← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 168

Sashe 121

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin jijjiga É—akin da suke É—in ya fara yi, almace na yana son rugujewa. Saketa ya yi a hanzarce tare da cire mayafin jikinta duk da babu girma ya rufe Adiva É—in da shi, sannan ya É—auketa cak ya ce da Jehan É—in zu je, su yi sauri su fita gidan zai ruguje, domin Abbon ya mutu duk wasu kambun tsafi ya karye, so dole gidan ya ruguje.

A takaice dai da kyar suka iya sha daga cikin wannan gida, saura kaÉ—an ginin ya ruguje da su, Allah ya taimaka suka fito. A gidan baya na motar ya kwantar da Adiva É—in, sannan suka shiga gidan gaba, a guje ya figi motar suka É—auki hanyar da suka bi suka zo. Gidan tsafin Abbo kuwa ya ruguje gabaÉ—aya da gawarsa a ciki.

A can gida kuwa, gwaggo, Rimsha, Akila da kuma Aafia, sun shirya tsab suka nufi wajen gyaran jiki tare da kunshi haÉ—e da wankin kai. Tga ne zai kai'su, sai kallon Aafia yake yi, yana tuna sumar da ta yi a jikinsa a garden, bayan farfaÉ—owarta da yadda ta zaro mashi idanu da ta farfaÉ—o ta gan shi a gabanta, ta tsorata sosai shi ne ta tashi ta gudu cikin gida, bai hanata ba dan kada ta sake sume mashi.

Yau sun ci kwalliyar Abayas, sun yi matuƙar kyau da su, Rimsha dai sai ɗingisa kafa take yi, tun da suka fito Tga ɗin ya tsare Aafiar da idanu, sun zo zasu shiga cikin motar a gidan baya, ya yi maza ya buɗewa gwaggo karfin motar yana faɗin Aafia ta shiga gaba ba sai sun yi mota biyu ba, su tafi a ɗayar ma ya wadatar.

Cikin hanzari Aafiar ta ce "A'a ni ba zan shiga gaba ba gaskiya, sai dai Akila ko Rimsha su shiga gabar, ni a baya zan zauna".

Why ya tambayeta yana tsareta da idanu.

Kawar da kanta daga kallonsa ta yi tana jin zuciyarta na bugawa da sauri sauri.

"Ni matar mutun ce, dan haka ba zan shiga gabar mota da mijin wata ba, dan Heartbeat bai yarda da hakan ba". Cewar Akila, ta kai karshen maganar tare da wucewa ta shiga gidan baya abinta, tana ta aikin latsa waya.

Guntun tsaki Rimsha ta ja kafin ta ce "Uncle T gaya masu ni haramun ce ma shiga gabar mota idan ba motar yaya Saif ba, kuma ko motarsa ɗin ma sai dai idan shi zai tuƙa ne zan shiga gaba". Cikin masifa ta yi maganar, kamar mai jin haushin wani.

Me gwaggo zata yi idan ba dariya ba? Su Rimsha manya, akwaita da iyayi idan ya gameta, barema yanzu da take jin haushin Lion, sai abin ya shafi kowa, kowa masifa take yi mashi, yanzu shi dai Uncle T uncle nata ne fa, tun da Uncle ɗin Lion ne, amma har da shi yau ya sha masifar, dan hawai tana jin haushin Lion.............😂

"A'a Rimsha ai dama ko da kowa zai shiga gabar motar wani ai banda ke". Cewar Tga É—in, dan ya san halin Lion sarai, ya san shi da bakar kishi, dan haka shi ko da sunan wasa ma baya fatan Rimsha ta shiga mashi gabar mota, yana da tabbacin yanzu ma ba dan gwaggo ba, da wlh Rimsha ba zata tako ko tsakar gidan nan ba, saboda Lion fa karshe ne a É—an banzan bakin kishi.

"Aafia to ki shiga gaban mana kawai". Cewar gwaggo, ta yi maganar ita ma tana shiga cikin motar gidan baya kenan.

ÆŠan turo baki kaÉ—an ta yi. "A'a gwaggo ni nafi son baya ne". "Meyasa to?". Gwaggon ta tambaya.

"Saboda ni uncle T tsoro yake bani". "Meyasa nake baki tsoro?". Ta tambaya yana rufe Kofar motar gidan bayan, dan su gwaggon sun kammala shiga, saura ita kaÉ—ai suka bari a waje tsaye kamar mara gaskiya.

Tsareta da ido ya yi yana jiran amsa, Æ´an kame kame ta fara yi mashi. "Okey now sai ki shiga kawai tun da baki da wani sauran option". Ya faÉ—a tare da buÉ—e mazaunin driver zai shiga.

Turo baki ta yi kamar ta ce ta fasa zuwa, amma saboda tana son ayi mata gyaran jiki da kuma kunshi, sai ta hakura ta shiga, tun da Dr Nawid ya rasu bata sake yin kunshi ba, har ta gama takaba da jimawa, kafin Dr Nawid ya rasu kullum cikin yin kunshi da gyaran jiki take, Allah sarki rayuwa kenan.

Tun da ya fara tukin motar yake aikin kallonta ta cikin mirror motar, jefi jefi ita ma tana satar kallonsa ta gefen idanu, sai dai tafi mayar da hankalinta a saman titi.

