Sashe 139
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin yadda take kukan yana taɓa mashi zuciya sosai ne yasa ya ɗauketa cak suka fito izuwa cikin bedroom ɗin. A saman bed nasu ya kwantar da ita yana ƙoƙarin komawa saman bedside drawer. A dubu ɗari ta kara ƙanƙame shi tana mai cigaba da kukan nata, jikinta sai wani irin kerma na tsananin tsoro yake yi, duk ta yi wani iri da ita lokaci guda, ta fita a hayyacinta.
Dole ba dan yaso ba ya zauna a saman bed É—in tare da riketa da kyau, shi ba addu'a ya iya ba bare ya tofa mata, shi fa ko addu'ar da pastor yake yi masu ma bai wani rike ba, da yake tun ainahinsa musul ne hakan yasa ma duk abin da pastor zai yi bata shiga kansa, a lokacin yana dai zuwa church É—in ne saboda Lion yana zuwa, bacin haka da wlh ba zai je ba, ba wani son addinin yake yi ba dama, bawan Allah ashe ma shi musulmi ne bai sani ba, kai su Anderson basu kyauta ba, duk kuma Jacob Roshan shi ne silar komai, ya cuci Dr William da familynsa sosai.
Haka ya mannata da jikinsa kawai yana ganin yadda take ta kerman tsoro, ga shi ta kasa yi mashi magana, duk ya shiga ruɗu, yanzu zargin da yake yi a cikin zuciyarsa na cewa tana da wata matsala a ƙwaƙwalwarta ya tabbatarwa da kansa hakan, amma bai nuna mata a fili ba, ya dai riketa kawai yana jiran yaga karshen haukar tata a ina zai tsaya.
A can dining room kuwa, duk Akila ta damu, so take yi kawai taga Heartbeat nata, cin abincin kawai take yi, hankalinta da nutsuwarta yana can wajen tinanin Heartbeat nata.
Duk cikin dining room É—in babu wanda ya lura da ita sai gwaggo, da yake ta je wajen Aseef É—in É—azun ta san me matsalarsu, sai ta ce "Akila tashi ki je ki yi wanka ki je ku yi breakfast É—in a tare da autana, nasan da cewa bai yi breakfast É—in ba, dan ya ce shi dole dole dake zai ci abinci".
Kasa da kai ta yi, dan ita tana da kunya sosai, jiki ba kwari ta miƙe ta bar wajen. Tagumi sir Arvin ya buga yana kallonsu, har ta fice daga room ɗin.
Daddyn Rimsha ne ya ce "Arvin lafiya kuwa?".
Nisawa ya yi kafin ya ce "Uncle wai dukka yanzu sun yi aure sun barni? Gaskiya sun yi mun wayo, kuma ba zan yarda ba".
"To waye ya hanaka yin aure dama my son?". Cewar gwaggo.
"Momma ni da ban da girlfriend ina ni ina aure? Ai sai kana da ita, amma dai koma menene QUADRUPLE na sun saka mun sha'awar son yin auren, dukkansu sai su É—auki matansu su wuce dasu cikin bedroom su barni tare da Pinky? To ita ma Pinky aure zamu yi mata da wuri, na koyi darusa sosai zuwana nan, dan haka aurar da Pinky da wuri zamu yi muma Daddy".
"Haba Arvin Pinky ai yarinya ce sosai". Cewar Dr William.
"Daddy matar Saif fa da kaɗan tafi Pinky, dukkansu mate ne, kuma ga shi ta zauna zaman aure da mijinta lafiya, dan haka ita ma Pinky shagwaɓarta ya isheni a gidan nan, na gaji".
"Babu ruwanka da Pinky, kai dai ka nemo mata mai hankali da nutsuwa, ida muka yaba da hankalinta sai mu yi maku aure, Pinky tana nan tare da mu har sai idan ita ta buƙaci yin aure, kawai zaka wani sauke haushin gaurancinka a kanta, a kanka take zaune?". Cewar daddyn Rimsha.
