← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 168

Sashe 114

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Jehan". Ya ambaci sunanta cikin sanyin murya. "Na'am my baby". Ta amsa mashi. Shiru ya ɗan yi yana jin sautin sunan my baby da ta faɗa, ko da sunan wasa bata taɓa kiransa da hakan ba, wani irin daɗi na musamman ya ji tana ratsa shi.

"Muje nayi wa matata wanka ko?". Ya kai karshen maganar yana shafa kanta izuwa tsakiyar bayanta. Kai kawai ta gyaÉ—a mashi kafin ta É—an raba jikinta da na shi, sai dai taki buÉ—e idanuwanta, dan tsoron ganinsa babu kaya take ji.

Wucewa ya yi ya je ya haÉ—a masu ruwan wanka, tana tsaye idanu a rufe har ya dawo wajen nata, cancak ya É—auketa sai cikin jacuzzin. Wash ta É—an furta saboda yadda ruwan yake da zafi sosai, su kuma TRIPLETS sun saba yin wanka da ruwa mai zafi sosai, saboda sanyin kasarsu, so abin sai ya zamar masu jiki.

A takaice a cikin ruwan ma bai kyaleta ba, sai da ya yi ta wasa da ita son ransa, sannan ya yi mata wanka, ya yi ya yi a kan ta yi mashi wankar shi ma, amma taki yarda ta yi mashi, haka ya hakura ya yi wa kansa, ya naÉ—ota a towel suka koma cikin É—akin, a saman bakin bed ya sauketa tare da wucewa ya kunna wutar É—akin, sannan ne ya wuce izuwa dressing room nasa.

Kayan barcinsa masu kyau da tsada ya sanya a jikinsa, sannan ya É—auko mata kala É—aya, da kansa ya sanya mata, bata hana shi ba.

Bayan sun kammala ta sauko kasa ta fara zuba mashi abinci, kusa da ita ya zo ya zauna, sai kallon face nata yake yi cike da so da tsananin kaunarta tamkar wani ya ce zai kwace mashi ita.

"Baby gobe zaki rakani wani waje fa". Ya faÉ—a yana tara mata gashin kanta dake zubo mata a wuyarta idan ta sunkuyar da kai kasa tana zuba abincin, kayan barcin nasa babu hula, hakan yasa kanta yake a buÉ—e, ga gashin da danshin ruwa a jikinsa, basu busar da kan nasu ba, saboda Areef É—in yana jin yunwa sosai, sai ta ce ya fara cin abinci kafin su kammala komai daga baya.

"Okey tom". Ta faÉ—a tana dago da kallonta a kansa. A duk lokacin da ta sauke idanuwanta a kansa, sai ta ji tamkar ta shige cikin jikinsa su cure su zamo abu guda kawai, saboda tsananin son da take yi mashi.

"You are so very very beautiful my baby". Ya faÉ—a yana kai hannunsa ya É—an shafi gefen face nata. Wani irin kallon ta wurga mashi da waÉ—an nan dara daran idanuwan nata masu rikita shi. "Ban kai ka kyau ba ai my baby, yanzu dai ka ci abinci". Ta kai karshen maganar tare da É—ebo abincin a spoon ta kawo mashi saitin É—an bakinsa.

(Idan ba wani abin Jehan ta shirya ba yaushe zata tsaya zuba waɗan nan kalamai fisabilillahi 🤌😂 kun ji fa har da nuna damuwa da ya ci abinci yana jin yunwa 😂 har da bashi a baki yau🤌 innallilahi Jehan wan kill me with laugh 🤌😂 harda kiransa da baby, dan ma Allah yasa shi ma Areef ɗin ba tayan baya bane, da ai ba mai kwatarsa a hannun wannan yarinya ta maman Yasmin 😂)

A hankali ya buɗe ɗan bakin ta zuba mashi, lumshe idanuwansa ya yi yana mai matuƙar jin wani irin daɗi yana ratsa shi

kai, kai, kai nima haka nake jin daɗi idan ina shan Maltina mai sanyi 🧐 haba mana, ni masoyan nan sun fara isata🥲 dan haka zan dakata a nan sai gobe kawai in Allah ya kai mu, ina dalili? Kowa sai love yake sha sun barni da kayan takaici🤌😂 na fara kishi🥱😂

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

Date: 21/5/2024

E36

A hankali ya buɗe ɗan bakin ta zuba mashi, lumshe idanuwansa ya yi yana mai matuƙar jin wani irin daɗi yana ratsa shi.

"Did you eat yours?". Ya faÉ—a yana kallon cikin kwayar idanuwanta, ita ma kallonsa take a cikin idanu. Gera É—aya ta É—aga mashi tare da kashe mashi ido É—aya kafin ta ce "Yeah, amma kuma idan zaka bani abaki zan kara ci". Ta kai karshen maganar tare da sake É—ebo mashi wani abincin ta kai mashi saitin É—an bakinsa.

