← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 168

Sashe 32

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abu na farko, jaririn da ya ga mutun ya kawo, tabbas mai brown eyes ne, idan hasashensa gaskiya ce, to Aseef ne kenan, dan wanda yake kwance a saman sofa dai, mai blue eyes ne, hakan na nufin shi ne kenan, babban abin da ya fi ɗaga mashi hankali shi ne, ya fi kaunar Aseef ɗin sama da kansa, ya fi son Aseef fiye da Areef, ya fi son Aseef fiye da kowa, sun fi shakuwa, shakuwar da take a tsakaninsu baki ba zai iya faɗarta ba! Gara ace mashi mutuwa ya yi, da ace mashi Aseef ba jininsa bane! Ba zai iya jurar hakan ba, ko na rana ɗaya ba zai iya rabuwa da shi ba! Yana kaunar shagwaɓatinsa! Yana son ɗan rigimammensa! Yana son pleasurensa! Shi ne bugun zuciyarsu! Ko daddynsu ya fi kaunarsa sama da kowa! Ya ilahi ya lillahi, ina zai saka ransa ya ji sanyi! Josephine ta cuce shi! Ta gama da rayuwarsu, sai da suka saba! Suka taso a tare! Komai tare, shakuwa tasa har suke jin juna a jikinsu, yanzu ya Areef zai ji? Anya zai iya yarda kuwa? Babbar tambayar da Lion ɗin yake yi wa kansa shi ne, to meyasa suka yi hakan? Meyasa aka canza masu ɗayasu? Me suka yi da wancan ɗayan da suka ɗauka? Ina suka kai shi? Yana raye ne ko ya mutu? Shin Aseef mutun ne ko aljani? Cikakken mutun ne kuwa? Ko shi ne yasa yake wasu abubuwa da bana cikakkan mutane ba? Dole dai akwai dalilinsu na yin waɗan nan abubuwa dukkan, haka kawai baza'a canzasu ba! Haka kawai baza'a kawo wani yaro daban a cikinsu ba!!

Ni kuma PRINCESS TEEMA abin da yake cikin ra'ina, yake kuma damuna shi ne ya Akila zata yi? Ya zata ji a ranta? Shin zata zauna da wanda ba mutun bane? Ko dai yaya? Anya zata iya rayuwa babu shi kuwa? Tana son heartbeat nata fiye da kanta, wai Meyasa Aseef ya cika mugu mugun shiga ran mutane dayawa har haka ne? Meyasa kowa ya fi son shi? Wannan ma ayar tambaya ce!!.

Abu na biyu da ya sanya Lion ɗin zuciyarsa ta kusa bugawa shi ne, wannan mutumin da ya kawo wannan jariri ba kowa bane face uncle Herry, ba shakka uncle Herry ne, dan da kallo ɗaya Lion ɗin ya yi mashi, ya kalle shi da idanun basira, nan ya fahimci uncle Herry ne, duk da ya ɓoye komai na jikinsa, yana cikin shigar bakaken kaya, hakan bai hana kaifin ƙwaƙwalwa Lion ta gane cewa shi ɗin bane, saboda idanun uncle Herry, John, Jay, GTA, daddynsa, Aseef, Areef, ba za su taɓa canzawa ko su ɓoye mashi ya kasa gane su ba, ba zai taɓa kasa ganesu a ko wani irin yanayi ba, zaka gan shi wani lokaci kamar baya kallo abubuwa, amma yana sane da komai, tabbas uncle Herry ne ya kawo jaririn. Tambayar da Lion ɗin yake yi wa kansa, to ina uncle Herry ya baro daddynsu? Ina ya baro Dr? Bayan kuma a tare suka fita daga gidan a lokacin, ko dai ya yi wa Dr ma wani abin ne? Wai shin menene gaskiya? Me yake faruwa ne?!!!.

