← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 168

Sashe 134

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu ya kai dai'dai saitin marfin drawer, yana kai hannu ta buɗe kanta da kanta. Ya ilahi, kayane dankare makare a ciki, kaya ne da suka wuce baki ya misilta maku su, da yake drawer tana da girman cin bango guda, sai ya zamana komai da nasa part ɗin, to wannan part ɗin da Lion ya buɗe shake tab yake da always da kuma pants, ma'ana dai kayan ciki na period na mata ne, tun ranar da Rimsha ta fara period time da suke tafiya ƙasar Russia, tun a ranar ya rike date ɗin, kasancewar zasu dawo U.s kuma ya ga date ɗin period ɗin nata ya kusa ne yasa a kayan da ya yi mata oder har da always mai uban yawa kamar wadda zai buɗe shagon sayar da su, su kaɗai sunci side ɗaya na drawer, dan ma dai dama ba kayan fita waje ya saya mata ba, iya su kayan barci ne da nasu shan iska, sai su pant and bra, sune ya saya mata, Josephine yasa ta saya mashi kamar yadda ta saya mashi wancan time ɗin, to wannan time ɗin ma ita ya aika ta sayo mashi, sai dai bai je gidan nata da kansa ba, sako ya tura mata a wayarta, daga karshe ya sanar da ita su gwaggo zasu zo, so zai turo azo a ɗaukota, da okey ta bishi, sannan ta je ta saya mashi duk abin da ya dace mata masu bala'in kyau da tsananin tsada, ya tura aka ɗauko mashi zuwa gidan nasa.

Katon ledar always guda É—aya ya ciro, sannan ya É—auko kwalin kyakkyawan pant kwali É—aya. A saman mirrorsa da yake a cikin dressing room É—in ya É—aura always da pant É—in, sannan ya yage ladar ya ciro always É—aya ya ajiye a gefe, sai ya buÉ—e kwalin pant É—in shi ma, irin wanda yake zuwa guda uku a kwali É—ayar nan ne. ÆŠaya ya ciro mata tare da mayar da sauran ya mai da su cikin drawer, ya zo ya É—auki waÉ—an da ya fitar É—in ya fito daga room É—in izuwa cikin bedroom nasa.

Har lokacin tana kwance idanu a lumshe, tana jin azaban ciwon mara, dama idan baku manta ba nata period É—in da azababben ciwon ciki yake zuwa mata.

Kusa da ita ya zauna tare da ɗan kai hannu ya yi kasa da bargon da take lulluɓe da shi ɗin. Saman kanta ya ɗaura hannunsa tare da shafawa a hankali yana ambatar sunanta.

Tamkar jira take yi ayi mata magana, sai kawai ta sa mashi kuka, ta kuma kasa iya buÉ—e idanuwanta.

Ajiye always and pant É—in ya yi a gefe guda, hannayensa dukka biyu ya kai ya É—agota, a saman Lion chest nasa ya mannata yana shafa bayanta a hankali.

Ƙanƙameshi ta yi, cikin azaban ciwon take faɗin "Noorish cikina ne yake yi mani ciwo". Tana magana wasu zafafan hawayen suna bin kuncinta da gudu kamar ruwan famfo.

ÆŠan raba jikinsu ya yi tare da sanya hannunsa a saman shafaffen cikin nata. "Sorry my Meesha, yanzu zai dai'na yi maki ciwon In Sha Allah, nan da Æ´an mintuna kaÉ—an dai period É—in naki zai zo ki huta, yanzu daure ki tashi ki shirya mashi kin ji?".

Kara ƙanƙanme shi ta yi tana kara sautin kukan nata. Rarrashinta ya rinƙa yi tare da lallaɓata har ta hakura ta mike ta shirya kamar yadda ya buƙata, sai da ta miƙe ɗin ne kuma da ta buɗe idanuwa ta kalli irin kyan da ya yi, ya yi shirin fita, sai me? Ai tuni kishinta ya motsa, ji ta yi Allah ba zata iya barinsa ya fita da irin wannan azababben kyan nasa ba, saboda tasan dole sai ya gwara kan ƴan mata, dole za'a tsare mata shi da kallo, zai haɗa accident ba kaɗan ba. Dan haka sai ta sake narkewa a jikin nasa tana mai sake saka mashi kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Nan take ya hau rarrashinta tare da tambayarta meyafaru kuma take sake yin kuka?.

Kin bashi amsa ta yi, sai ma kara shigewa jikinsa da ta yi tana mai kara marairaice murya ta yadda kukan nata ma zai taɓa mashi zuciya sosai da sosai.

Aikuwa dai ta yi sa'a, dan kuwa wannan kuka ba ƙaramin ɗaga mashi hankali ya yi ba, dik sai ya rasa me yake yi mashi daɗi, ga shi taki yi mashi magana bare ya ji menene yanzu kuma yake damunta.

Rarrashinta ya rinƙa yi, dan ba zai iya jurar kukar ba, da kyar ya samu ta buɗe baki cikin kuka ta ce "Ni Noorish bana so ne ka fita, ka zauna da ni tun da bani da lafiya".

Shiru ya É—an yi yana tunanin meeting É—in da zai je É—in, tana da mahimmanci, amma kuma hannun Meesharsa guda É—aya kawai ta fi mashi komai nasu mahimmanci bare ita da kanta.

