasa Anayar yin hakan, idan ta girma zata dai'na........Babban magana girma kuma na nawa?.

Haka suka cigaba da zuba hirarsu har zuwa rana ta ɗago, Anayar ma tuni ta yi barci a kwance a saman laps na daddynta, sai sauke nauyayyar ajiyar zuciya suke yi a cikin barci, sun sha kuka sun ƙoshi, ita ma Jehan barci ne ya ɗauketa, ta ci kuka kamar ba gobe.

After 2 days.

A cikin wannan kwana biyu da suka wuce, abubuwa da dama sun faru, bari mu fara da ɓangaren su Lion, sun isa Enugu state lafiya, kamar yanda Ammie ta basu address ɗin gidansu, haka suka yi amfani da shi, sai dai ko da suka je, gidan babu kowa, gate ɗin gidan ma a rufe yake ruf, da alama an ɗauki lokaci babu mutane a cikin gidan.

Zubawa gidan idanu sosai Lion ya yi, kai daga ganin gidan kasan ba iya kuɗin nema ne kawai ya gina shi ba, wannan uban kuɗi da aka narka wajen gina gidan, ai dole sai da kuɗin TSAFI, dama already Ammien ta gaya masu Queen bata zama a gidan, bata nan a cikin gidan, kuma gidan babu kowa, dan haka ko sun je, wahala za su sha, shi kuma Lion abin da kuka sani ne, a duk lokacin da ake magana, to yana nutsuwa ne ya saurari maganar da kyau, dan tattare zancen mai maganar a cikin ƙwaƙwalwarsa yake yi, saboda samun mafita, yana aiki ne da kaifin basirarsa sosai da sosai, a lokacin da Ammien take bada labarin Daular Mutuwa, a lokacin ya nutsu sosai yana jinta, a maganarta ta ce a baya tana shiga har cikin Daular Mutuwar, which means da akwai hanyar da zai sadaka da Daular Mutuwa daga ta cikin gidan kenan, kuma dama ai da kamar wuya ace babu wata hanya daga cikin gidan Queen da zai sadaka da Daular, tun da ita ce shugaban Daular, to dole akwai hanyoyi ma ba hanya ɗaya ba ta cikin gidanta, hakan tasa ya ce da Ammien ta bashi address na gidan Queen ɗin, kun ji masu hikima da basira, ita kuma Ammien sam bata kawo cewa da haka zai yi amfani ba, dan ita bata taɓa shiga Daular Mutuwa daga ta cikin gidansu ba, ta waje take shiga, Queen ta ɓoye masu hanyar cikin gidan, hanyar sirrice wanda babu wanda ta yarda ya sani, sai ita kaɗanta.

Duk sojojin sun tsaya suna jiran su ji me Lion É—in zai ce, basu ankara ba sai ganinsa suka yi ya yi bismilah ya kama gate É—in gidan ya haye, dan ba mutane a cikin gidan.

Wani abin da basu sani ba shi ne, tun da suka baro garin Kaduna a kan idanun Queen suke tafiya, har suka iso Enugu, duk motsinsu tana ganinsu, ta barsu ne kawai su iso, dan a cewarta a cikin satin nan, suna da liyafa a gidan nata, dodan tsafinsu na bukatar jini sosai, akwai wasu sabbin ma'aikata da suka karu, dama idan baku manta ba, duk waÉ—an da suka jima a Daular Mutuwa, in dai Queen ta kasa kashe su, to tana mayar da su mutanenta ne, sai ta juyar da su izuwa irinsu barbushi, to akwai wasu mutane guda biyu ciki har da Mustapha da wani, a satin nan za'ayi liyafar mayar da su mukarraban Queen, wato su zama magicians suma. BABBAR MAGANA, shi ne yasa Queen É—in ta bar su Lion É—in su iso kawai ta bawa dodan tsafinsu su, asha jininsu a ji daÉ—in yin liyafa da kyau, har shiga cikin gidanta da suka yi a yanzu, duk tana kallonsu, dariya ma suke bata.
Chapter 46 · 0% Book details