← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 168

Sashe 124

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wannan rana dai haka suka wuni cikin farinciki, Sir Arvin yaki yarda ya rabu da Lion da kuma Aseef, sun sake komawa TRIPLETS tun da Areef baya nan, duk ya ƙosa su Areef su iso ya ga cikon ɗayansu, yau a bedroom na Lion suka wuni, shi kuma Handsome a tare da daddyn Rimsha ya zauna, sai tunanin Dr Cherish yake yi, ita kam Pinky abin da kuka sani ne, tana manne da Sir Arvin, dan shi ta sani, da shi ta saba, ta saba da shi sama da mummynta, shiyasa ko'ina suna a tare.

Da daddare ma sir Arvin ya ce shi a bedroom na Lion zai kwana, dama shi Aseef ai already sun saba in dai kwana a bedroom na Lion ne, sai su zo su haye mashi bed nasa shi da Areef, su haye su kwanta, su bar nasu part É—in, to yau shi ma Sir Arvin ya ce babu in da zai je, Lion ya ce mashi da akwai almost parts empty da babu kowa wajen guda uku a wannan hawa da suke, ya É—auki É—aya, ya ce sai wani lokaci zai É—auki É—ayan, yanzu dai a nan zai kwana tare da su.

Aseef kuwa ya ce mashi "Ai bed É—in tana É—aukarmu mu dukka TRIPLETS dama, dan haka ga toilet ka yi wanka ya sanya kayan barcin Lion kazo mu kwanta, ni bari na kira matata".

ÆŠan zaro dara daran blue eyes nasa sir Arvin É—in ya yi tare da faÉ—in "Wow kana da mata?".

Jinjina mashi kai Aseef É—in ya yi tare da fito da hoton Heartbeat É—in tasa yana nuna masa.

Karɓar wayar ya yi yana kallonta. "She's so beautiful, amma bata sanya maka ciwon kai ko?".

Lion ne ya amsa mashi da cewa "Ƴar aljanna ce in ji Aseef ɗin, ƴar aljanna kuma ai kaga ba zata sanya mashi ciwon kai ba".

Kallon Lion É—in da kyau sir Arvin É—in ya yi kafin ya ce "Okey we can see ai, ni dai nasan mata koya kake dasu sai sun sanyaka ciwon kai, haka Dr Cherish da daddy, kullum cikin sanya shi ciwon kai take yi, ya yi ta faman shan magani, kuma wai a haka tana son shi".

Karɓar wayarsa Aseef ɗin ya yi yana faɗin "No my heartbeat dai daban take da kowace mace, wai baka ji Lion ya ce maka ƴar aljanna bace? Ai ƴar aljannarce da gaske, bata laifi, kuma bata son ɓacin ra'ina, ni ku bar damuna bari na kirata mu sha love ɗin mu".

Jinjina mashi kai kawai sir Arvin É—in ya yi, dama shi Lion baya kula shi in dai a kan Heartbeat ce, dan fa shi Aseef bai yarda Heartbeat zata yi mashi laifi a duniya ba, Æ´ar aljannarsa ce.

Nufar toilet sir Arvin É—in ya yi, ita dai Pinky tana zaune kusa da Lion saman bed, ta yi shiru abinta, wannan ita ce Queen amount the Kings, ita kaÉ—ai ce mace a cikinsu, gata Æ´ar karama, zata sha gata kam, daga wajen Lion sai wajen sir Arvin abinta.

Har sir Arvin ya je zai shiga toilet É—in, sai kuma ya dakata tare da juyowa, a kan Lion ya sauke idanuwansa, while shima Lion É—in shi yake kallo. "Kai fa? Kana da mata?". Sir Arvin É—in ya tambaya.

Jinjina mashi kai ya yi, calmly ya ce "I have a Queen amount the Queens, one in million".

Duk da sir Arvin baya dariya, a wannan gaɓar sai da ya ɗan yi siririn murmushi kaɗan, sannan ya ce "Oh ashe ba laifin Aseef bane, kai ma hakance, ƴar aljana wadda bata laifi kai ma ke gareka ba?".

Shiru Lion É—in ya yi bai amsa mashi ba.

"Will you show me her pic's?". Cewar sir Arvin É—in.

Girgiza mashi kai Lion É—in ya yi. "No". Ya faÉ—a tare da kwanciya da kyau a saman bed É—in.

Kamar zai tambaye shi meyasa ba zai nuna mashi ita ba, sai kuma ya fasa ya wuce cikin toilet É—in kawai, sai dai zuciyarsa cike tab da mamakin ya aka yi matar Aseef take bakar fata? A haka ma bai san Akilar fara ce tas a Nigeria ba, in da Rimsha ya gani ne sai ya ce mata baka kai tsaye, saboda ita ce chocolate color, su Akila da Jehan ai fararen tattabaru ne, amma da yake shi mai jan kunne ne sai yake masu kallon bakaken fata.

A takaice dai a tare suka kwana a saman bed guda su ukun, Pinky dai tana manne da Sir Arvin, taki rabuwa da shi, a saman kirjinsa ta kwanta, kuma Lion bai rabasu ba, dan ya lura sun yi muguwar sabo fiye da tunanin mutun, so ba zai so a rabasu a kaita wani bedroom É—in ba, sai dai da suka yi barci shi ya tashi ya bar masu bedroom É—in, ya koma part É—in Areef ya yi kwanciyarsa kayansa.

Washegari da safe suka rinƙa damunsa da tambayar meyasa ya gudu ya barsu da suka yi barci?. Shiru ya yi masu bai amsa masu ba, haka suka gama takura mashi da tambayar, da dai suka ga ba zai amsa masu ba, sai suka kama kansu suka nufi dining room, dan su yi breakfast.

