Sashe 56
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Areef kuwa magana ya fara yi da Dr Salman a kan ko ya san wani abin dangane da gidan nan. Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Na shafe shakaru sama da talatin da uku a nan, amma har yau ba zan iya ce maka ga takamaimen abin da suke yi ba bayan kashe mutane da ɗibar jini da wasu sassa na jikin ɗan adam, sannan har yau ban taɓa ganin gini na farko ko kuma na karshe na wannan gida ba, sai dai kuma, na san da akwai wata hanya da Duna ya taɓa gaya mani, ya ce ko bayan sun ɗauke shi, idan zan iya na bi wannan hanya zan tsira daga wannan gida, sai dai kuma hanyar tana da haɗari, sannan tana da nisa sosai, kuma a karshen hanyar da kawai kofa da zata fitar da kai waje gabaɗaya, bayan hanyar da su Rimsha suka fita, wannan ita ce hanya ta biyu ta sirri a cikin gidan, sannan ya ce mani idan har ina tafiya a kan wannan hanya, to kada na juya baya, komai zan ji na tafi kawai, abin da yasa ban fita ba, saboda komai ya kare mani, ina jin ko nafita bani da kowa a duniya, kuma ya ce hanyar tana da tsawo sosai, so ba zan iya doguwar tafiya ba, ni kaɗai ne kuma, dan a lokacin, sun ɗauki mai taimaka mani ɗin, wato Mustapha, shi ne mai taimakona dama, to sun rabani da shi, sun mayar da shi cikinsu, suna can suna ƙoƙarin juyar da shi izuwa nasu, a halin yanzu ma ina ga sun mayar da shi ɗaya daga cikinsu ɗin, wannan dalili yasa na ce gara na cigaba da zama a nan ɗin kawai har ranar da rai zata yi halinta".
Shiru Areef ɗin ya yi yana jinjina wannan al'amari na Dr Salman, abin gwanin ban tausayi, shekara ɗai ɗai har talatin da uku a cikin wannan bakin azzalumin gidan? Gaskiya Queen ta azabar da bawan Allah nan, ko da ace iya ajiye shi kawai ta yi, bata yi mashi komai ba, wlh masifar da yake gani wanda suke aikatawa kawai ya isa ya kashe shi idan da kwanansa ta kare, Allah sarki, da Allah ya ƙaddara kwanansa na gaba, shi ne har ya kawo iyanzu duk da irin masifu da yake gani, Allah ne kawai zai bi masu hakkinsu, dan kome aka yi wa Queen a yanzu, wlh ba'a biya ko mutun ɗaya abin da ta yi mashi ba, yanzu a kalla ba'a akasaraba wannan Daular Mutuwar ta haura shekaru hamsin da kafata, sai Allah ne kaɗai zai iya kiyaste rayukan da aka salwantar a cikinta, ya ilahi ya lillahi.
Rugujewar sauran É—akunan dake gefe da gefensu ne ya dawo da Areef É—in daga duniyar tunanin da ya afka, da mamaki ya É—ago kai yana bin É—akunan da kallo, sai rugujewa suke yi tamkar waÉ—an da ake jijjigewa. Anya lafiya kuwa? Areef É—in ya tambayi kansa. Aseef kuwa kara kankame Akila dake kankame da shi gam ya yi, saboda tsoro, ta tsorata ne da ganin yanda gine ginen suke jijjigowa da kansu, sai ruguzowa suke yi, tamkar katafila ce take watsi da su.
"Aseef let's go, saboda ina ganin gabaÉ—aya ruguje arean nan ake son yi, so tsayawarmu a nan babban haÉ—ari ne, ka kawo Heartbeat ta tafi da su baba ta hanyar da ya gaya mani yanzu, zamu cin masu a hanya idan mun gane a in da Lion yake". Cewar Areef kenan.
Kankameta ya kara yi yana faÉ—in "No Areef su baba É—in su je kawai, ita Heartbeat tana nan tare da ni". "Aseef ba da wasa nake yi ba, kada ka yi ka salwantarwa da yarinyar nan rayuwa, ka barta ta bisu". "Nima ai Areef bada wasa nake yi ba, babu in da zata je, muna tare da ita".
Dr Salman ne ya sa baki ta hanyar cewa "Jikana da ka bari mun yi abin da É—an uwanka ya ce, dan wannan gida ya wuci tunaninka".
"Baba ni fa ba zan rabu da Heartbeat ba, ai dama ta ce zata soni komai wuya komai daɗi, kuma idan ma aka bata zaɓi a kan mutuwa, to zata zaɓi mu mutu a tare, dan haka kunga ita already a shirye take da ta mutu a tare da ni, please kada ku dame mu, ko ba haka ba Heartbeat?". Tana daga kwance a saman kirjinsa ta amsa mashi da cewa "Haka ne, a tare zamu mutu".
Girgiza kai kawai Areef ya yi, waÉ—an nan sun yi nisa, sam ba zasu ji kira ba, idan ka biyewa Aseef sai ya sanyaka hawan ruwa ba na jini ba.
Tsananin jijjigar da gine ginen wajen suke yi ne yasa suka dawo cikin hayyacinsu, da sauri Aseef É—in ya riko hannunta tare da raba jikinsu, cikin hanzari ya nufi su Dr Salman É—in yana faÉ—in "Wayyo Areef menake ji da gani haka? Kada fa waÉ—an nan gine gine dukka su faÉ—o mana a kanmu, ya kamata mu gudu, dan ni dai gaskiya ban shirya mutuwa a yanzu ba, sai na sami magaji tukun nan........" Bai gama rufe baki ba gine ginen suka fara ruguzowa tamkar waÉ—an da karapila take jijjigewa.