Waɗan nan sune abubuwan da suka hargitsa zuciyar Lion, ace kannen babansa dukka maciya amana, kuma su rasa amanar waye za su, sai na yayan nasu, kai duniya ina zaki damu, ɗan uwa ya ci amanar ɗan uwan sa, sun cutar da rayuwarsu, to wai me suka yi da jaririn da suka ɗauka? Kuma a ina suka samo jaririn da suka kawo ɗin? Ga dukkan alamu dai suma aiki suke yi a karkashin wata kungiya, ko kuma wani, dan ga dukkan alamu umarni suke karɓa, duba da yanda suka tsara abin, a lokacin shekarasun ya yi kankantar da za su iya tsara hakan, sun yi kananan wajen shirya wannan abin, dole akwai wanda ya fisu shekaru da yake shirya masu komai, wannan dalilin yasa Lion ɗin bai ji cewa yana bukatar ya zauna da su, dan su gaya mashi gaskiya ba, dan ya san irin wannan case ɗin, ko kashe su zai yi, wlh ba za su taɓa faɗar gaskiya ba, so is better for him ya nemo gaskiya da kansa, babbar magana, ta ina zaka fara kenan? Waye zaka fara tunkara?!!

Murya a dashe saboda kuka Aseef É—in ya ce "My Lion, please ka tashi ka ji?". Kara datse idanuwansa sosai Lion É—in ya yi, har cikin ransa yake jin muryar Aseef É—in, yanzu idan gaskiya ta gama bayyana, shi Aseef me makomansa? Kenan idan ba mutun bane tafiya zai yi ya barsu? Ko yaya ne? Ya ilahi ya lillahi.

Gwaggo ce ta matso tana faÉ—in "Saif ka tashi dan Allah".

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da waro idanuwansa a hankali, kai tsaye sai saman face nata kallonsa ya sauka. Shiru ya ɗan yi kafin ya kai hannu ya ɓalle karin ruwan da aka sanya mashi, ya cire, sannan ya yunkura ya mike zaune.

"Saif meyasa ka cire ruwan kuma?". Cewar gwaggo. Girgiza mata kai ya yi alamar baya da bukatar ruwan. Matsowa ta yi tare da dafa kafaÉ—arsa tana shafa kansa da hannu É—aya.

Ɗago idanu ya yi yana kallon TGA dake tsaye a gefe guda, tun da yake da Uncle T ɗin nasa, bai taɓa tsura mashi idanu yana kare mashi kallo irin na yau ba, zuciyarsa na gaya mashi cewa har da uncle T ɗin yanzu a tafiyar su Josephine ɗin, amma yaki yarda da hakan, saboda wasu dalilan guda biyu, na farko TGA yana sonsu so na tsakani da Allah, dan an taɓa yin yunkurin harbin Lion ɗin ma da bingida, GTA ya tare, ya shiga tsakaninsu bullet ɗin ta same shi, na biyu kuma, TGA yana ɗan ƙaramin yaro lokacin da abubuwan suka fara faruwa, sai dai abin da ya sanyawa Lion ɗin shakku a kan Tga ɗin shi ne, meyake kai shi wajen Josephine a yanzu? A gaban idanunsu zai nuna baya son Josephine, amma a bayan idanunsu zai saci kafa ya je wajenta, ga uncle Herry ma, a gaban idanunsu yana nunawa baya sonta, amma a bayansu kuma 5 and 6 suke da ita. Wannan abin akwai matukar ɗaure kai over.

Ganin ya mike zaune ne yasa uncle T É—in ya kariso wajen nasa da sauri, shi ma Mark karisowa wajen ya yi yana yi mashi sannu.

Zuro kyawawan fararen kafafunsa kasan gadon ya yi ba tare da ya ce masu komai ba. A hanzarce Mark ya bashi takalmar dake kafansa, dan ya sanya, saboda ya san halin Ogan nasa da bala'in kyankyani.

"Momma let's go". Shi ne kawai abin da ya iya furtawa, sannan ya mike tsaye. Daga Mark har TGA kallon gwaggo da ya kira da momman suka yi, mamaki Mark yake yi, tambayar kansa yake yi wacece gwaggo kuma? Shi dai ya shiga duhu.

