Sashe 100
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar Areef zai yi mashi magana, sai kuma ya fasa, saboda ya lura ran Lion ɗin ya ɓaci sosai, idan ya kuskura ya yi mashi wata magana a yanzu, to suna iya dakuwa da juna, mafi a'ala kawai ya kyale shi sai ya yi barci ya farka, idan zuciyar ta sauka, sai ya gaya mashi ita fa Rimsha yarinya ce, kuma son shi da take yi ne yasa har ta damu da tana son ganinsa, idan bata son shi ba zata ko kula shi ba, a cikinsu dukka TRIPLETS ɗin waye ta kira ta ce sai dai ya dawo idan ba shi ɗin ba? Ai ko iya haka ya kamata ya san cewa ba wai dan rashin kunya ko raini yasa ta faɗa mashi magana haka ba, so ne ya jawo hakan, kuma su mata fa sai ya yi hakuri da su, dan annabi ya ce a karkace suke, ba zasu taɓa miƙewa ba, so dole ka bisu a yadda suke idan kana son zama da lafiyarka ba sai ka rinƙa ziyartar asibiti ba, bugu da kari kada ya manta da abin da ya yi mata kwanaki ashirin da tara da suka wuce, dan ma Allah ya taimake shi bata san me ya faru ba, ai ta cancanci ya ɗaga jirgi ne ma musamman ya je ya dubata ya dawo, ba wai ya kara ɓata mata rai ba, amma dukkansu zuciya da kuma shaiɗan sun ɗebesu, sun zuciya a banza, wanda hakan kuma sam ba shi ne solution a garesu ba, dan ba hanya mai ɓullewa suka bi ba, hanyar da zata jefasu cikin ukuba suka sake afkawa, zasu yi bayani ne dukkansu biyu! Dan dukkansu suna matuƙar kaunar juna na wuce misali!.
Miƙewa Areef ɗin ya yi ya diro kasa daga saman gadon, bedroom nasa ya nufa yana mai addu'ar Allah ya shirya mashi Lion ɗin nan, mutun sai bala'in zuciya, yana da tabbacin da'a gabansa Rimsha ta yi wannan magana, da ba abin da zai hana bai yi mata dukar mutuwa ba, dan duk cikinsu ma Lion ɗin ya fi tsanar kalmar raini, da sai ya yi mata ɗan banza duka, sai dai daga baya ya yi danasani, amma zata daku kam.
Lion a haka ya runtse idanuwansa yana mai jin zuciyarsa tana yi mashi zogi har barci ɓarawo ya yi awon gaba da shi. Shi ma Areef ɗin bedroom nasa ya koma ya kwanta, dama shi Aseef already yana can bedroom nasa suna aikin da suka saba shi da Heartbeat a waya. Asuba ta gari.
KASAR CHINA.
Babban birnin Beijing, Capital Cityn kasar China kenan, birni ne mai matuƙar girma tare da cike da abubuwan more rayuwa da kawa, yana da matuƙar ɗaukar hankali, akwai guraren yawon buɗe idanu kala kala, kun san China da uban technology, akwaisu da iya ƙere ƙeren abubuwa, ga wajajen hutawa na more rayuwa, ko'ina a cikin birnin tsab yake babu datti, al'adunsu dayawa daga ciki gwanin birgewa, ga su da karrama bako, suna da son mutane, tsayawa zayyana maku yaɗuwar birnin Beijing ma ɓata lokaci ne, dan baki ya yi kaɗan wajen zayyano shi, dan fa kowa yasan China karshe ce, sun haɗu iya haɗawa, dan haka mu shige kai tsaye cikin storyn dan jin yadda zata kaya.
Ministry of defence, wato Ma'aikatar tsaro ta kasa bakiÉ—aya.
Wani tampatsetsen office ne a cikin Ministry of defence ɗin, a dukka ofisoshin dake a wajen wannan ya fisu girma da kawatuwa, ya tsaru iya tsaruwa na wuce misali, kai daga gani ko ba'a faɗa maka ba kasan cewa office ɗin Defence minister ne, wato Ministan tsaro, yanayin tsarin office ɗin nasa ma na daban ne, ya tsaru iya tsaruwa, gabaɗaya fentin office ɗin fari kal ne mai matuƙar kyau da tsada.
Daga cikin parlour na office É—in, wato wajen meeting nasu kenan, wasu lumtsuma luntsumar tsadaddun Chinese sofas ne masu numfashi jere a wajen, set biyu ne dai'dai sofas É—in, sun tsaru iya tsaruwa, gasu da laushi tamkar audiga, kana zama zasu lume da kai, launin ash color ne, lallausa kuma tsadadden Chinese carpet dake shumfuÉ—e a tsakiyarsu ma launin ash É—in ne, daddaÉ—ar kamshi tare da sanyin A.c mai ratsa zuciya tare da kwantar da hankali sai tashi yake yi a cikin parlour, kai kace parlourn wani hamshakin sarki mai ji da karfin mulki ne, amma kuma office na mutun É—aya ne, common dustbin dake a cikin parlourn office É—in nan abin kallo ne, dan ba kuÉ—in wasa aka zuba mashi wajen sayansa ba, na manyan kai ne, ko'ina tsab kamar yanzu aka zuba sabbin kayan cikin.
Akwai wani kyakkyawan table mai É—auke da table chair da yake a gefe guda, wata farar tattabara ce, wato wata farar budurwa kyakkyawar gaske ce zaune a saman chair É—in, da alama Secretariya ce, Æ´ar Chinance, tana cikin shiga irin na ma'aikata, mining sket black color and long sleeve fara, ta É—aure gashin kanta a tsakiyar kai, ta saki jelar har gadon bayanta, kunsan yanda gashin Chinawa yake ai? Ba sai na taya zuba maku dogon bayani ba.