Ganin ya yi shiru ne yasa ta sake cigaba da yin kukanta, shi da yake bai gane tana kishi dan ya yi kyau over bane, saboda shi bai san kalar kishin matan Nigeria ba, na turawan ma bai sani ba bare bakaken fata, kun san shi ba alaƙa da nata take yi ba bare ya sani, sai kawai ya kara rumgumeta a jikinsa yana faɗin. "Do you agree na yi attending meeting ɗin through online?".

Tsit ta natsu a jikinsa jin abin da ya ce, kasa kasa ta ce "Amma a wajen meeting É—in babu mata?".

Sai yanzu ya gane dalilin hana shi fita da take son yi, sosai ya ji daɗin hakan, dan su maza a duniya suna bala'in son suga an damu da su har ana nuna kishi a kansu, ko basu fito sun nuna jin daɗinsu a fili ba, amma ba makawa suna jin daɗi over, idan ma baki nuna kishi a kansu wasu har kasa hakura suke yi sai sun tambayeki kekam baki da zuciya ne? Dan kawai baki nuna kishi a kansu ne zasu ce maki baki da zuciya, so wannan ɗabi'a ce ta maza, koda mata biyu suke da su a gida, zasu so ayi zaman lafiya a tsakanin matan, amma kuma suna bala'in son suga ko wacce tana nuna masu tana kishi sosai a kansu, a jininsu yake, dan haka idan ma baki nuna mashi kina kishinsa, tun wuri gara ki fara, zaki ga har wani murmushi yake yi idan kika fito da kishin naki fili ya gani, dan yaji daɗin andamu da shi, maza mutanenmu mu kuma sai Allah.........🤌😂

"Meesha sarkin rigima, to idan ma akwai mata a wajen ni ina ruwana da su?". Ya yi maganar yana kallon face nata, kun san idan mace tana period tana kara wani sihirtatcen kyau, jikinta har wani glowing zai rinƙa yi, to haƙiƙa ta tafi da imaninsa sosai ta yadda ya kafeta da idanu babu ko kyaftawa.

Turo baki ta yi kamar zata sa kuka. "Noorish ni gaskiya in dai da akwai mata a wajen bazaka je ba, ko ta online ɗin nema bana so". A shagwaɓe sosai ta yi maganar.

Matso da É—an bakinsa saitin kunnenta ya yi, kasa kasa ya raÉ—a mata."To ai ke kaÉ—ai kin ishe ni, ni bana ma haÉ—a hanya da mace, because dukka ina É—aukarsu a abu guda, keda momma ce kawai kuke daban".

"Ni gaskiya duk da haka dai mu zauna tare a nan, ai idan kai baka kulasu su zasu kula mani kai, kaga kyau ɗin da kayi kuwa? Shi ne kuma zaka fita? Tab kana son ka saka mata su yi ta suma a kan hanya ko? Wata ma mayya mai kafar shamuwa nasan sai ta yi maka magana koda ba zaka kulata ba". Ta kai karshen maganar tare da sanya mashi wani irin kuka mai kama da na shagwaɓa, sai dai kuma na soyayya ce.

Shiru ya zuba mata idanu har ta gama zuba surutun nata tana aikin turo baki. Shi dai Lion kamar kullum, har yau murmushi sam bata ga gurbin zama a face nasa ba, Rimsha ta yi juyin duniyar nan dukka a kan ya yi mata murmushi ko da sau ɗaya ne a rayuwarsa, amma ya ce sam shi bai iya ba, bai san ya ake yi ba, kullum fuska a ɗaure tamau, bata da zaɓin da ta wuce dole ta hakura ta rabu da shi, dan a yanzu ta fahimci rashin murmushin nan haka yake, ba zai taɓa yi ba, gara kawai ta kyale shi har Allah ya kaita ranar da zata ga murmushinsa koda sau ɗaya ne a rayuwarta.

"See your beautiful mouth like mace zata yi mani magana, aww ke yanzu Meesha kina tunanin yadda nake dake a nan haka nake magana da kowa a waje ne?".

GyaÉ—a mashi kai ta yi alamar e.

Nisawa ya yi kafin ya É—aura da cewa "Ai in dai ni ne yanzu ki fita ki zuba makudan kuÉ—aÉ—e ki ce namiji ma ya tinkare ni ya yi mani magana zaki bashi kuÉ—in, zaki ga ikon Allah, babu wanda zai kulaki ko me zaki basu, namiji ma bare kuma mace, ni ai kowa tsorona yake ji a kasar nan, i don't know the reason why, but wani lokaci zaki gani idan muka fita, yanzu haka idan kika tara mutane É—ari ba lallai biyar daga cikinsu sun san kalar voice nawa ba, yanzu dai jeki shirya kizo mu yi attending meeting É—in a tare da ke, ba shikenan ba?".

Kai ta gyaÉ—a mashi tare da shigewa jikinsa tana murmushi, ita a dole ta ji kunya, ga wani guntun hawaye na iyashege a face nata.

Miƙewa da ita ya yi zuwa toilet, a tsakiyar toilet ɗin ya sauketa, sannan ya juya izuwa waje yana mai gaya mata idan ta gama wanka da akwai kayanta a drawer a cikin dressing room nasa, ta shirya sai ta zo ta same shi a ɗakin computers nasu, ya gama mata kwatance ya fito abinsa.
Chapter 134 · 0% Book details