← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 168

Sashe 21

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuma Lion kalma ɗaya zuwa biyu ne suke mashi yawo a cikin ƙwaƙwalwasa, na farko, cewa da gwaggon ta yi TRIPLETS nata biyu daga ciki kamanninsu ɗaya, kuma dukkansu biyun blue eyes ke garesu, shi kuma ɗayan idanunsa daban, to shi dai Lion yasan su TRIPLETS da Dr William ya haifa, dukkansu idanuwansu daban daban, babu wanda idanunsu yake iri ɗaya, Areef ash eyes, Aseef brown eyes, shi kuma Lion ɗin blue eyes, kuma duk cikinsu shi kaɗai ne yake kama da Dr William kamar yanda gwaggon ta faɗa, to ya aka yi hakan ta faru?! Ina blue eyes na ɗayan?! Meyasa kuma bai yi kama da Dr William or Lion ɗin ba?! Wannan abin ya tsaya mashi a rai over, idan ya yi tunanin to ko dai ɗaya daga cikinsu Areef ba TRIPLETS nasa bane, sai kuma yaga hakan sam ba zai yi wu ba, duba da yanda suke jin bugun zuciyar juna, sannan suna da kwari da kunama, ga kuma uban shakuwa da take a tsakaninsu na wuce misali, kai bama zai taɓa yiwuwa ace ɗaya daga ciki ba cikon TRIPLETS bane! Hakan sam ba zai yiwuba! Dole dai da akwai abin da ya saɓa, kuma dole Josephine da Dr William ne za su faɗa menene ya saɓa ɗin!!. Abu na biyu da yake ta jujjuyawa a cikin ƙwaƙwalwasa kuwa, ya aka yi su Dr William suka koma Kristen? Kamkar basu taɓa musulta ba, kuma a labarin da gwaggon ta bada, har karatun Alkur'ani mai girma sun iya sosai, to ya aka yi suka canza? Canzawa mai ban mamaki haka? Ina Cherish take? Me ya rabata da su Josephine? Ina take lokacin da gwaggon zata dawo Nigeria? Waɗan nan sune tunanin da suka hana Lion runtsawa, ya rasa amsarsu, ya nutsar da brain nasa yana neman amsa cikin nutsuwa.......... NI KO NA CE AI KAI ƘWAƘWALWARKA DA BASIRARKA TA GADO CE, KA GAKI BASIRA BA KARYA, DOLE MA KA BANKAƊO GASKIYA IDAN KA SAKA KANKA, BA ABIN DA ZAMU CE MAKA FACE ALL THE BEST OUR LION!!.

Hakika kuma ya shiga damuwa na rashin Rimsha a kusa da shi, shi ne ma yasa tunanin da yake na neman amsar ta kasa gudu, ya kasa samun amsa da wuri, saboda rashin Meesha a kusa da shi babbbar barazana ce ga nutsuwarsa, hankalinsa ya rabu kaso uku, kaso biyu yana kan tunanin Meesha, É—aya kuma tunanin su Josephine, da Rimsha na kusa, wata kila a daren zai iya bankaÉ—o menene gaskiya, dan ya yi alkawarin bama zai tambayi daddynsa ba, saboda yana ganin kamar daddyn ba zai gaya mashi gaskiya ba, ya ce da kansa zai bankaÉ—o komai da komai.

AFTER SOME HOURS.

Da misalin karfe 9 na safe, shirye cikin wando jeans mai matukar bala'in kyau, black color, da polo t-shirt fara kal, Lion ya fito daga cikin bedroom nasa, hannunsa na ɗaure da TRIPLETS watch, still sarkan nan tana wuyarsa, ya ɗaure gashin kansa a bayan wuya, sai tashin daddaɗa kuma zazzafar kamshi yake yi, ya yi matuƙar kyau sosai, sai dai da kallo ɗaya zaka yi mashi, kasan bai sami damar yin barci daren jiya ba, dan idanunsa sun yi wani kal da su, tamkar wanda bashi da lafiya, fuskarsa ta yi wani fayau da shi.

Bedroom na daddyn Rimsha in da gwaggo take ya nufa. Kasa kasa tamkar bai yi magana ba ya yi sallama, tare da shiga ciki. Areef na zaune a bakin bed nata, ita kuma gwaggon tana zaune a saman bedside drawer suna zuba hira, shi kuma Aseef yana can yana zuba barci, bai tashi ba, dan daren jiya bai yi barci sosai ba.

A tare gwaggon da Areef É—in suka amsa mashi sallamarsa, karisowa cikin É—akin ya yi, yana taku cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, tamkar baya son taka kasa, da alama jikinsa duk a mace yake. Gefen Areef ya zo ya zauna yana tambayar gwaggo ya ta kwana?.

Sai murmushi take yi ta amsa mashi da lafiya lou ta kwana, Areef ne ya fara ɗaga mashi gaisuwa, a takaice ya amsa da lafiya tare da miƙewa ya ce da gwaggon yana zuwa, zai je unguwa.

"A'a zauna ina son yin magana da kai!". Okey ya amsa mata tare da gyara zama. Shi kuma Areef mikewa ya yi yana faÉ—in "Momma bari na je na É—auko matata, dan ba iya jurewa zan yi ba". Ya kai karshen maganar tare da wucewa da sauri. Kafin ta yi wani magana ma ya fice abinsa.

Dawo da kallonta a kan Lion É—in ta yi tare da fara magana a nutse. "Ina Muhammad, Sudais da kuma A'isha suke?". Wato su Uncle Herry take nufi kenan.

Shiru ya É—an yi kafin ya ce "Just call them Herry, Josephine, and Tyson, because all of them are Kristen now, ba yanda kike tunani bane".