Cikin hanzari da zafin nama suka yi maza suka fara ƙoƙarin barin wajen. Dr Salman ne ya nuna masu hanya, a in da suka bi ta wata kofa dake ta yamma. Suna tafiya da sauri sauri, gine ginen ɗakunan bayansu na rugujewa kamar ba lafiya ba.
Ganin Ayla zata basu matsala ne yasa Areef ya sauke jakar bayansa, a in da ya dawo da jakar ta gaba, sannan ya goya Aylar a bayansa, dan ba karya ta galabaita iya galabaita, ta sha bakar wahala, da kyar baiwar Allah take iya jan kafafunta, hakan kuma zai sanya har gine ginen su ruguzo a kansu ba tare da sun fita daga wajen ba, shi ne yasa Areef É—in ya goyata, shi ma Aseef goya Akila a bayansa ya yi.
Sun yi tafiya mai nisa kafin su cikaro da wani É—aki, Æ´an mata guda uku ne rufe a cikin É—akin, buÉ—e masu kofa Aseef ya yi, duk da basu san su ba, amma sun taimaka masu. Haka suka cigaba da tafiya, duk wani É—aki da zasu gani, in dai da akwai mutane a ciki, to sai sun buÉ—ewa mutanen, su ce su biyo bayansu, tun suna su kaÉ—an, har suka kai kusan su 40 a wannan tafiya tasu, har a lokacin kuma basu cinma wannan hanya da Dr Salman yake son nuna masu ba, wanda kuma ta nan ne kawai za su bi su fita.
A can gida kuma, abubuwa sai ƙoƙarin rikece masu yake yi, yau da wani irin azababben zazzaɓi Rimsha ta tashi, ga tsananin ciwon kai, tun safe take zuba barcin wahala, har misalin karfe 4, shi ma sai da gwaggo ta ga barcin ya yi yawa, sannan ne ta tasheta.
Tana tashinta sai kuma me? Wani sabon tashin hankali suka afka, dan kuwa Rimshar tana tashi ta fara tambayar gwaggon wacece ita? Babbar magana. Zaro idanu waje sosai gwaggon ta yi, idanuwan nata tamkar za su faÉ—i kasa, cike da mamaki a samar fuskanta ta ce "Rimsha ni yau kuma kike tambaya wacece ni?".
Wani irin harara ta watsawa gwaggon da waÉ—an nan dara daran fararen Sleeping eyes É—in nata, ta É—auki tsawon a kallah minti biyar kafin ta amsa mata da "E mana wacece ke? Kin wani zo ki zaunawa mutane a waje".
Shiru gwaggon ta yi, ta rasa me zata sake ce da Rimshar. A haka Brr Naurat ta shigo ta samesu. Da mamaki take tambayarsu lafiya suka yi wani cirko cirko da idanu haka.
Nisawa gwaggo ta yi tare da gyara zamanta, sannan ta ce "Mummy wai Rimsha ce take cewa bata sanni ba yau kuma".
Murmushi kaÉ—an Brr ta saki tana faÉ—in "To kin dai san halin masu ciki, wata kila yau kuma da irin halin da ta tashi kenan, ai sai ki rabu da ita ki kama wani abin ko? Idan lokacin da ta dawo dai'dai ya yi, sai ki zo ki yi mata maganar da dama zaki yi mata É—in". Ta kai karshen maganar tare da zama a gefen bed É—in.
Hakika dukkansu basu ɗauki zancen Rimsha na cewa da ta yi bata sannu ba da mahimmanci, gani suke yi dukka shirmene da kuma laulayin ciki, ita kuma ba wani shirme, har ga Allah da gaske take yi, bata sansu ba, gabaɗaya ƙwaƙwalwarta an ɗauke shi ne aka kifa shi, ta mance da komai na rayuwarta, da kuma kowa, ita kanta ma ta mance da ita wacece. Tashin sense!!.
Komawa ta yi ta kwanta tana wani irin ɓata rai tare da ɗaure fuska sosai. Daga gwaggon har Brr Naurat ɗin babu wanda ya sake kulata a cikin ɗakin, da haka barci ya sake yin awon gaba da ita, yau tun da ta yi sallar asuba, bata sake yin wani sallah ba, dan ita kanta bata san wacece ita ba bare ta san cewa ita musulmace ko Kristar, wannan shi ne tashin hankali, to meyasameta kuma? Wanene ya juyar mata da tunani? Meyasa aka yi mata hakan?. Ku kasance da Alkalamin FATEEMA ZAHRA MUSA, PRINCESS TEEMA, alkalamina ne kawai zai iya warware maku wannan cankwakiyar.
Hira Brr Naurat da gwaggo suka fara zubawa, ita kuma Rimsha ta mayar da barci. Baki É—auke da sallama Jehan ta shigo cikin É—akin.
Saman bed É—in ta haye tare da tada kai da laps na gwaggo, da kallo É—aya zaka yi mata kasan cewa tana cikin tsananin damuwa, har Æ´ar rama ta yi, ta yi wani fiki fiki da ita, tamkar ba Jehan D.P.O kuma jarumarmu ba.
Shafa kanta gwaggon ta fara yi tana faɗin "Babyn daddynta waye kuma ya taɓo mani ke?".
Tamkar jira take yi a yi mata tambaya, sai kawai ta sa kuka, hawaye wani na bin wani, Allah mai iko, yai Jehan ce take kuka da hawayenta? A lallai abu ya yi tsamari.
"Subhanallahi, Jehan lafiya kike kuka?". Cewar gwaggon. Brr Naurat ma dai abin da ta tambaya kenan, lafiya take kuka?.