Sashe 93
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai tsaye gida ya koma da ita. A haukace yake taka motar, dan su isa da wuri. Wani irin horn mai sauti ya fara dakarawa gateman tun bai kariso bakin gate É—in ba. A hanzarce suka wangale mashi gate É—in.
A guje ya danna hancin motar ciki, yana kashe motar a parking space ya fito tare da buɗe gidan bayan, babu ɓata lokaci ya saɓeta a kafadarsa zuwa cikin gidan.
Kai tsaye bed nasa ya wuce da ita, sai zubar da jini kanta yake yi, a iya kai ne kawai ta samu buguwa, kuma fashewar ba dayawa bane, amma da yake shi jini kofa kaÉ—an idan aka yi mashi ya samu hanya, to zuba kawai zai yi ta yi, buguwar da kan nata ya yi ne kuma yasa ta sumewa.
Katafaren bed nasa na'a shunfuɗe da white bed sheet, a haka ya kwantar da ita a kai da jinin nata, bai wani damu ba. (Abin mamaki, Uncle T da ya tsani bakar fata yau shi ne da taimakon bakar fata? Kuma har ya ɗaga hankalinsa haka?🤔 Abin da mamaki)
Fitowa ya yi tare da haurawa saman benen. A bakin kofar bedroom na Lion ya tsaya tare da yi mashi excuse, dan Lion ɗin ya shata masu layi da shiga ɗakinsa a yanzu, ya ce kada su rinƙa shiga mashi kai tsaye, dan matarsa tana kwance a ciki, baya da bukatar kowa ya kallah mashi ita a kwance, idan ta fito da kafafunta, wannan suna iya kallon face nata, amma tana a kwance a cikin bedroom nasa kam bai lamunta wani ya ganta ba, hakan yasa suke yi mashi excuse su kuma tsaya sai ya fito.
Ya ɗauki tsawon a kallah minti 10 a tsaye a wajen lafin Lion ɗin ya fito, jikinsa na sanye da kayan barcin masu matukar kyau, launin milk color, sai tashin kamshi yake yi kamar anyi ɓarin perfume a jikin nasa.
Ko da ya fito ma bai yi magana ba, sannan kuma tun da ya É—aura idanuwansa a kan uncle T É—in nasu, kallo É—aya ya yi mashi yasan ba lafiya ba, ga jini a hannunsa da jikinsa, sai dai bai tambaye shi meyake faruwa ba, ya tsaya shiru dai ya zuba mashi idanu.
"Lion I need A box and the rest". Ya faÉ—a cikin nutsuwa. Shiru Lion É—in ya yi mashi na tsawon mintoci kafin calmly ya ce "What is going on?".
Ba tare da ɓata lokaci ba ya bashi labarin abin da ya faru sama sama, daga karshe ya gaya mashi cewa yarinyar da ya buge ɗin tana dakinsa a sume, shi ne yake son dubata.
Jinjina mashi kai Lion ɗin ya yi, saboda yasan uncle T ɗin ma ba baya ba wajen sani da kuma karantar aikin likita daga wajen daddynsu na karya, ko ace photocopy, an cucesu aka sanya mashi komai na ainahin Dr William, harta ilimi da komai, da yake abu ne na tsafi, sai dai ko ba komai sun karu da shi, ga shi yanzu suna iya treating na kawunansu idan basu da lafiya, sam basu zuwa hospital sai idan abu ya zama mai matuƙar zafin gaske, amma ciwo irin na yau da kullum tsab suke duba kawunansu.
Ciki ɗakin Lion ɗin ya koma, jim kaɗan ya fito mashi da duk abubuwan da yake buƙata ɗin, dan su a wajensu dan Tga ya kawo mace wanda ya buge da mota, dan zai dubata ba su ɗauki hakan a bakin komai ba.
A hanzarce ya karɓa tare da juyawa ya nufi bedroom ɗin nasa. Shi kuma Lion ya koma ciki, har yanzu dai Rimsha shiru shiru bata farfaɗo ba, kusa da ita ya kwanta yana ta kallon face nata, ta kara wani irin azababben kyau, saboda karin ruwa da ake ta yi mata, tana kwance a sume, babu ci babu sha, drip kawai ake ta loda mata, dan ya taimakawa jikinta kada ta nakasa, hakance tasa ta kara kyau, kun san dama fa shi drip yana sanya mutun ya yi ƙiba ya kuma kara haske da kyau, duk wanda aka yi wa karin ruwa a hospital, zaku gan shi ya kara ƙiba, sai dai idan dama ba mai jikin ƙibar bane ba, amma koma yaya zai ɗan murmure.
Sosai ya zuba mata idanu babu ko kyaftawa, idan ya kalleta sosai, sai ya kai kyawawan lips nasa saman nata ya sumbata, sannan ya cigaba da kallonta kamar wani ya ce zai kwace mashi ita, ko ance za'a rabasu.
Shi kuwa uncle T, yana shiga bedroom ɗin nasa ya fara dubata cikin hanzari. Da yake bata ji wani ciwo sosai ba, a iya kai ne kawai, cikin ƙanƙanin lokaci ya kammala komai tare da yi mata alkuran barci, sannan ya nufi toilet dan ya yi wanka, sai tunanin face nata yake yi, ta tsaya mashi a ransa, sai dai bai ɗauki hakan a matsayin wani abin ba, ya mayar kawai taimako ne.
