Sashe 3
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zazzaƙar murnarsa ne ya dawo da ita cikin hayyacinta a in da ya furta mata "Ke dabbar ina ce?! Babu kwakwalwa a cikin kanki ne?!". Ya yi maganar cikin natsuwa. Jin hakan yasa ta dawo dai'dai. Ɗago dara daran idanunta da suka yi ja sosai saboda marin da ta sha ta yi, tare da sauke kallonta a kan fusatatcen fuskansa. Duk da ta sha jinin jikinta na ganin face ɗin nasa a ɗaure, ga uban kwarjini mai rikitarwa, ta kuma tsorata, amma hakan bai hanata ta datse idanunta ita ma ta ɗauke shi da wani gigitatcen mari ba.
Cherish da ba ita Gwaggo ta mara ba, sai da ta saki plate na kayan cima dake hannunta suka zube kasa suka tarwatse a wajen, saboda tsabar mahaukacin razana da ta yi, bata taɓa tunanin za'a iya samun wanda zata iya marin dangerous boss a cikin wannan school ɗin ba, zaratan maza ma tsoronsa suke yi bare mata. Da gudu ta watsa ta bar wajen dan ta je ta sanar da Abbi abin da yake faruwa da Gwaggon.
Jama'ar dake wajen ba ƙaramin razana suka yi ba, dan dayawansu sun san waye shi, bashi da mutunci, kuma iyayensa suke goya mishi baya, a kansa zasu iya buga shari'a da kowa, ɗan gidan manyan mutane ne masu karfin murya ta faɗa a ji a kasar, yayan mahaifinsa ma shi ne president mai ci a wannan lokaci, shiyasa yake yin abin da ya ga dama.
Ba'a taɓa yin wanda ya nuna mishi koda yatsa a cikin school ɗin ba, yau an wayi gari wata mace ta wanke mishi kyakkyawar jajir ɗin lallausan fuskarsa da mari a gaban jama'a. Tashin hankali, ko iyayen da suka haife shi basu taɓa dukan shi ba, sai dai su yi ta lallaɓa shi tamkar jariri, ɗan gata ne over.
Ita kuwa Gwaggon hankalinta a kwance dan bata ma san wanene shi ɗin ba, sai ma ƙoƙarin sake raɓawa gefensa da ta yi dan ta wuce. Cikin fushi da ɓacin rai ya sanya kafa ya kwashe kafafunta ta zube kasa wanwar.
Tsadadden belt É—in wandonsa ya ciro da nufin ya yi mata dukan mutuwa, hakan kuma ya yi dai'dai da shigowar Abbi da Cherish. Daga can baya Cherish ta tsaya. Shi kuma Abbi, da sauri ya kari so wajen tare da rike belt É—in na Dr William É—in yana tambayar shi me yake faruwa.
Kwashe Abbin ma da wani gigitatcen mari ya yi, dan fa ya fusata a lokacin, ransa ya yi mugun ɓaci, baya ji baya gani. Sauke musu belt ɗin hannun nasa kawai ya fara yi a jiki. Da sauri sauran jama'ar da suke wajen suka yi kansu, duk da suna tsoronsa bai hana su bashi hakuri ba, saboda mace yake duka. Ainahin Dr William baya dukan mata, kowa ya san da hakan, ɗabiarsa ce, kuma shi ya koyawa su Lion dukan mace kaskanci ne, amma ita ta raina mishi wayo ne, kuma ya tsani raini a rayuwarsa, zata zuba mishi abu a jiki ba tare da ta wani damu ba zata wani ce mishi sorry cikin nuna halin ko in kula, dole abin zai ɓata mishi rai. Uwa uba ga kuma marin da ta yi mishi a bainan nasi
Da kyar aka danne shi ya hakura ya rabu da ita, badan haka ba ya yi niyar yi mata ɗan banzan dukan da ko motsawa ba zata yi daga wajen ba sai an ɗagata. Cikin fushi ya yi wurgi da belt ɗin tare da wucewa ya bar wajen yana wani huci. Bayan ya tafi ne jama'a suka taimaka mata ta miƙe, jiki ba kwari suka fito daga cikin wajen. A cikin zuciyarta, ta kuduri niyar wlh bazata barshi ba, sai ta koya mishi hankali!!.
Abbi ya shiga damuwa sosai, amma ita ko a jikinta, bata wani damu ba, yanayin rayuwarta a lokacin sak rayuwar Jehan, ba maraba, dan bata shiga harkar kowa ita ma, amma idan ka shiga nata, to fa wannan faÉ—a ba zata kare ba har sai ta ga ta yi nasara a kan abu, haka take.
Sati biyu Abbi ya yi a wajenta, tun daga wannan rana kuma bata sake yin 4 eyes da Dr William ba, har sai ranar da Abbi ya koma, bayan ta raka Abbin airport ta dawo ne ta wuce shopping dan ta sayo wasu abubuwan bukata da bata da shi a gida.
Shiryawa ta yi cikin wandon jeans fari tare da high neck t-shirt, shi ma fari tas, ta gyara gashin kanta tare da ɗaura wani ɗan ƙaramin handkerchief a kan nata, shi ma fari, kafarta na sanye cikin high heel fari, from up to down dukka wankar fari ta yi. Wayarta da Atm kawai ta ɗauka sai key ɗin mota ta fito. Da yake gidan nata yana hawa na goma ne ta lifter ta sauko kasa, kowa na benensu yana harkar gabansa, babu ruwan kowa da kowa. Wucewa ta yi zuwa wajen kyakkyawar motarta, shiga ta yi ta bar gidan.