Zaro idanuwanta waje sosai ta yi, cike da mamaki ta ce "Harda Josephine É—in?". Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya sake yin magana ba.

Shiru ta yi tana al'ajabin wannan al'amari, katse mata shirun ya yi da cewa "Momma forget about them, saboda babu mai gaskiya a cikinsu, ko kin tanbayesu, karya za su yi maki, kamar yanda suka yi mana, dukkansu bakinsu É—aya, so forget about them, I will do something about da case, now abin da nake so da ke, kada ma ki sake yin maganar, kada kuma ki sake tambayar kowa komai a kan labarin baya, ki rufe babin kawai!".

Tabbas ta sha jinin jikinta na jin abin da É—an nata ya faÉ—a, ta kuma sha ruwan mamakin yanda aka yi gabaÉ—aya su Dr William ya zama bakinsu a haÉ—e, ya aka yi Josephine mace mai hankali ta biye masu? Wai menene yake faruwa ne?.....

"Momma zan iya tafiya?". Ya faÉ—a cikin sanyin murya.

"Ina zaka je?".

Kai tsaye ya bata amsar gidan uncle zai je, kamar zata tambaye shi wani uncle É—in daga ciki, sai kuma ta fasa, dan ta lura baya son yawan magana, hannu ta kai ta shafi kansa tare da fara kwararo mashi ruwan albarka da adduo'in masu ratsa jikin duk wani mumini.

Wani abin sai uwa, babu wanda ya taɓa yi mashi makamancin hakan, hakan tasa ya ji wani mugun sanyi tana ratsa zuciyarsa, Allah sarki, wata kila da ace gwaggo ta rayuwa da su, da ba zai yi zafin zuciya har haka ba, da ko ma yaya ne zai rage wasu abubuwa, uwa, uwa, uwa, haka Allah ya kirata sau uku kafin ya kira uba, Allah ka karawa iyayenmu lafiya da nisan kwana, waɗan da suka rigamu gidan gaskiya kuma, Allah ya jikansu da Rahman, ya kai haske cikin kabarinsu, ya sadasu da manzon rahma.

Miƙewa ya yi ya kara mastowa kusa da ita sosai, a saman cinyarta ya kwantar da kansa, a can cikin zuciyarsa kuma, yana jin tamkar ya haɗiyeta, saboda so da kauna. Ita kuwa, ta cigaba da kwararo mashi ruwan addu'a ba kama hannun yaro, tana yi tana shafa lallausan gashin kansa, ya yi shiru yana sauraronta, abin gwanin birgewa, kowa ya gansu a haka, sai ya matsa kwallar farinciki, haka ta yi wa Areef ma da ya shigo ɗazun, dan shi tun karfe 6 yana wajenta, sai hira suke yi har lokacin da Lion ɗin ya shigo.

Sai da ta kai karshen addu'ar ne ya É—ago kansa tare da kai É—an bakinsa saitin kumatunta, sumbata ya manna mata a wajen yana faÉ—in "I really more appreciate and happy da ya kasance kece mahaifiyarmu, i love you so much my momma". Ya kai karshen maganar tare da sake manna mata sumbata a kumatun nata.

Shafa lallausan sajensa ta yi, tare da manna mashi sumbata a goshin tana faÉ—in "Na fika farincikin kasancewarku Æ´aÆ´ana, ina alfahari da ku, je ka wajen uncles É—in naka ka dawo, idan ka dawo, sai ka gaya mani aikin me kuke yi? Akwai wanda ya gaje mu a karatu ne a cikinku? Ko dai babu Dr a cikinku?".

Jinjina mata kai ya yi tare da miƙewa ya nufi kofar fita ba tare da ya sake cewa komai ba. Da kallo ta bishi tare da fatan alkhairi har ya fice. Yana fita Mark ya shigo mata da abinci, dan Areef ya gaya mashi ya kawo mata abinci kafin su dawo, sai su ci a tare gabaɗaya.

A can gidan daddyn Rimsha kuwa. Sai misalin karfe 8:30 daddy ya fito cikin shirin kananan kaya, waje gabaÉ—aya ya fita, restaurant ya wuce, abinci ya sawo masu ya dawo. Kafin ya dawo mum ta jera plates da komai a saman table, tana zaune tana jiransa.

Ko da ya dawo, saman table É—in ya wuce yana faÉ—in su Rimsha basu tashi daga barci bane? E ta amsa mashi da shi. Jinjina kai ya yi kafin ya ce "Okey ki kyalesu duk time da suka tashi, sai su zo su ci nasu breakfast É—in". Okey ta amsa mashi da shi.

Wani irin daddaɗar kamshi perfume ne ya daki hancinsu, a tare suka ɗago kai dan ganin wanene. Jehan ce take saukowa daga saman bene, ta shirya cikin ɗaya daga cikin kayan da ta samu a cikin walldrop na bedroom nata, doguwar riga ce mai kama da baya, blue color, kaya sun yi mata matuƙar kyau, abinku da farar mace, ta haɗu da blue color, ai kunsan dole ta haska. Ta yafo gyalen kayan a kanta, light make up ne a fuskarta, sai lips gloss da ta sanya a kyawawan lausasan kananan lips nata, duk wanda ya ganta, sai ya sake waigawa ya kalleta, saboda ta fita ta yi kyau over.

Kusa da su daddy ta zo ta tsaya tare da É—aga masu gaisuwa. Cikin tsantsar so da kauna suka amsa mata gaisuwar tare da tambayarta irin wannan uban kyau haka waye ta yi wa kwalliya.

A takaice ta ce "Daddy zan je naga gwaggona, ba zan iya zama ba tare da ita ba!" Ta kai karshen maganar tana yamutse fuska.
Chapter 21 · 0% Book details