← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 168

Sashe 148

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda kuka sani ne a bisa ka'idarsu Lion ko in ce shugaban kasar zai je wajen ne tare da matarsa, to hakance ta kasance, tare suka shirya da shi da Meesharsa. Duk da cewa kowa yasan da cewa Lion ya musulta, domin ya yi editing na komai da komai nasa ya cire sunansa na Romeo William Jacob izuwa Saif William, duk da sun san da hakan, dan kafin ya yi hakan sai da sanin ƴan jarudu kamar yadda yake a dokance, amma kuma abin ya yi matuƙar basu mamaki na ganinsa tare da Rimsha kuma cikin shiga irinta addinin musulunci, sun sha mamakin ganinta cikin complete shiga ta rufe komai nata.
Sanye take da farar abaya mai bala'in kyau da tsada, sai ɗaukar idanu yake yi tsabar kyansa, ta yi rolling na veil ɗin abayar a kanta, sannan ta sanya face mask mai bala'in kyau irin na mijin nata a face nata, hannayenta da kafafunta dukka suna sanye cikin safa fara kal, ta yi kyau iya kyau duk da tana cikin face mask, watch da Lion ya ɗaura mata a hannunta kawai ya ɗauki idanun duk jama'ar da suke wajen, wani dankareren diamond watch ne wanda sai Allah kaɗai yasan a ina ya sawo mata shi, kuɗin wannan watch ɗin kawai ta isa ta sayawa mutun dankareriyar gida a malali Abuja, ga shi watch ɗin ɗan dai'dai da hannunta, duwatsun da aka yi wa wannan watch ɗin kwalliya ba ƙaramin ɗaukar idanu kyallinsu yake yi ba, daga wuyarta zuwa kunnenta dukka wasu shegun gwala gwalai ne wanda Josephine ta sanya mata, dan ita Josephine ɗin ita ce ta yi mata kwalliya yau, sai tashin kamshin perfume ɗin Lion ɗin take yi, sai dai kuma ta kara zama baka sosai a cikin masu jajayen kunnuwar.

Shi kuwa Lion sanye yake cikin wasu shegun tsadaddun suit masu bala'in kyau launin white color irin kalar kayan jikin Rimshar, ya tara kyakkyawar dark black curly hairnsa a baya ya ɗaure, sai face nasa ta fara fitowa sosai, sai dai kuma duk wannan uban kyau da ya yi fa fuska a ɗaure tamau kamar hadari, yau ya sanya siririn glass mai bala'in kyau a face nasa, sannan ya sanya face mask, cover shoes ce a ƙafarsa, kuɗin duwatsun dake jikin cover ɗin nan kawai ya isa ya buɗewa mutun katafaren mall mai cike tab da kaya, kusan takalmar kafarsu iri guda dana Rimsha, ita ma cover ce mai kwalliyar duwatsu masu bala'in kyalli a jiki, sai dai nata na mata ne nasa na maza, komai na jikinsu from up to down farare ne kal kal, tsadarsu kuwa baki bai isa ya faɗi kuɗinsu ba.

Tun da suka shigo white house Lion yake ruke da hannunta, ya kuma ɗan mannata da jikinsa dan ma kowa ya sani cewa ba son wasa yake yi mata ba, kuma ita Rimsha ma bata iya tafiya sosai, kafarta yana ciwo, shi ne ma yasa Josephine ta ce ta sanya cover shoe plat wanda Lion ɗin ya saya masu a tare, da ita Rimshar a yarintarta high heels zata saka, ita da kafa yake ciwo, Lion ya ragargajeta jiya, hakan yasa bata iya tafiya sosai, karfin hali ne ma kawai irin nata, da farko ma cewa ta yi ba zata je white house ɗin ba, sai da ya lallaɓata sannan ta yarda da cewa zata je.

Ita dai mummyn Rimsha kunya abin yake bata, yadda Lion ya wani rungume matarsa kamar ance za'a kwace mashi ita, gwaggo kam ko a jikinta, hannunta ita ma yana a cikin na Dr William kamar wasu taurari, kusa hasken fatar Dr William dana gwaggon É—aya, da kaÉ—an ya fita, sun fito a iyayen QUADRUPLE É—in da gaske, sai haskawa suke kamar wasu sabbin taurari.

Sam mummyn Rimsha taki yarda daddy ya riko hannunta a bainnar nasi, sai dai suka nufi cikin a jere kawai, saboda tana kunyar su brr Naurat. Shi kam Aseef da akwai dama ma ai ɗaukar Heartbeat cancak zai yi ya saɓata a shoulder ɗinsa su shiga ciki, dan baya son ta sha wahala, kada ta jijjiga mashi baby.

Areef da Jehan ma haka suka jero gwanin birgewa, yana ƙanƙame da hannunta. Sir Safwan da Maryam haka suka jera rike da hannun juna, duk kuma shirin Josephine ne, Uncle T tare da Aafia, Mahhir tare da Adiva, Dr Salman and Brr Naurat suna rike da hannun Pinky, Mark tare da Anaya, sai aikin turo baki Anaya take yi wai bata son zuwa, da kyar ita ma ya lallaɓata ta yarda ta biyo shi.

Tamkar wasu taurari haka familyb Dr Salman and Familyn Dr William suka shigo white house, a kalla dankara dankaran motoci sama da guda hamsin ne suka É—aukosu daga gida, hakan zai tabbatar maka da Lion ya shirya abubuwa sosai, dan motocin gabakiÉ—aya sababbi ne gal gal, babu tsoho na gida ko É—aya a ciki.

