← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 168

Sashe 162

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

E54

"Amma akwai waya a wajen ai? What I mean here is zamu iya samunku a waya ko?".

Jinjina mashi kai ya yi alamar e ba tare da ya yi magana ba.

"Okey tom Allah ya tsare hanya, ka dai kula mana da our Meeshar mu, dan naga kamar ba ita kaÉ—ai ba ce".

Nan ma jinjina mashi kai ya yi ba tare da ya ce komai ba.

Juyawa Sir Safwan ɗin ya yi ya fice daga cikin ɗakin, shi kuma Lion ya hau shiri na duk abin da zasu buƙata.

Ta kofar sirri wanda yake ta bayan ya fice, gwaggo and Dr William kawai ya sanarwa da ga in da za su je sai sir Safwan É—in.

Addu'a sosai iyayen nasa suka yi mashi tare da sanya mashi albarka, sannan suka ce ya kuka masu da Rimsha sosai. Amin ya rinƙa amsawa da shi kafin ya sa kai ya wuce abinsa.

Iya waÉ—an nan sojoji daya ware ne kawai suka bisa, bayan ya fita ta baya É—auke da Rimshar tasa dake barci, sai sojojin suka zago suka same shi, da motoci biyu suka tafi.

Sun yi tafiya mai ɗan nisa kafin su isa baƙin wata dam, already an shirya masu jirgin ruwa ɗan ma dai'daici, yana zuwa kawai suka kama hanyar tafiya.

GabaÉ—aya tsallake arear su suka yi, suka nufi É—ayar tsagin, tamkar yadda Rimshar take damunsa tana son rayuwa a irin wannan waje, haka ya kaita yau, a bakin ruwan su Mark suka yi aikin haÉ—a masu irin wannan É—akin da take magana a kai É—in.

Da yake ya san in zasu je, sai ya tanaji komai, harta electric katifa dake aiki da wuta, kuma yana aiki da Power bank, to haka su Mark suka sha aikin shirya waÉ—an nan abubuwa, jirgin ruwansu kuma suka baro shi a can jefe.

Sai zuba barci Rimshar take yi, bata san me yake faruwa ba, sai dai ta farka taga surprise.

Baya su Mark sun kammala aikin haÉ—a masu komai, É—auko Rimshar ya yi daga cikin jirgin ruwan ya kawota cikin É—akin, suna da komai a cikin jirgin ruwan, har da katafaren bed, amma dan ya cikawa Rimshar mafarkinta, sai yasa aka yi mata irin wannan É—akin da take so a rayuwarta, suka rufo jirgin ruwan nasu kuma.

Kwantar da ita ya yi a saman electric bed É—in nasu, sannan yasa su Mark su kawo masu trolleynsu. Mark kam mamaki ne kamar zai kashe shi, yarasa dalilin da yasa Lion ya zo nan wajen, me ya kawo shi? Ga shi ba halin tambaya.

Bayan sun kawo mashi trolleyn ya karɓa ya koma cikin ɗakin, su kuma suka tsaitsaya a gaba da bayan ɗakin dan bashi tsaro.

Kayan jikinta ya cire mata ya sanya mata pajama mara nauyi, dan ya ga duk da sanyin da yake a ƙasar tasu ita zufa take haɗawa, hakan yasa ya canza mata kaya izuwa shara shara mara nauyi.

Daya kammala sai ya ɗauki kayan da zai buƙata ya koma cikin jirgin ruwansu dan ya yi wanka ya shirya, ya rufota a cikin ɗakin. Tyrone ne ya bi bayansa dan ya bashi tsaro a wajen jirgin ruwan, ita kuma Rimsha su Mark suka cigaba da tsaron ɗakin da take.

Bayan ya yi wanka ya shirya a cikin three cuter, bai sanya riga a jikinsa ba, saboda yanayin weather wajen da akwai É—an zafi zafi, kasar tasu akwai sanyi sosai, ga shi nan bakin ruwa suke, sai dai kuma wani ikon Allah wajen da É—umi sosai kamar ba bakin ruwa ba.

A dai'dai bakin ruwan ya zo ya zauna bayan su Mark sun kawo mashi wata tsadaddiyar kujera daga cikin jirgin, Mark dai har yanzu mamakin zuwansu wannan waje yake yi, ya baro Anayarsa da baby's nasa, sai kewarsu yake yi Lion ya wani kawosu bakin ruwa ya ajiye, kamar ya yi kuka haka yake ji, to amma ya zasu yi? Dole ne su bi umarni.

Aikin latsa wayarsa ya fara yi yana tunanin yakamata ace Rimsha ta farka izuwa yanzu.

Bai kammala dawowa daga cikin duniyar tunanin da ya afka ba kamar daga sama ya ji ihunta.

A dubu ɗari su Mark ɗin suka juyar da kallonsu izuwa wajen ɗakin da take a ciki ɗin, shi ma Lion ɗin miƙewa ya yi tsaye cikin nutsuwa, dan yasan ba komai yasa ta yi ihu ba face farkawa da ta yi ta ganta a bakon wajen da bata taɓa tunanin zata ziyarci wannan waje ba, hakan yasa ta kurma wannan ihu.

Yana ƙoƙarin nufar ɗakin sai gata ta fito da gudu.

Dakatawa ya yi daga tafiyar da yake yi, zuba mata waÉ—an nan dara daran idanuwan nasa ya yi.