Wani irin jiri yake gani da ya mike, har wani layi yake yi. Ganin hakan yasa da sauri Mark da Tga suka yi ƙoƙarin tallafa mashi. Hannu ya ɗaga masu alamar baya bukata, sannan ya juyo da kallonsa a kan Aseef dake ta binshi da kallo. Alama da hannu ya yi mashi a kan ya zo ya tallafa mashi su fita, Allah sarki sam baya son Aseef ɗin ya fahimci komai, ya zai ji a rayuwarsa? Ya zai yi da ransa idan ya san gaskiya?.

Mikewa ya yi, duk jikinsa a mace, ya nufo Lion É—in. ÆŠan rungumo shi Lion É—in ya yi yana shafa kansa gwanin ban tausayi, haka suka nufi waje. Da sauri gwaggon ta mike ta rufa masu baya, su Tga suka rufa mata baya. Shi dai Mark kansa ta shiga duhu....... NI KO NA CE MARK BA KAI KAÆŠAI BA, KOWA MA KANSA TA SHIGA DUHU, WAI KAI DAN MA BAKA SAN ABIN DA MUKA SANI BA, AI DA DUHUN DA ZAKA SHIGA MA BA ZAI FAÆŠU BA!!.

Suna fita sojojinsa suka rufa masu baya izuwa wajen motocinsu. Lion haka kawai yake jin babu daɗi zuciyarsa, tunanin Rimsha dake ta faman sheka barci a gida ne ya faɗo mashi a cikin ƙwaƙwalwarsa, nan take ya ji kirjinsa ta buga, tasbihi ya fara yi a cikin zuciyar nasa, dan ya samu salama, abubuwan sun yi mashi yawa, tunani yake yi bai kamata ya yi nisa da duk waɗan da suke da kusanci da shi ba, dan a wannan point da suke a yanzu, kamata ya yi ya haɗe familyn gwaggon gabaɗaya waje guda, domin kuwa, a yanzu koma suwaye suke bibiyar rayuwarsu, sun san ya san komai, ba shakka za'a cutar da su, kuma tabbas familyn gwaggon za'a cutar, dan familyn daddynsu kam suna da hannu dumu dumu a kan komai, so yana da kyau ya haɗa gabaɗaya ƴaƴa da jikokin Dr Salman waje guda, sannan a saka masu matakan tsaro, idan ba haka ba, za'ayi masu ɗauki ɗai'ɗai!!. Babbar magana.

Wayar Aseef ne ta fara kara dai'dai lokacin da suka shiga cikin motar. A hanzarce ya cirota daga aljihunsa, ya sha ruwan mamakin ganin uban miss call na Areef, dan lokacin da Areef É—in ya yi ta kiransa, sam bai ji ba, baya a cikin hayyacinsa.

My uncle, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen É—in wayar. A hanzarce ya É—auki kiran, a lokacin kuma har motocin nasu sun fara tafiya, sun fito daga asibitin, yana zaune kusa da Lion, shi da gwaggo sun saka Lion É—in a tsakiya a gidan baya na motar.

A hand-free ya sanya wayar, daga ɗayan ɓangaren daddyn Rimsha ya ce "Aseef kuna tare da Akila ne? Ta zo asibitin ne?". Jin tambayar daddyn Rimshar yasa Lion ya juyo da kallonsa a kan wayar.

"A'a uncle, ni tun da kuka tafi da ita jiya, ban sake ganinta ba, na kira numberta da safe ma a kashe". "E ba shakka wayarta a kashe, muma mun kira bata shiga, amma ina zuwa".

A hanzarce Aseef É—in ya ce "Uncle lafiya dai ko? Meyasameta? Bata gidan ne? Ina ta ce dama zata je?". Ya yi maganar a rikice.

"A'a babu abin da ya sameta Aseef, ka kwantar da hankali, ina zuwa zan sake kiranka". Bai jira masar da zai bashi ba, kawai ya katse kiran.

TOH FAH INA AKILA KUMA TA SHIGA⁉️
Chapter 32 · 0% Book details