His Excellence ma yazo taya Lion murna, kuma dama dole ya zo, dole ya kasance yana wajen, dan shi ne zai miƙawa Lion ɗin mulkin.

Manyan shuwagabannin kasashe da dama sun halakci taron rantsarwar. An kawata white house ɗin nan na wuce misali, baki ya yi kaɗan ya zayyana yadda kawatuwarsa ya kasance, har shi kansa speaker room dake a cikin fadar shugaban kasar, komai sai dai mu ce masha Allah, billions of dollars aka narka wajen sake kawata white house ɗin, saboda sabon shugaba zai shi ga, tsadaddun motocin da aka zuba na fitar President a cikin white house ɗin ma kawai kuɗin su ya kai kuɗin budget ɗin wata ƙasar, dollars sun yi kuka, sun ci uwarsu a wannan lokaci, ita kanta kujerar da His Excellence Saif William zai zauna kuɗinta ya fi kuɗin budget na state.

Dollars da aka kashe wajen shirya kujerun zaman bakin da zasu taya Lion murna ma kawai ta isa wata kasa ta inganta kanta, shegun tsadaddun kujeru aka zuba, bafa wani zama zasu yi su jima ba, amma a haka aka narka waÉ—an nan shegun dollars É—in kawai dan a kawata wajen, abin dai baki ya yi kaÉ—an ya faÉ—e shi.

Wani irin azababben fitinannen daddaɗar kamshin ne yake tashi a gabaɗaya ilahirin white house ɗin, ga wasu jiga jigan security's masu jini a jika dake aikin fesa perfume ta ko'ina. Dubbannin zaratan sojoji masu jini a jikka ne suka kewaye ko'ina a faɗin cikin white house ɗin, ta ko'ina idan ka juya kaki zaka gani rike da jiga jigan bindigu masu rai da lafiya, ƴan'sanda ta ko'ina suna shawagi, ga wasu haɗaɗɗun helicopters da suke shawagi a sararin samaniya dan kara tabbatar da tsaro, apart from helicopters da akwai wasu na'urori da suka tasa sama dan kawai su tattabar da tsaro, ga wasu kananan jirage masu amfani da computers, duk wasu Generals na sojoji sun hallara a wajen, a ɓangaren ƴan'sanda ma I.G da D.I.G na kasa bakiɗaya ma sun bayyana a wajen. Duk wasu Ministers sai da suka zo, ga manya manyan lauyoyi ma dukka a wajen.

Kowa daga cikinsu ya samu waje cikin tsadaddun luntsuma luntsuman sofas da aka jeresu a cikin fadar suka zauna, daga gefe guda kuma shuwagabannin kasashen da suka zo taya shi murna ne a wajen.

Dukkansu suna saman sofas Lion and Rimsha ne kawai suka hau saman stage É—in da aka kawata shi da ado mafi tsada a duniya, shi kansa speaker da Lion zai yi magana a wajen da diamond aka yi shi.

Meesharsa tana gefensa, ga wasu jiga jigan lauyoyi ta kotun duniya da suke tsaye a gefe da gefensa, sanye suke cikin kayan lauyoyi masu kyau da tsada, ga su jajir dasu kamar ka taɓa jini ya zuba. Ta ko'ina hasken Cameras wanda ƴan jaridu suke ɗaukarsu ne yake tashi, daga ɗan bayansu Lion ɗin kuwa lieutenant General na sojoji ne, sai Major General and Brigadier General, su ne suka tsaya a bayansa ta gefe guda rike da jiga jigan bindigu, ta gefe guda kuma I.G and D.I.G na kasa ne tsaye a wajen.

Wani hamshakin shararren lauya ne ya kawo wa Lion wata takarda wanda zai karanta a wajen domin ya sanar da al'umma irin alkawarin da ya yi masu da kuma aikin da zai yi masu, takardar tana kunshe da abubuwa sosai na bayani da zai yi. Sai dai kuma, ko da suka kawo mashi bai karɓa ba, ya ɗaga masu hannu a kan baya buƙata.

Rimsha ta ƙanƙame shi sosai saboda tsoron waɗan nan jiga jigan sojoji dake tsaye a bayansu, ga taron jama'a dukka idanu naa kansu, hakan yasa ta kasa sukuni, baiwar Allah bata saba ba, duk sai ta shiga damuwa ta ƙanƙame shi sosai, shi ma ɗin bai saki hannun nata ba duk da sun hau saman stage ɗin, yaki sakinta, dan yasanta da shegen tsoro. Har mamaki jama'a suke yi, waɗan da basu gani su kyale har sun fara tofa albarkacin bakinsu, sai maganarsa ake yi, na farko ga shi sun ra'ina matar tasa, ƴar ƙarama da ita, na biyu ga shi sai biye mata yake yi, ya wani ƙanƙameta kamar sun ce zasu kwace mashi ita, hakan yasa ƴan jaridu suka kara ɗaukarsu hotuna sosai da kyau da kyau dan su sami abin yaɗawa a tashoshinsu.

Live aka kunna a fadar, gabaɗaya faɗin ƙasar har ma da na ketare ana kallon me yake gudana, kowa ya sha ruwan mamakin kin karɓar takardar nan da Lion ya yi, hakan tasa kowa ya nutsu domin ya ji menene dalilinsa.
Chapter 148 · 0% Book details