Wajen gyaran jikin da suka je last time, nan suka je yauma, har cikin wajen ya bisu, gwaggo tana ganin yadda yake ta aikin kallon Aafia kamar wadda aka bashi gadinta, daga nan ta ce tafiya da Aafia U.s ya kamasu, dan ko basu tafi da ita ba sai Tga ya dawo ya ɗauketa, gara ma kawai su sassautawa bawan Allah kawai su wuce tare da ita, idan sun je komai ya dai'dai ta sai ya musulta kawai a ɗaura masu aure a can, dama bai kamata su bar Aafiar a Nigeria ba, duba da abubuwan da suka rinƙa faruwa da ita a baya, bare kuma yanzu da ta yi aure mijinta ya rasu, ai tana bukatar kulawa ne fiye da can baya, kowa kuma yasan Aunty dai ba zata iya rike Aafia ba, saboda suna ganin bata yi wani karatun kirki ba, so bata waye ba a ganinsu, ita kuma Hjy Hadiza ai bama sai na sake faɗa ba, kun sani tana can tana yawon ta zubar ɗinta, so bazata bi ta kan Aafiar ba, Abbi ba zama yake yi ba, shi ma daddyn Jelly zai koma Kano abinsa, dama a can ya fi wayo, Irfan ya koma school, gidan yanzu babu kowa, dama solution dai kawai gwaggon ta ɗauketa ko kuma su mayar da ita gidan Abba wajen Ammie, tun da ita ma Ammien ba baya ba, ta iya bada tarbiya kuma tana da zafin sosai, ita ce zata iya zama da Aafiar duk da ba ita ta haifeta ba, amma yanzu tafiya da ita U.s ma ai dole ne, dole ayi mata password da komai da komai duk a yau ɗin nan!.

Yau ma dai kamar ranar, kusan wuni zumbur suka yi a wajen gyaran jikin, sai dai fa sun sha gyara, Rimsha dai bata fasa ba, sai dai aka yi mata flowers na zane har wuya abinta, a tafin hannunta ma ta bada kalar zanen da take so ayi mata, ta yi wani irin fitinannen kyau, amma wa ƴan Nigeria ta yi wa kyan, dan su dai TRIPLETS basu son kunshi, ita ma Akila ta biyewa Rimsha aka zana mata har wuya, da yake ita bata san da cewa Aseef baya son ƙunshin ba. (Ni kuwa nace lallai U.s zata kama da wuta, dan duk son da Aseef yake yi mata sai ya goge ƙunshin nan da chemical 😂 yo ni ina ruwana? Ina da Maltina mai sanyi a fridge ai😏)

Wlh kamar ka sace Rimsha saboda tsananin kyau, an kara tsatso mata kyan fatarta da gyara, sun yi wani luwai luwai da su, gwaggo dai bata daddara ba, a karo na biyu ta sake bari an yi wa Rimsha gyara na musamman, ita ma Akilar haka, ita fa gwaggon bata san da cewa kyan da Rimshar ta yi wancan karin ne ya fara ruÉ—ar da Lion ba a wancan ranar ma, ita ta É—auka sai da ya shigeta ne ya gigice, bata san daga kallonta ma da ya yi bane ya gigice É—in, sai ta bari aka sake zuba masu gyara na musamman, sun yi kyau kam, Akila ba'a magana, sai tashin wani fitinannen kamshi suke yi, dan anyi masu wankar turare.

Da yake Tga yana zaune a parlourn wajen ne bai bisu can ciki ba, saboda gyaran jikin da za'ayi masu sai a can cikin bedroom, dan sai an shafe dukkan jikinsu da kayan gyara da sauransu, shi ne yasa ya zauna a parlourn saman sofa yana jiransu. Time da suka fito shi da kansa sai da ya miƙe tsaye yana kallonsu, sun zama kamar wasu taurari masu matuƙar hasken gaske, sai dai kuma shi ma baya son ƙunshi, da alama hakan a jininsu yake, ko kuma saboda Lion baya so ne ya dasa masu tsanar abin suma, saboda kada ma su kawo mashi a arear da yake.

Sai kallon Aafia yake yi tamkar wani ya ce zai ɗauketa, ita kuma sai faman ɓoyewa take yi kada su haɗa ido, dan ita tsoron ash eyes nasan nan ma a zahiri take yi, gara a Tv tana iya kallonsa sosai, a zahiri sai idanun suna bata tsoro, tana ganinsu suna wani haske, a haka ma dan bai taɓa zaro mata su ba. (Ni kuma nace dan bata taɓa yin 4 eyes da blue eyes na Lion bane, ai da sai ta kusa fitsari a wando, musamman ma ace da daddare, kuma ya zarosu😂 ya kuke gani?😂)

Gaba ya yi suka rufa mashi baya, gidan baya na motar ya je ya buÉ—ewa gwaggo. Kamar yadda suka zo haka suka shiga a komawar ma, wajen shopping suka nufa. Abubuwa sosai suka saya, komai da suka yi Tga ne yake ta aikin biyan kuÉ—i, sai da suka kammala komai suka dawo gida.

Suna dawowa kuma suka hau shirin tafiyar da zasu yi gobe, sam ba zama. Su kuwa Areef da Jehan da kyar motar nan tasu ta iya mayar da su wajen asibitin da Maryam take a kwance, suna zuwa suka miƙawa likitocin Adiva ɗin ma, dan a ɗan yi mata dressing su sami ta yadda zasu wuce Kd da ita, daga nan suma ya yi masu password and visa, dan ya ce ciwon nan nasu sai kwararrun likitoci, Allah ma yasa da jet ɗin Lion zasu tafi, dan yana isa U.s ya sake sanyawa aka tashi jet ɗin dan ya zo Nigeria ya ɗaukesu, ba jirgin kasuwa zasu bi ba, saboda tafiya mai gabaɗaya zasu yi, sun sallami Nigeria kenan.

Ko da suka koma asibitin ba laifi, jikin Maryam É—in da É—an dama dama, ba kamar yadda suka É—auko ta ba, sai dai har yanzu ba'a iya gane menene ainahin abin da yake damunta ba.
Chapter 121 · 0% Book details