← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 168

Sashe 111

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A takaice dai tun muna one hundred level a school namu Harvard university Washington DC nake tsananin son Dr William, sai dai shi baya kula kowa, tsoronsa ma nake ji, because he is a dangerous boss, ba shi da sauki ga zafin rai, duk wanda ya bi ta hanyarsa ma take shi yake yi ya wuce, ina tsananin tsoronsa da yasa ban iya bayyana mashi soyayyata ba, muka cigaba da tafiya a haka har na haɗu da wata friend ɗina ƴar kasar Russia mai suna A'isha (gwaggo kenan, dan su ainahi basu san gwaggo tana da alaƙa da Nigeria ba, dan duk takardun makarantarta ya nuna daga kasar Russia ta fito, idan baku mance ba bata yi zaman Nigeria ba, so takardan ɗan kasa da komai nata na Russia ne, shiyasa suka san ita ƴar Russia ce kasarsu Naurat kenan, idan baku manta ba ita ma gwaggo ta faɗa lokacin da suka haɗu da fake William, ta ce mashi dama baka san ni ƴar Nigeria ba ce ko? So basu san tana da alaƙa da Nigeria ba sam, haka zalika a yanzu Cherish bata san Lion ɗan gwaggon bane, yanzu labari take basu ba tare da tasan waye shi ba, fatan kun gane?.) Mun yi ƙawance mai nisa tare da A'isha, ina sonta sosai, saboda tana da kirki, kuma in the first place da gaske muke ƙawancen namu, da gaske nake sonta har cikin ra'ina, shigowar Dr William rayuwarta ne yasa na tsaneta, saboda ina son Dr William tun kafin A'isha ta san shi, shi kuma sai ya zo ya fara sonta, amma haka na danne na jure muka cigaba da tarayya da A'isha ba tare da na nuna mata cewa ina son Dr ba, na yi ƙoƙarin cire Dr a ra'ina, amma abin ya ci tura, na kasa, saboda ina son shi da gaskiya, wani abin haushinma shi ne, son nashi karuwa mani yake yi a kullum, hakan yasa na fara tunanin kashe A'isha, sai dai ban kai ga aiwatar da hakan ba suka yi aure da Dr kuma iyayen Dr suka mutu, wannan dalilin yasa na ɗan dakata da shirin kasheta da nake yi, muka yi zama a haka tsawon watanni kafin na zo nan kasarmu hutu, to a nan ne na sanar da auntyna halin da ake ciki, sai ta ce to na juyarwa da Dr ɗin tunani ta yadda zai tsani Aishar mana kawai, ba sai na kasheta ba tun da nace ina sonta, hakan tasa na ɗauki shawarar aunty na cusawa Dr tsanar A'isha, time da na koma hutu na sami A'ishan da Dr sun yi faɗa har sun raba gida, a lokacin har A'isha ta ce ba zata kyale shi ba sai ta kashe shi, saboda ya ci amanarta, ga ciki a jikinta ya barta da shi, na rinƙa bata hakuri tamkar ban san komai ba, alhalin kuma nasan komai, so in takaice maku labari ban san ya aka yi uncles ɗin Dr suka san cewa na tsani A'isha ba, ina zaune a gidana uncle na Dr wani wai Anderson ya zo gidana a daddare, to a nan ne suka bani aikin na ɗaukewa Josephine hankali ta dai'na ibada ita da A'ishan na tsawon awanni, saboda zasu yi amfani da hakan su juyarwa da Josephine tunani, ita kuma A'isha zasu sanyata ta amsa da bakinta ta bada ɗan da zata haifa domin su ɗauki fansar jinin Roshan da Dr William ya salwantar, suka yi mani alkawarin zasu bani Dr William idan na yi masu hakan, ni kuma ina son Dr sosai, dan haka sai na yi iya kan ƙoƙarina na aikata abin da suka ce, bayan sun juyarwa da Josephine kwakwalwa, suka sanyata ta sa A'isha ta bada ɗan da zata haifa da kanta, (Kunsan labarin yadda gwaggo ta kare da Dr William, so ba sai na sake maimaita shi ba, dan haka zan tsallake.) So a takaice bayan A'isha ta haihu sun ɗauki yaron, sai suka ki cika mani alkawarina da suka ɗauka mani na bani Dr William, sai suka ce mani ai shi ma mai laifi ne, dan haka kashe shi zasu yi, shi ne ni kuma na gwada masu cewa duk duniya babu in da ya kai ƙasar China iya tsafi da makirci, na yi wasa da hankalinsu na ra'ina masu wayon da har yanzu basu iya gane gaskiya ba, na yi amfani da tsafin kanana ni ma na shiga har cikin Daular tasu na ɗauki ainahin Dr William na sanya masu na karya, har zan tafi sai na kalli ɗan A'isha suna ƙoƙarin yin tsafi da shi, shi ne shi ma na ɗauke shi na yi amsani da tsafina na basu wani yaro na karya, abin da yasa na ɗauki yaron kuma, saboda da iya gaskiyata ina son A'isha, kawai soyayyar Dr William ce ta rufe mani idanu yasa na tsaneta, amma da na san na sami Dr, sai na ɗauko ɗan nata na rike, daga nan muka dawo ƙasar nan China da zama, na shafewa Dr William tunanin kowa a rayuwarsa sai ni da ɗansa kuma ɗan A'isha wato Arvin, mu biyu kawai yake tunani, dama already mun gama karatu, sai na buɗe mana karamar hospital kafin muzo mu boɗe babban nan da kuɗi ta zauna, mun yi aure da Dr William kuma mun haifi yara biyu, da Handsome da Pinky, su ne yaranmu, shi kuma Arvin ɗan A'isha ne, amma bai taɓa sanin cewa shi ba ɗana bane, saboda na rike shi da amana, a kullum ina jin zafin cin amanar mahaifiyarsa da nayi hakan yasa na rike shi da amana ko zan goge zunubina dana aikata, su Pinky basu san shi ba ɗana bane, kuma tun daga lokacin ban sake jin labarin A'isha ba, su Josephine duk na rufe babinsu, muna rayuwarmu cikin tsantsar farinciki da kaunar juna, Dr William ma ba ya iya tuna kowa sai mu, saboda na juyar mashi da kwakwalwa, har yau yanzu da nake yi maka magana su His Excellence basu iya gane cewa na ɗauki Dr William da kuma Arvin na gaskiya na sanya masu na karya ba, dan tsafinsu karami ne, mune iyayensu a tsafi, wannan shi ne a takaice labarin abin da ya faru, amma kai kuma da kake kama da Arvin nawa waye kai?!!". BABBAR MAGANA WANNAN SHI NE GABA DA GABANTA WAI ALJANI YA TAKA WUTA, GA IYAYEN SU HIS EXCELLENCE A IYA TANTIRANCI.