Dr William kuwa tun wannan suma da ya yi jiya, har yau bai farfaÉ—o ba, kuma Lion ya hana a zuba mashi ruwa, ya ce su kyale shi na É—an lokaci, dan da alama kullin da Dr Cherish ta yi mashi ne yake son kwancewa, shi ne ma yasa ya shiga doguwar suma bawan Allah.

Sai da suka yi breakfast a tare cikin farinciki, kowa yana farinciki amma banda Handsome, yana cikin damuwa bawan Allah. Yau Lion ma a tare da su ya yi breakfast, duk da baya karyawa da wuri, yau saboda su ya karya da wuri.

Bayan sun kammala ne suka É—ugunzuma izuwa bedroom na Dr William da yake kwance, yana kwance kamar yadda Lion É—in ya kwantar da shi jiya, sai dai ko da suka shiga sai suka tarar da ya fara motsi, a hankali yake motsawa yana sambatu kasa kasa, basu iya jin me yake faÉ—a, saboda kasa kasa sosai yake magana.

Sai da suka matso kusa da shi ne suka fara jiyo abin da yake faÉ—a kasa kasa. Ba komai yake faÉ—a ba kuma face sunan gwaggo. A'ish, A'ish, yake ta kira.
Tsawon shekaru talatin da uku zuwa da huÉ—u kenan yau, tun kafin a haifi TRIPLETS ya rabu da gwaggo, amma yau sai ga shi anwayi gari bayan tsawon waÉ—an nan shekaru dukka ya farfaÉ—o da ambatar sunanta, Allah Akbar. Da alama ya dawo cikin hayyacinsa ne.

Sosai sambatun nasa yake kara yawaita, zuba mashi idanuwa suka yi suna kallonsa, Lion da daddyn Rimsha ne suka yi karfin halin fara tofa mashi adduo'i, dan kada ya tashi a birkice, suna tofa mashi adduo'in ne dan Allah ya taimakesu ya tashi a cikin nutsuwarsa.

Sir Arvin kuwa tuni idanuwansa suka ciko da kwallah tab, hakika ya ji tausayin daddyn nasu da kuma mommar tasu, tsawon waÉ—an nan shekaru masu uban yawa haka! Shin gwaggon ma zata yarda da shi kuwa? Idan fa aka karyawa mutun zuciya a karon farko, mawuyacin abu ne ya sake yarda da koma me! Allah sarki Dr William, rayuwarsa da akwai ciwo ainun.

Sun jima a haka kafin nan su samu ya farfaɗo mai gabaɗaya, ko da ya farfaɗo kuma da sunan gwaggo a bakinsa ya farka, ya tashi ne da tambayar ina take? Sai dai sun yi sa'a ya farfaɗo cikin hayyacinsa, ya farfaɗo a cikin nutsuwarsa, wannan adduo'i da suka rinƙa yi mashi ta taimaka mashi sosai. Sai dai fa kamar yadda Dr William ya dawo normal sanadiyyar mutuwar Cherish, haka suma su Anderson suka sami damar gane cewa ba Dr William na gaskiya bane a hannunsu, saboda Cherish ta mutu komai ya karye, gaskiya ta bayyana, akwai kura ba kaɗan ba, kada ku manta shi Sir Arvin ba musulmi bane ba, zasu iya ganinsa a duk in da yake tun da shi ne nasu, shi ne aka basu, shi suka ɗauka Cherish ta ra'ina masu wayo, ta kwace shi, tab ga rai'inin wayon da ta yi masu, hakan zai kara bakanta masu rai, akwai badakala!!.

Dr William yana É—aura idanuwansa a kan su Lion É—in ya dakata daga ambatar sunan gwaggo da yake yi, zaro idanuwansa ya yi yana kallonsu da mamaki, ga shi Lion da sir Arvin ya fara sauke idanuwansa a kansu, su ne masu kama da shi kuma. Cike da mamaki ya kai hannu ya shafi face nasa, dan ya ji wai nasa face É—in tana nan ne ko dai ita ce aka cire aka sanyawa waÉ—an nan masu kama da shi É—in?

Tambayar kansa yake yi su waye su? Sam bai san cewa yaransa bane, bai ma kawo a ransa cewa yanzu shakaru 32 sun wuce ba, shi dai yasan tabbas gwaggo tana da ciki, kuma cikin nata bai wuce wata 3 ba a lokacin da ya sani, to suwaye waÉ—an nan masu kama da shi É—in kuma?.

Tambayar da yake ta faman jefawa kansa cikin ruÉ—ani kenan, ya shiga ruÉ—ani, ya kalli Lion ya kalli sir Arvin....... Allah sarki Dr William bawan Allah.

Ganin haka yasa daddyn Rimsha da yake ya fisu girma, ya kuma fisu sanin yakamata, sai ya ce masu bari ya bawa daddyn nan nasu labarin abin da ya faru, idan ba haka ba ƙwaƙwalwarsa tana a cikin ruɗani over, dan haka kowa ya zauna za'a sake dawo da labari daga farko.

Dukkansu babu wanda ya musawa daddyn Rimshar, waje suka samu suka zauna. Cikin nutsuwa daddyn Rimsha ya fara yi wa Dr William bayanin komai, tun daga farko har karshe izuwa yau yanzu da suke zaune, tashin hankali. Dr William ya yi shekaru 32 zuwa da uku bai san in da kansa take ba! Bai ma san wanene shi ba, anyi ta wasa da kwakwalwarsa tamkar yadda ake buga ball, bawan Allah, Allah ne kaÉ—ai zai saka mashi wannan cuta da suka yi mashi, amma hakika ancuce shi ba kaÉ—an ba!!.
Chapter 124 · 0% Book details