← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 168

Sashe 92

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

Date: 8/5/2024

E27

Da kyar mai motar ya iya taka birki, saboda yanda kan motar ta so ta kwace mashi.

Bai tsaya dai'dai ta nutsuwarsa ba ya fito a hanzarce, dan ya duba ko tana raye ko ta mutu.

Dai'dai lokacin shi kuma Abbo ya karisa wajenta da nufin ya É—auketa.

"Hi guy, where will you take her to?". Ya yi maganar cikin ƙwararriyar harshen turancinsa, kuma ya yi maganar yana nufosu, sanye yake da wandon jeans baka mai shegen kyau, sai army's T-shirt daga ta sama, kafafunsa na sanye cikin wasu kyawawan tsadaddun Booth mai matuƙar kyau, launin black color, ya saki gashi har bayan wuya, sai kamshi yake zubawa.

"She is my daughter, i want to take her to hospital". Ya bashi masa shi ma cikin harshen turanci ba tare kuma da ya É—ago ya kalli wanene bane, shi dai burinsa kawai ya É—auketa su bar wajen.

Jin hakan yasa Tga É—in ya juya ya nufi wajen motarsa ba tare da ya sake yi masu magana ba, dama idan baku manta ba shi baya son bakaken fata, yanzu ma abin da yasa ya fito dan yaga wanene ya buge ne, saboda a matsayinsa a soja bai kamata ya taka dokar kowace kasa ba, hakan ce ma kawai tasa ya fito, to tun da ya ji mahaifinta yana wajen, sai ya koma cikin motarsa da nufin ya bar wajen kawai.

Kunna motar ya yi tare da ɗan yin reverse, dan ya samu damar wucewa. Kamar wanda aka yi wa allura, sai wani tunani ya faɗo mashi a cikin ransa, idan har da gaske wannan mutumin mahaifin yarinyar nan ne meyasa baya kuka da ya ga an bugeta? Meyasa bai nuna damuwa da tashin hankali ba? Ko dai su mutanen Nigeria haka suke basu damu da ƴaƴan su ba ne?. Waɗan nan sune tunani da tambayoyin da suka faɗo mashi a cikin ƙwaƙwalwarsa kamar wadda aka yi wa allura.

Shiru ya É—an yi kafin ya ce yes maybe mutanen Nigeria haka suke, basu damuwa da Æ´aÆ´an su ne. Tuna hakan yasa ya ja motarsa ya bar wajen.

Shi kuwa Abbo hannu ya kai da nufin ya ɗauketa, sai ya ji a yanda yake ɗin nan fa ba zai iya ɗaukarta ba, dole sai ya canza zuwa matashi mai jini a jika idan yana son ɗaukarta. Dan haka sai ya fara ƙoƙarin canzawa izuwa matashi. Cikin ƙanƙanin lokaci ya canza izuwa santalelen matashi, da yake dare ne, jama'a sam babu kowa a saman titin, dama kuma kunsan irin waɗan nan manyan unguwanni ba kasafai ka cika ganin mutane a waje ba, sai dai jefi jefi kaga giftawarsu, hakan tasa babu wanda ya nufi in da suke.

Yana ƙoƙarin ɗaukarta wasu matasa su biyu daga bayansa suka yi mashi sallama tare da tambayarsa ko lafiya? Accident aka yi ne?.

"Mota ce ta buge mani yarinya ta, kuma mai motar ya gudu, shi ne zan É—auketa zuwa gida, daga nan sai mu wuce asibiti".

A hanzarce matasan suka ce "Innallilahi wa inna ilahirrajiun, wannan ai gaggawar kaita asibiti zamu yi, idan ba haka ba tana iya rasa ranta, bakaga yadda take zubar da jini bane? Ameer mu taimaka mashi".

Jin haka yasa Abbon ya juya idanun tsafin nasa tare da juyowa ya kallesu, nan take suka juya suka kama kansu, da alama shi ne nan ya kawar wa da mutanen arean gabaÉ—aya hankalinsu daga kansu, haka su Ameer dai suka juya salamun salamun suka bar wajen, tun da suka juya kuma basu sake waigo shi ba, da haka suka tafi.

Santalelen matashi mai jini a jika ya rikiÉ—a ya koma, hannu ya kai a karo na uku zai É—auketa, kamar daga sama ya ji daga bayansa an ce "Am doubting about what you said, this girl isn't your daughter, am a soldier, you look like a criminal in my eyes, so i have to be come back and check you very well, that's why am here!". Cikin nustuwa ya yi maganar, kamar Lion idan yana magana.

A razane ya juyo, dan ya ga wanene, kun san É—azun dama bai É—ago ya kalli Tga É—in ba.

Yana juyowa kuma ya jefa kwakwalwar Tga É—in a cikin tunani, saboda a iya saninsa dai É—azun babban mutun ya gani ba matashi ba, ya aka yi yanzu kuma ya dawo yaga mata shi? Shi ne abin da ya É—an juyar mashi da tunani kenan.