Kana shigowa zaka yi ido huɗu da tampatsetsen frame na president, governor and Defence minister a manne a bango suna fuskantar kofar shigowa. Wani haɗaɗen Chinese door ne daga gefen dama, irin tsadaddun nan ne da suka amsa sunansu, cikin wannan door ɗin, nan ne ainahin cikin office ɗin, duk wanan kawatuwa da na zayyano maku a iya parlour ne kawai, cikin ya wuce tunaninku, idan ka shiga sai ka yi zaton kabar duniya, saboda wani irin ni'ima da zai ziyarceka lokaci guda, wani irin sanyin A.c mai bala'in daɗi ga kuma daddaɗar kamshi air freshener mai matukar kwantar da hankali, su kansu luntsuma luntsumar sofas dake a cikin office ɗin ya isa ya sanya mutun ya saki baki yana kallonsu, office chair ne mai bala'in kyan gaske a wajen wani katafaren table wanda ya haɗu ya gaji da haɗuwa, wannan office chair ya wuce baki ya zayyano kyansa, shi kansa table ɗin ya wuci misali, tiles na kasar floor white color ne mai matuƙar kyau, ga shi fari kal, hakan zai tabbatar maka da cewa mamallakin wannan office ɗin tsabta tana yi mashi mubaya'a, tiles dake a jikin bango light ash ne, sai kyalli suke yi, alamar ko wace rana sai an gogesu tsab, tamkar hannu bai taɓa taɓasu ba, gabaɗaya Curtain dake a cikin office ɗin white color ne masu bala'in tsada.
Wasu tsadaddun desktop computers ne a É—aure a saman wannan tsararriyar table É—in, tulin files ne a gabansa kusa da computers É—in.
Wani santalelen matashi mai jini a jikka ne zaune a saman wannan dankareriyar office chair ɗin nan, tsalelen matashi dogo da shi, daga kafafunsa dake sanye da wasu shegun black covers masu matuƙar kyau da tsada har izuwa kyakkywar dark black curly hairnsa dake kwance mashi har bayan wuya dukka tsadaddun kaya ne da suka amsa sunansu tsadaddun, komai na jikinsa kuɗi aka narka ba kaɗan ba, watch ɗin hannunsa kawai ma abin kallo, danƙareriyar diamond watch mai matuƙar ɗaukar idanu saboda kyalli ne, ɗayar hannunsa na sanye da wata ƴar siririyar diamond hand chain, akwai wani tsadadden diamond ring a ɗaya daga cikin kyawawan fararen ƴatsun hannunsa, baka iya ganin face nasa, saboda ya duƙar da kai ya kurawa wata hoto dake jikin jarida idanu. Black suit ce a jikinsa, ta yi matuƙar yi mashi tsantsar kyau, duba da yanayin fatar jikinsa kamar madara, hakan tasa ya yi wa suit ɗin matuƙar kyau sosai. Gashin kansa sai wani kyalli yake yi tamkar gashin kan Lion namu na Meesha.
Shiru ya zubawa wata hoto idanu yana kallo, idanuwansa na sanye da black glass mai matuƙar kyau wadda ta kara fito mashi da hasken face nasa, soft skin nasa tamkar madara, a kwance luwai luwai, ga wasu chains na zallar zinari masu bala'in kyau a wuyarsa wadda suka sauko mashi har saman chest nasa, fuskarsa a ɗaure tamau kamar hadari, alamar babu wasa a tattare da shi, tamkar yadda face ɗin Lion take a ɗaure kullum, haka nasa face ɗin ma take. Ba komai ya kurawa idanu ba face hoton Lion, bai taɓa sanin Lion ba sai a yanzu da Lion ɗin ya fito takarar neman shugaban kasa, a nan ne ya ga hotunansa a kafafen yaɗa labarai suna yawo, a news sai maganarsa suke yi tare da ɗaura ainahin hotonansa, ga postoci da aka yi mashi, kun san a da can baya ba kowa ya san ainahin face nasa ba, saboda da face mask yake yawo, so a yanzu babu face mask ake buga postocin siyasar tasa, ta hakan wannan matashi ya samu hotonsa na ainahi, abin ya yi matuƙar girgiza shi time da ya fara ɗaura idanunsa a kan hoton Lion ɗin, saboda babu wata banbanci dake a tsakanin face nasa tsawonsa komai nasa da ta Lion ɗin, time da abokinsa ya turo mashi hoton, lokacin da ya buɗe sakon abokin nasa, yana ɗaura idanunsa a kan hoton bai san time da ya miƙe tsaye a razane ba, da farko ya ɗauka hotonsa ne, sai daga baya da ya kalli na jikin hoton da kyau, sai ya lura Lion ya fishi murɗewar jiki, sannan ya fishi cika, kuma a jaridar an rubuta cewa ɗan takarar shugaban kasa na ƙasar America da ya lashe zaɓen primary election a halin yanzu, hakan tasa ya fahimci ba shi ne a jikin hoton ba, kama ce kawai da ta yi over, tun da gari ya waye ya zo office nasa ya fara aiki, tun da abokinsa ya turo mashi jaridar nan ya dakata da yin aikin komai, ya dakatar da kowa da samun damar ganinsa, ya zauna ya zubawa wannan hoto ido yana mamaki tare da al'ajabin irin wannan muguwar kamanni da take a tsakaninsu.
Abin ya yi matuƙar girgiza shi, ya aka suka yi irin wannan kama tamkar mutun guda haka? Abin ya yi mugu mugun tashin kansa ba kaɗan ba.