Karɓa ya yi yana faɗin "Dole zan baki a baki mana, because gobe da sassafe zamu fita da ke, ba zamu yi breakfast a gida ba, yanzu zan kara baki ki ci sosai, dan ba ma lallai mu yi breakfast on time ba". Ya kai karshen maganar yana kai ɗan yatsarta ya shafi lallausar lips nata.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce "Wai Yah Areef ina zamu je ne?". Tana magana tana kara É—ebo mashi abincin.

"Gidar Hjyr daÉ—i". Ya bata amsa cikin halin ko in kula, sannan ya yi maganar like bai ma san me ya faÉ—a ba.

Zaro dara daran idanuwanta waje ta yi, sam bata san lokacin da a dubu É—ari ta ajiye spoon na hannunta tana kallonsa ba, a lokacin shi kuma ya mayar da kallonsa a saman abincin, ganin ta ajiye spoon É—in ne yasa ya É—ago da idanuwansa a kanta.

"Lafiya?". Ya tambayeta yana tsareta da idanu.

"Who told you the story about Hjyr daÉ—i? Ya aka yi ka sani? And them yaushe kasan da hakan?". Ta yi maganar ba tare da ta kyafta idanuwanta ko sau É—aya daga kallon da take yi mashi ba.

"Maso tsuntsu ai shi yake binsa da jifa, do you think that soyayyar da nake yi maki is a joke? Do you think that kawai kalmar i love you É—in ce take yi mani daÉ—i nake furta maki ita?".

Girgiza mashi kai ta yi ta kasa yin magana, fuskarta ɗauke da mamaki ƙarara. Ganin haka yasa ya ture abincin gefe guda tare da jawota jikinsa, calmly ya fara magana. "You are so very very special my baby, ke ɗin mai zuciyar zinari ce, ban taɓa ganin mace mai jarumta irin taki ba, a dai waɗan nan kananan shekarun naki, abin ya yi matuƙar bani mamaki, tun time da kika rabu da su uncle har izuwa time da muka haɗu dake kullum cikin jefa rayuwarki a cikin haɗari kike yi, duk dan ki taimaki wasu, tun time da Rimsha ta yi magana a kan Daular Mutuwa, sai naga yakamata nima na yi binciken a ina matata ta yi rayuwa bayan rabuwarta da su Rimshar, nasan dole yadda Rimshar ta yi rayuwa a wani waje har da Daular Mutuwa, kema ɗin hakance, dama kuma already na fara bincike a kan dalilin da yasa kika kashe Abubakar Salahuddeen da kuma in da kika kashe shi, sai zancen Rimsha na Daular Mutuwa ya zo ya dakatar da ni, da na dawo muka koma U.s sai na faro bincike daga farko tun ranar da kuka je Katsina, tun farkon rikicinki da Farooq Salahuddeen wanda kuma dama shi ne Lion ya kawo shi gidan nan a matsayin yayansa, hakan tasa nasa aka kashe shi, amma fa my baby kin iya dirama, waye ya baki idean da kika shirya wa baban Sadiq wancan muguntar?".

Shiru ta lafe a jikinsa tana ruwan hawaye tana sauraronsa, bata taɓa tunanin yana bincike a kan rayuwarta ta baya ba, ya tuna mata da abubuwa dayawa a yanzu, ya tuno mata da su Sadiq, da irin tsiyar da ta sanya suka yi wa babansu shi da amarya, ga kuma rayuwar da ta yi a gidan na Hjyr daɗin, komai ya dawo mata sabo.

Jin ta yi mashi shiru ne yasa ya ɗago haɓarta. "Sure my baby, for sure dole ki yi kuka, amma idan bananan ne zaki yi kukar, ina nan babu kukan da zaki yi, you are the best, kin shiga haɗari sosai saboda ki taimaki wasu, i really love, baki barin rashin adalci a wajen da kike zaune, ya isa kukan haka, su friends naki da suke a gidan Hjyr daɗin duk gobe zamu je mu ɗauko su kin ji ko?". Ya kai karshen maganar yana matso da face nasa izuwa saman tata.

A hankali ya fito da tongue nasa ya fara aikin lasar hawayen nata. Rungumarsa sosai ta yi a jikinta tare da cusa kanta a cikin kirjinsa tana sakar mashi kuka mai sauti.

Sosai ya rikota tare da fara rarrashinta, da iya gaskiyarta yau take kuka, babu makirci ko kuma tsiya, iya gaskiya yau take yin kukan, wani irin azababben sonsa ne ya ninkun mata a cikin zuciyarta.

Rarrashinta ya rinƙa yi har sai da ya samu ta yi shiru, sannan ne ya jawo plate na abincin suka cigaba da ci a tare. Sai da suka ƙoshi tab, sannan ta tattare komai ta fitar waje, da kallon so da kauna ya bita har ta fita ta dawo.
Chapter 114 · 0% Book details