← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 168

Sashe 33

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karɓar wayar Lion ɗin ya yi, cikin sauri ya fara kiran number Rimsha, dan dama ya kawo wa ransa za'ayi wa matan familynsu gwaggo ɗauki ɗai'ɗai, kuma idan basu yi saurin ɗaukar mataki ba, duk za'a kashe matan ne, dan da alama babu wasa a lamarin masu aikata hakan, bare ma da suka san yanzu asirinsu na gab da tonuwa, ai sai dai wanda Allah ya ƙaddara kwanansa na gaba, amma za'a zubar da jini kam ba kaɗan ba!, Kuma dole hankalinsa zai tashi, saboda a halin yanzu Rimsha ta fi kusa da shi sama da kowa, kuma ga shi shi ne yake shirin bankaɗo gaskiya, shi ne babban makiyin mutanan, ko dan a sanya shi ya rusina, za'a iya yi mata wani mummunar abin, so dole ta kasance a tare da shi a ko da yaushe, rayuwarta yana cikin hadari sosai, da alama ya yi shigar sauri wa mutane, bai shirya ba ya shiga yakin, hakan kuma zai wahalar da shi da na kusa da shi ba kaɗan ba!!.

Sai kiran wayar yake yi, amma ina bata É—auka ba, number Areef ya kira, su kuma a lokacin sun kamo hanyar Kaduna, babu network sam, number bata shiga, tsaki ya ja tare da dakawa Mark tsawa a kan ya taka motar nan da sauri su kai gida da wuri, dan ya duba ya tabbatar Rimsha tana gida or not. Babbar magana.

Mikawa gwaggon wayar Aseef É—in ya yi, cikin sanyin murya ya ce "Momma ki gayawa dukka uncles namu yanzu ba sai anjuma ba mu haÉ—u a gida, dukkansu da Æ´aÆ´ansu gabaÉ—aya".

"Saif meyake faruwa ne? Ɗazun Abban Imran ya kirani ya ce Ayla matar uncle naku Maik ta ɓata, daga baya ya sake gaya mani mijin Aafia ya rasu, ita kuma Aafiar bama su san a wani point zasu ajiye ta ba, yanzu kuma na ji Nawazuddeen yana tambayar Aseef ina Akila, me dukka wannan ne?".

Nisawa ya yi kafin ya ce "Momma babu komai, just tell them what i said kawai, and ki yi sauri ki bani wayar ina son in gayawa Areef a duk in da yake, ya yi sauri ya zo gida ina son yin magana da shi......." Bai kai ga rufe baki ba Mark ya ja wata mahaukaciyar burki, waddata sanya su suka tafi luuuu suka buga kansu da jikin sofar motar, shi ma Mark É—in sai da ya buga kansa da jikin steering motar.

Kusan a tare suka É—ago kawunansu tare da kai kallonsu a gaban motar, dan suga menene ya sanya Mark É—in taka irin wannan burki haka...................

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

E9

Kusan a tare suka É—ago kawunansu tare da kai kallonsu a gaban motar, dan suga menene ya sanya Mark É—in taka irin wannan uban burki haka.

Ko da suka É—ago kansu, babu komai a wajen, kan hanyar wayam, da mamaki Aseef yake kallon Mark É—in, bawan Allah shi kuma wata halitta ya gani tsaye a tsakiyar hanyar, shiyasa ya yi kokarin kauce mata, ashe gizo kawai aka yi mashi, da alama an shirya masu hakan ne domin su yi accident, sai kuma Allah ya karesu da kariyarsa.

Aseef É—in zai yi magana, Lion ya dakatar da shi, sannan ya ce da Mark É—in su tafi kawai.

Kunna motar ya yi suka cigaba da tafiya, ita kuma gwaggon ta kira su Abba kamar yanda Lion ya ce mata, daga haka babu wanda ya sake yin magana a cikin motar.

Har sun kusa isa gida, kome Lion ya tuna, sai ya karɓi wayar Aseef ɗin ya turawa Areef massage a kan ya tsananta addu'a sosai a duk in da yake, kada ya bari askar ta kubce daga bakinsa, dan fa akwai gagarumin matsala ba kaɗan ba.

Motarsu na yin parking a cikin gida, motar su daddyn Rimsha ma ya shigo cikin gidan, gabaɗaya familyn sun haɗu waje guda, ita ma Akilar sun ganta, ashe makwabtansu ta shiga, ta je su gaisa ne, dan kunga tun da ta yi aure, ai bata je ba, shi ne yanzu da dama ya samu, sai ta leƙasu. Ita kuma Ayla shiru, babu ita babu labarinta.

Mark yana kashe motar Lion ya fita daga cikin motar, bai bi ta kan kowa ba ya wuce cikin gida da sauri. Kai tsaye bedroom nasa ya nufa, ya sha ruwan mamakin ganin Rimsha tana zuba barci har iyanzu, kai kallonsa a kan agogon bangon dake manne a cikin É—akin ya yi. Almost 4 to 5 hours tana zuba barci, anya barcin nan na lafiya ne kuwa? Ya tambayi kansa.