Shi kuwa Abbon, ganin Tga É—in ba karamar razana shi ya yi ba, saboda abin da kuka sani ne, Tga tsayayyen namiji ne mai jini a jika, lafiyayye kuma horarre, ga kirar karfi, idan ka ganshi kamar TRIPLETS yake, basu da banbanci sai É—an abin da ba'a rasa ba, so dole duk wani mutun idan ya gansu sai ya ji gabansa ya faÉ—i, musamman ma wannan Lion face É—in nasu, da yake cike da kwarjini na wuce misali, ga kuma hasken fitillu a kan hanyar ko'ina, so suna iya ganin juna sosai.

Ƙoƙarin juyarwa da Tga ɗin hankali Abbon ya yi, amma ina ya kasa, tsafinsa taki yin aiki a kansa, abin ya razana shi, ya kuma yi mugu mugun ɗaure mashi kai, meyasa tsafinsa ta ƙi kama Tga? Ya tambayi kansa. (Ni kuma nace saboda Josephine tana kula da su😒🤧 ba zata taɓa bari a cutar da su ba, sai dai idan an shanmaceta)

Shi kuma Tga ganin cewa wanda ya gani É—azun da wanda ya gani yanzu ba mutun É—aya bane yasa ya nufe shi gadan gadan, yana taku cikin nuna jarumta tare da nuna cewa shi É—in tsantsar lafiyayye ne.

Yana zuwa bai yi wata wata ba ya damko wuyar Abbon tare da shakesa da karfin, calmly ya ce "Who are you? What do you want to do for her? Where's that man that i saw in the first place?". Ya kai karshen maganar tare da É—aga Abbon da hannu É—aya kuma da wuyarsa da ya damke, ya raba shi da kasa sannan ya yi wurgi da shi gefe guda. Dama kunsan halin uncle T da iya mugunta, baka yi mashi laifi bama ya iya zalunci bare kuma yana zarginka, ai sai abin da hali ya yi kawai, sai ya baka a jikinka kafin ya baka damar ka yi mashi bayani.

Gadan gadan ya sake nufarsa, sai dai abin al'ajabi kafin ya kai in da yake yashe a kasar ya yi amfani da tsafinsa ya ɓace ɓat ya bar wajen. Dakatawa da nufar wajen Tga ɗin ya yi, da mamaki yake kallon wajen, da gaske ya ɓace, babu shi babu labarinsa, abin mamaki. Abin ya ɗan ɗaure mashi kai, sai dai ko kaɗan bai bashi tsoro ba, babu tsoro ko ɗigo a jinin familyn Roshan, haka suke tun ainahi, daga manyansu har kananansu basu da tsoro, bare kuma shi Tga da yake horon Lion, ai dama tsoro ma bataga wajen zama a wajensu ba.

Juyawa ya yi ya nufi wajen da take kwance cikin jini, da farko kamar ba zai ɗauketa ba, amma da ya tuna yanda Abbon ya ɓace, sai ya sawa ransa cewa cutar da ita zasu yi, dan haka bari ya taimaka mata.

A gabanta ya zo ya tsugunna, dan ya duba ta ina zai fara É—aukar tata. Zubawa face nata idanu ya yi, sosai ya ga kamanninta da su Imran, kun san an ce jini ba wasa ba, a zahirin gaskiya bata wani kama da su Imran, amma da yake jini ya wuce wasa, akwai kaman jini a jikkunansu, kuma kowa da yanayin yanda yake kallon mutun, sai kaga mutun ya yi maka kama da wani, idan ka tambayi jama'a kuma sai su ce maka a'a babu kamar da kai kake gani, so kowa da yanayin yanda yake ganin mutun, shi dai Uncle T ta yi mashi mugu mugun kama da su Imran, sai dai kuma fa ba iya kamar kawai ya tsaya gani a face É—in nata ba, tsintar kansa ya yi da jin sha'awar kallon face É—in nata duk da baya son bakaken fata kuma bashi da wata ra'ayi a kan mace, amma ba shakka face É—in Aafia ta tafi da tunaninsa a kallon farko.

Ya ɗan ɗauki lokaci yana kallonta kafin nan ya tsinci kansa da kai hannu ya taɓa kumatunta. Wani irin sanyi kamar daskararren ƙanƙara da ya ji a tattare da face ɗin nata ne yasa ya ɗauke hannunsa da wuri tare da miƙewa ya saɓeta da hannu ɗaya a saman kafaɗarsa, alama ta nuna babu jini a jikinta, baiwar Allah dama ba isshasshen lafiya yake gareta ba.

Anya basu Abbon bane suka zuƙe mata jinin⁉️

Gidan baya na motar ya buÉ—e tare da shumfuÉ—eta a saman lallausan kujerar motar, sannan ya koma mazaunin driver da sauri, saboda tana zubar da jini kuma alama ta nuna babu jini a jikinta sosai.

Da gudun gaske ya figi motar ya bar wajen, dama fitowa ya yi zai je shopping, saboda akwai abubun amfaninsa da suka kare, dama shi already kun sani kamar Areef yake, akwai shi da yawace yawace idan ya zo waje, kun tuna farkon zuwansa Naija wani lokaci ma baya kwana a gida? Kun tuna lokacin? Yawonsa yake tafiya dan ya ga gari, hakan tasa ya san wajaje da dama a cikin garin Kaduna.
Chapter 92 · 0% Book details