Bayan ya yi wanka ya fito, shiryawa ya yi cikin kayan barcinsa masu kyau da tsada, kusan irin na jikin Lion. Saman bed É—in nasa ya haye abinsa, tana gefe guda, shi ma ya kwanta a gefe guda tare da É—an rage gudun A.c, dan kada sanyi ya daketa. A hankali ya lumshe idanuwansa, ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi.
A ɓangaren su Abbi kuwa, time da suka dawo gida, ba ƙaramar tashin hankali suka shi ga ba ganin Aafia bata a gidan, kasancewar dare ne, sai basu kira su Abba sun tayar masu da hankali ba, suka fara nemanta a cikin unguwar, ita kuwa Hjy Hadiza tana can wani kauye wajen wani malami, a can zata kwana, Aunty baiwar Allah ta shiga damuwa na wuce misali.
Sun sha yawo kamar ba gobe, amma babu Aafia babu dalilinta, haka suka dawo gida har wuraren 12 na dare, ga gajiyar hanyar Katsina, ga wahalar yawo a cikin unguwa, mai gadi dai ya shaida masu Aafia da kafarta ta fita gidan da gudu, ga shi babu waya a hannunta bare su kirata, haka suka kwanta jugum jugum, a wannan dare dai barci ya gagaresu, dan suna cikin tsaka mai wuya, Allah Allah suke yi kawai gari ya waye su shiga nemanta babu kakkautawa, baiwar Allah ga shi ba lafiya yake gareta ba. Ita kuma Hanan sun barta a Katsina, dan next week za'a ɗaura auren nasu, A'A ya ce baya son ɓata lokaci, ayi komai da wuri a wuce wajen, to shi ne yasa suka barota a can zata yi kwana biyu, dan ta bi ƴan uwa su yi ban kwana, daga nan sai ta dawo gidan Abbin, dan a nan za'ayi komai na bikin, Abbin ya ce ba zasu sake zuwa wajen babanta ba, gara ayi komai a gidansa cikin mutunci tun da baban ya amince.
Washegari tafiya ce ta kama Lion cikin gaggawa, bashi da zaɓin da ya wuce ya koma U.s, sam baya jin kamar zai iya tafiya ya bar Rimsha ba tare da ta farfaɗo a gabansa ba, amma dole ce tasa sai ya tafi ɗin, saboda primary election da sauran abubuwa, ba zai yi wu ya tafi da ita ba, dole zai barta a nan.
Gwaggo ce ta yi ta kara mashi kwarin gwiwa a kan ya je kawai zata kula da Rimshar sosai, kada ya damu. Shiru ya yi bai amsa mata ba, dan shi gani yake yi ma ita fa gwaggo sam bata san me yake ji ba, ba zata gane halin da yake a ciki bane, da zata shiga cikin zuciyarsa ta ga irin azababben son da yake yi wa Rimsha, da sam ba zata taɓa yin gigin ce mashi ya yi hakuri ya tafi ya barta ba.
Karfe 7 na safe ya kamata jirginsa ya É—aga, amma sai ya É—aga tafiyar zuwa da yamma, duk saboda Rimsha, duk da baya jin cewa zata iya farfaÉ—owa a cikin wannan satin ma gabaÉ—aya ba yau ba, amma ya jinkirta tafiyar tasa zuwa yamma, dan ya kara kula da ita sosai kafin ya tafi.
A ɓangaren Jehan kuwa, duk ta yi laushi, ta rame sosai, amma har yanzu taki yarda ta kira Areef ɗin a waya ma bare ta bashi hakurin.
Sam Areef baya son wannan rama da take yi, abin yana kona mashi rai, sai dai bashi da zaɓin da ya wuce ya bi maganar mum, a koda yaushe yake son ganinta, zai ganta, amma ita ba zata gan shi ba, saboda bata san cewa yana da hanyar ganinta ɗin ba, sai dai fa shi ganinta bai wadatar da shi ba, ba iya ganinta da ido yake da buƙata ba, yana bukatar jin voice nata, duk da kullum dama cikin dirama suke, ba wasu kamai da take gaya mashi, amma yana son diramar, yana son jin muryarta tana yi mashi diramar, ba wai ya ji muryarta tana magana da su gwaggo ba, in takaice maku shi fa komai Jehan ta yi burgesa take yi, pure love na kin karawa yake yi mata, tsayawa zayyana irin son da yake yi mata ma ɓata baki ne, dan bakin ya yi kaɗan wajen iya zayyana shi.
A takaice sai misalin karfe 5 jirgin Lion ya ɗaga zuwa U.s, zuciyarsa sam babu daɗi na rabuwa da Meesharsa, babban abin da ya fi ɓata mashi rai ma shi ne, yanda tafiyar ya kama shi ba tare da Meeshar tasa ta farfaɗo a gaban idanunsa ba, shi ne ya ɓata mashi rai a game da tafiyar kawai.
A ɓangaren Tga kuwa, washegari da safe da ya tashi, wanka ya fara yi tare da shiryawa cikin tsadaddun kayansa, ya fito ya nufi motarsa ta jiya, bai bi ta kan Aafia ba, duk da tana kwance a saman bed nasa, kuma ya ganta sarai, sai dai wani abin ya sha gabansa, akwai in da zai je.