Karisawa cikin É—akin ya yi, cikin nutsuwa ya haye saman bed É—in, hannu É—aya ya sanya ya tallabo kanta, sannan ya sanya É—ayar hannunsa ya shafa kyakkyawar face nata.

Cool murmushi ta saki har sai da dimples nata suka yi wani irin lotsawa mai matuƙar ɗaukar hankali. Cikin magagin barci ta fara faɗin "Kai Noorish ka bari mana". Kamar tasan shi yake taɓata.

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kai É—an bakinsa ya sumbaci lallausan lips nata, sannan ya kankameta gam a kirjinsa, yana mai jin wani irin tsananin kaunarta tana ratsa shi. Ya É—an É—auki lokaci a hakan kafin ya mayar da ita a hankali ya kwantar, sannan ya diro kasa ya nufi toilet, ita kuma, cigaba da barcinta ta yi cikin kwanciyar hankali.

Hakika tabbas an so ɗaukar Rimshar kamar yanda Lion ɗin ya yi tunani, Malika ta ɓoyeta, ko da aka zo ɗaukarta ba'a ganta ba, Malika ta lulluɓeta da nasu siddabarun na aljanu, a gaskiya Malika tana kaunar Rimsha sosai, sannan kuma tana kula da ita sosai, sau da dama tana tare mata abubuwa da dama wanda idan ba ta gaya maku ba, ba zaku taɓa zaton ita ce ta tare ba, so ake ta karfi da ya ji a ladabtar da Lion, so suke su rufe mashi baki a kan case ɗin, so dole suna son yin amfani da rauninsa, dan su sanya ya rusina, sai dai kuma kash, dukka raunin nasa baza su taɓu ba, barema Rimsha da take tare da Malika, ba zata taɓa taɓuwa ba, sai dai idan shammatar Malikar aka yi, tun da dukka abune na tsafi da aljanun, so babu abin da ba zai iya faruwa ba.

Wanka Lion É—in ya yi, sannan ya fito ya shirya cikin kanana kaya, wando three cuter fara kal, da T-shirt sky blue bara nauyi, bai É—aure gashin kansa ba, ya saketa.

Wayarsa ya zo ya É—auka a saman bed, number Areef ya sake gwada kira, still dai bata shiga, zama ya yi a bakin bed É—in, number Mark ya kira a kan ya zo ya gyara mashi bedroom nasa, ya kwashe laptop da ya fasar nan.

Yana katse kiran ya ji saukar hannayenta a saman kugunsa ta wajen flat tummynsa, ta rungume shi ta baya, a hankali ta kwanto da kanta a saman bayansa, da murya irin na mai barci ta fara magana. "Noorish shi ne baka tashe ni daga barci ba ko?".

Nisawa ya yi, har cikin ransa ya ji sassauci na abin da yake ji, ya ji sanyi sosai, hannun nata ya riko ba tare da ya yi magana ba.

"Noorish na yi mafarkin wani waje, in gaya maka ina ne?". Tana magana kamar wadda barci bai isheta ba.

Juyowa ya yi a hankali, sannan ya jawowata ta dawo saman kirjinsa, zubawa face nata idanu sosai ya yi. Idanunta a rufe ruf take zuba surutu, sai guntun murmushi dake a saman face nata, ga dimples nata duk sun lotsa sosai, sai ta kara kyau matuƙa.

"Meesha tun da na bar gidan nan baki tashi daga barci ba?". Ya faɗa cike da tantamar irin barcin da ta rinƙa zubawa kamar ba gobe, abin da bai sani ba shi ne, Malika ce ta sakata yin wannan barci, dan da ta farka, to babu abin da zai hana Josephine bata ɗauketa ba! Saboda yanzu farautar rayuwarta suke yi tamkar ruwa mai sanyi a sahara mai tsananin zafin rana, a gefe guda, ga Queen of Daular Mutuwa tana nemanta ruwa a jallo, daga ɗayan gefen kuma, su Josephine suna nemanta ko ta halin kaka ne su ɗauketa, dan hawai su karyar da zuciyar Lion ɗin, hakan tasa Malikar ta sakata wannan uban barci kamar ba goben, har sai da ya dawo, sannan ta tafi ta basu waje, shi ne ma Rimshar ta iya farkawa.

"Noorish ban tashi ba, nifa yanzu na tashi, dama ka fita ne? Shi ne baka tashe ni na raka ba? Na ɓata da kai to". Ta kai karshen maganar tana haɗe mashi fuska, irin ta yi fushin nan.

"Open your eyes first, sai ki kalli cikin idanuna ki ce mun ɓata". Make mashi kafaɗa ta yi.

Hannu ya kai ya shafi lallausar wuyarta dake kara É—aukar hankalinsa a koda yaushe. "Open your eyes". Ya faÉ—a yana gangaro da hannun nasa izuwa kirjinta.
Chapter 33 · 0% Book details