Ita ma dakatawa ta yi daga tunkarosa da gudun da take yi, ta tsaya cak tare da tsare shi da idanu babu ko kyaftawa.

Su kuwa su Mark, ai a dubu suka juya, dan kada su ganta, sai suka juya suka ba su baya tare da sunkuyar da kansu kasa.

Kasa karisowa in da yake ta yi, ta yi mutuwar tsaye ne a wajen.

Ganin bata da niyar karisowa gare shi ne yasa shi ya tako cikin nutsuwa, kafafunsa suna sanye cikin wasu shegun tsadaddun bedroom slippers, ga su farare tas masu kyan gaske.

Yana isa gabanta ya kai hannu ya kyafta mata yatsunsa a dai'dai wajen idanuwanta.

Ina ko kyaftawa bata iya yi ba, tamkar wadda ta yi samar tsaye.

"Meesha are you okey?".

Ya faÉ—a in a low voice sosai.

Kasa amsa mashi maganar ta yi, ta kafe idanuwanta a kansa kawai tana kallonsa.

Ba komai yasa ta yi wannan sumar tsaye ba face surar jikinsa, tun da suke bata taɓa ganinsa babu riga ba sai yau, bata taɓa kallon waɗan nan ɓul ɓul ɗin kyawawan breast ɗin nasa ba sai yau, hakan yasa ta yi sumar tsaye, taga abin da ya haura sheƙarunta.

Shi kuma bawan Allah sam bai ma san dalilin da yasa ta yi mashi sumar tsaye ba, yaga dai sai kallonshi take yi babu ko kyaftawa. Hakan yasa ya kai hannu ya É—auketa cancak suka koma saman kujerar da yake zaune É—in.

Ya zauna da ita a manne ajikinsa, sannan ya kai hannu ya É—ebo ruwa daga cikin tekun ya É—an yarfa mata a fuska.

Dogon numfashi ta ja tare da sauke a hankali, sannan ta fara aikin kyafta idanuwanta domin ta tabbatarwa da kanta ba mafarki take yi bada.

Kyakkyawar dogon hancinta ya ja kafin ya ce. "Lafiyarki kuwa my Meesha?".

Da sauri ta dawo da kallonta a saman face nasa, sai kuma ta fara sauko da idanuwanta izuwa saman Lion chest É—in nasa domin ta tabbatar da abin da ta gani É—azun gaskiya ce ko mafarki ne.

Ganin gaskiya ce yasa ta fara bin damatsan hannunsa da kallo, duk mamaki ya cika mata rai, anya yah Saif É—inta ne kuwa? Ta tambayi kanta, dan taga kyakkyawar kakkarfar surar jikin nan nasa ya gigitata.

Shi kuwa mamaki ta bashi, ya rasa ma me zai ce mata, ga su Mark kuma can a kame sun juya masu baya, ba halin su juyo bayin Allah.

Ta ɗan ɗauki lokaci kafin ta warware ta dawo dai'dai, sai kuma me? Ai sai ta hau yin murna na wuce misali, yau gata a wajen mafarkinta, bakin ruwa tare da mutumin da take mafarkinsa tun tana karama, mutumin da ta fi so sama da komai nata, kuma ya zo mata a sak irin mafarkin nata, ga shi babu riga, ita kuma da ƙananan kaya, abin ya yi mata daɗin da ba zai taɓa yiwuwa ta manta da shi ba.

Rungumarsa ta yi cikin tsananin farinciki tana mai manna mashi sumbata ta ko'ina a face nasa saboda jin daÉ—i da murna.

Shi kuwa ya yi shiru ya tsareta da idanun yana ta kallon kyakkyawar fuskar nan tata mai É—auke da kayatatcen murmushi.

Sun É—auki É—an lokaci a wajen da a kallah ya kai awa biyu suna zuba love nasu, kafin ta ce

"Noorish ka kamo mun kifi, ina son in ci gasasshen kifi".

ÆŠan zaro mata idanun ya yi. "Meesha me zaki yi da kifin cikin tekun nan? Idan kifi kike so ai sai Mark ya je ya kawo maki fresh ko?".

Kukan shagwaɓa ta saka mashi tana faɗin. "Ni bana son wani fresh, na cikin tekun nan nake so".

Shafa lallausan kumatunta ya yi kafin ya ce. "To ya isa haka rigimammiyata, yadda kikeso haka za'ayi, bari su Mark su kama maki".

Wani sabon kukan ta saka mashi tana faÉ—in. "Wai Noorish cikin Mark ne a jikina ko naka? Babyna ya ce shi wanda daddynsa ya kamo yake son ci, dan haka kai zaka kamo mun nikam, idan ba haka ba sai dai babynka ya hakura da ci, bana son nasu Mark".

Tana magana tana kuka, har da wani É—an guntun hawaye na iyashege.

ÆŠan dafe kansa ya yi yana faÉ—in. "Wannan baby da alama ya fi uwarsa rigima, to tashi mun a jikina bari na je na kamo maki".

Make mashi kafaÉ—a ta yi tana faÉ—in. "A'a ni dai sai dai ka goyani mu kama a tare".

"To tashi bari na miƙe sai ki hau bayan nawa ko?"
Ya bata amsa a takaice.

Da sauri ta miƙe daga jikin nasa, miƙewa tsaye ya yi tare da ɗan duƙa mata kaɗan ta yi tsalle ta haye bayansa tana dariya.
Chapter 162 · 0% Book details