Ta kai karshen maganar cikin raunin murya.

Haƙiƙa Cherish ta cuci gwaggo, babban cuta mafi muni da ta yi mata ma shi ne yadda ta bar Arvin ya taso a Kriste, kenan daman musulcin karya ita ta yi? Duk dan ta ci amanar gwaggon, duk dan ta sami kusanci da su ta cutar da su, yanzu Arvin yana da 32 years, amma yana Kristen, ta cuci Dr William ta bar shi a Kristen tsawon shekaru bayan ya musulunta a da can baya, ko iya wannan cuta aka barta da shi ta gama cutar gwaggo sosai.

Shiru Lion É—in ya yi yana tunanin me ya dace ya yi wa wannan shaiÉ—aniyar? Bawan Allah kullum yana cikin jin bala'in da karamar kwakwalwa ba zata iya É—auka ba, ya gama jin nasu His Excellence, yanzu kuma ga wani sabo na Cherish, sai kuma waye next? Dole Malika ta ce suna da ciwo a cikin rayuwarsu, ciwo kam babba kuma ba karama ba, bayin Allah, ga uban makudan dukiya, ga mulki, ga isa da izza, komai sun tara, amma suna cikin matsanancin ciwo da tarin tarihi marasa kyau da rashin daÉ—in ji!!

Shi kuwa Dr William ko kaɗai ma bai iya tuna komai ba, duk wannan labari da Cherish ɗin ta bada, bai iya tunano komai ba, saboda ta juya mashi ƙwaƙwalwar ne, amma shi Arvin ya ji komai, saboda shi babu abin da ta yi mashi, bata juya mashi ƙwaƙwalwa ba, kawai dan yana jariri ta ɗauke shi ta rike shi har ya girma ne yasa yake ɗaukarta a uwa, amma ba abin da ta taɓa daga jikinsa.

Dan haka ya ji komai, a yanzu ya ji ba ita ta haife shi ba, saura Dr William...... Yau ake yinta gaskiya, TRIPLETS gidan surprise, yau kuma kun ji ta in da muka juya, gidan cakwakiya gidan ruɗani, waye ya taɓa tunanin Dr William yana ƙasar China? Waye ya taɓa tunanin su Lion suna da wasu ƴan uwa, Arvin, Handsome da kuma Pinky? Tun da kuka fara karatun littafin TRIPLETS waye ya taɓa wannan tunani? To dai ga shi yau gaskiya ta fito cewa su Pinky dai ubansu ɗaya da su Lion, tashin hankali da ba'a sanya mashi date! Wannan shiri rikici da cakwakiya!! Kada dai daɗin labari yasa ku manta da cewa kuna karanta wannan daddaɗar labarin ne daga Alkalamin FATEEMA ZAHRA MUSA, A.K.A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA MAI ABIN BAN MAMAKI 🤙, zan fa tashi kanku a next book na ina kara gaya maku, ku shirya da kyau, dan TRIPLETS dai remain few pages mu kai karshensa In Sha Allah ❤️

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
Chapter 111 · 0% Book details