Bata zame ko'ina ba sai wani tampatsetsen super market. Tana parking bata ɓata lokacin ta ba wajen fitowa daga motar ta nufi cikin wajen. Sayyayya ta fara yi babu kama hannun yaro, tamkar ba kuɗi zata biya ba, da yake already Dr Salman ya zube mata kuɗi a cikin account nata ba na wasa ba.
Tana sayayya tana kewaye wajen. Kamar daga sama tana yin kwana ta wajen Lotions ta yi karo da mutun. Dankareren wayar dake hannunsa ne ya faÉ—i kasa. Ba tare da ta É—ago ta kalli wanene bane ta duka ta É—auko mishi wayar. ÆŠagowa da zata yi da nufin ta mika mashi suka yi 4 eyes da shi. Yauma dai kamar ranar, yana sanye da bakar glass a idanunsa, haka zalika wankar fararen kaya ne a jikinsa, sai suka yi iri É—aya da ita.
Ganin shi ne yasa ta ɗaure fuska sosai tamkar hadari, rai a matuƙar ɓace ta saki wayar tasa ta sake faɗuwa kasa. Kallon up and down ta yi mashi kafin ta ja keken sayayyarta ta raɓa gefensa ta wuce abinta. Shiru ya tsaya, ya kasa dakatar da ita, ya kuma kasa duƙawa ya ɗauki wayarsa, tunani yake yi a kan abin da ya kamata ya yi wa wannan yarinyar, dan ta yi mashi abin da ko iyayen da suka haife shi basu taɓa yi mashi ba, babu wanda ya taɓa marin shi sai ita, sam bai kamata ya kyaleta ba, kamata ya yi ya mata hukuncin da sai ta gwammaci mutuwa a kan shi!!.
Ya jima tsaye a wajen yana tunani kafin ya sa kai ya wuce. Isa da takama haÉ—e da jin cewa cikin narkakkun dukiya yake kwana ga uban girman kai ta hana shi ya tsugunna ya É—auki wayar tasa. Ficewa ya yi daga wajen zuwa wajen motarsa. Wasu jibga jibga bodyguards guda biyu masu sanye da black suit ne tsaye a bakin motar tasa, komai da suka sanya a jikinsu black color ne. Yana zuwa ya yi musu umarni a kan su tafi, sai wani huci yake yi, zuciyarsa na saka mishi abubuwa da dama da zai yi wa gwaggo dan ya É—auki mataki.
Ita kuwa sayayyarta ta yi sosai, sannan ta wuce wajen biyan kuÉ—i, sam bata sake bi ta kansa ba, tama mance da cewa sun haÉ—u a nan. Bayan an gama yi mata lissafi ta basu Atm card dan su ciri kuÉ—in nasu. Bayan an gama komai ma'aikatan wajen suka kwasa mata kayan zuwa wajen motarta, da haka ta wuce izuwa gida.
Da daddare Cherish ta zo suka sha hira tare da ciye ciyensu. A gidan Cherish ta kwana, sai takurawa Gwaggon take yi da maganar Abbi, ita kuwa gwaggo da ta gaji, sai ta bata number Abbin na Nigeria, dan ta daina damunta!.
Washegari haka suka shirya zuwa school, a tare suka wuce a motar gwaggo, Cherish ta bar motarta a gidan na gwaggo. Kamar dai kullum bayan sun fito daga lecture, kayan cima suka je suka sayo, a in da suka dawo garden suka zauna. Suna hira suna ci har suka kammala, sannan suka miƙe dan su koma gida.
Rayuwarta ita da Cherish gwanin birgewa, kullum idan sun zauna sai ta yi ta bawa Cherish É—in labarin Æ´an uwanta tare kuma da nuna mata hotunansu. Ita ma Cherish É—in tana yawan bata labarin Æ´an uwanta da hotunansu. Ainahin Cherish Æ´ar kasar China ce, karatu ita ma ya kawota nan, tana da kirki fiye da tunanin mai tunani, gata da son barkonci da dariya, tana da É—an shekaru, dan ta girmi Gwaggon ma a shekarun.
Washegari suka je school a lokacin zasu fara rubuta exams, sun sha karatu sosai, dan sam basu wasa, yau kowa ka gani a department nasu, zaka ganshi yana rike da handouts sosai, dan kowa dai yasan yanda karatun likita yake, ba karatu ne na wasa ba, sai masu ƙwaƙwalwa da basira sosai.
Suna tafiya suna hira, haka suka nufi cikin department ɗin nasu. Kasancewar gwaggo girman Russia ce ita, duk cikin turawan ta taso, sai ya zamana dressing nata sak nasu, tamkar ba musulma ba, a lokacin kuma da gaske bata zauna a Nigeria ba, sun dawo bai fi ta two months ba ta wuto Washington DC, so babu wani al'ada da yake tattare da ita face na turawar Russia, haka zata saki gashi ba ɗankwali abinta, duk da cewa Naurat tana iyaka bakin kokarinta wajen ganin ta basu tarbiya duk da ita ma tubabbiya ce, amma tana ƙoƙarin sosai, kuma ita kanta Brr Naurat ɗin a lokacin dressing na turawar take yi, so ba zaku ga laifin gwaggo a wannan lokaci ba!.
Sun zo zasu shiga class nasu, shi kuma Dr William yana fitowa, hannunsa na rike da wata shegiyar tsadaddiyar laptop da kuma takardu, sai sauri yake yi, hakan ce ma tasa bai mayar da laptop É—in cikin jakarsa ba, da alama wani wajen mai mahimmanci zai je. Karo suka yi da gwaggo a in da gabaÉ—aya abubuwan dake hannunsa harta wayarsa suka zube kasa. Hakan tasa hankalin jama'a ya yo kansu.