Ƙasa kaɗan ya yi da kansa kafin ya ce "Kai uncle, yanzu kuma ni za'a sakawa ido kenan?".
"E mana da kai da Alex gaku manya daku, Alex fa ya kai 36 yanzu, amma babu mata, bashi ma da niyar yin aure, dan ko maganar bayayi, baku tunanin gaba, to ni dai ba zan zuba muku ido ba, ba zan barku ku zauna a haka ba, maza ku nemo mata mu san abin yi".
Alex ɗin ne ya karɓi zancen da cewa "Kai yaya wato yanzu kai ma ido ka saka mun ko? To daga yau na dai'na zuwa cin abinci dining room ɗin nan, dan ido zaku saka mun, ni ina naga wata girlfriend da har zan yi aure? Nifa seriously ban taɓa tsayuwa na kalli wata yarinya da ido bama, idan kaga na kalli mace to by mistake ne, kunga yanzu babu in da zan samo mata kuma".
"Yauwa uncle Alex, tell them, we don't have a girlfriend". Cewar Arvin
"Ai su ma su Saif É—in da kuke gani sai da aka kai ruwa rana suka yi aure, barema shi Saif, ina ga duk kin matanku ko kwatansa baku kai ba, ni tun da Saif ya yi aure to duk wanda yake cewa ba zai yi aure ba a mashirmaci na É—aukeshi, dan daga kan Saif an rufe kofa in dai a kan tsanar mata ne, amma yanzu ga shi nan tare da matarsa cikin farinciki, duk ya mance da abubuwan da ya yi a baya, har poison Æ´an mata sun sha a kansa, ku tambayi Areef zai gaya maku, ku ai kun san Saif a lokacin da ya zama Saif ne, baku san shi a time da yake Romeo or Lion ba!". Cewar daddyn Rimsha, dan shi sarai yasan wanenen Lion.
Ita dai gwaggo da ido kawai take binsu da shi, ga idon nata kamar na Jehan da daddynta, dara dara da su, kai familyn Dr Salman akwai dara daran ido kam ba karya. Sai kallonsu take yi, amma hankalinta yana a kan tunanin Jehan, tunaninta kawai take yi, tana so ne ta gama cin abincin nan ta je ta sake dubata.
"Uncle do you know something?". Cewar sir Arvin.
Girgiza kai daddyn ya yi alamar a'a bai sani ba.
"Yanzu kawai ka nemo mana matan da zamu aure, ba shikenan ba?".
Kallon Alex daddyn ya yi yana jiran ya ji me zai ce shi kuma. "Yeah I greed, ka nemo mana matan kawai masu hankali, dan mukam bamu da ƴan mata, bamu ma taɓa yinsu ba, yanzu kaga bamu san a ina zamu nemo mai kirki ba, amma kai sai ka nemo mana".
Ajiyar zuciya daddyn ya sauke kafin ya ce "Sai na koma Nigeria, dan ƴan Nigeria dukkanku zaku aura, ban yarda da ku sake auran masu jajayen kunnuwar nan ba, gara mana.........." Ƙasa karisa maganar ya yi saboda wani kallo da Brr Naurat ta wurga mashi, wato bai yarda da masu jajayen kunnuwa ba, lallaima daddyn Rimsha yana tsakiyarsu kuma yana ƙoƙarin kauce hanya.
"Nawazuddeen ni kuma yaya zaka yi da ni kenan? Nima baka yarda dani ba ko?". Cewar Brr Naurat É—in.
Ƙasa ya yi da kai yana ɗan shafa kan nasa, gwaggo kam me zata yi idan ba dariya ba, shi ma Alex dariya abin ya bashi, da alama daddyn Rimsha ya manta asalinsa ne yasa yake nema kauce hanyarnan, da alama ya manta da suna wajen, da alama ya manta fa a kasarsu kuma cikinsu yake, dan gasu Dr William, Jay, da kuma John duk suna a wajen, yana cikinsu tsundum yake sakin layin.
Dr Salman ya ce "Barshi ba laifinsa bane, Æ´ar Maiduguri ce ta kiÉ—ima shi, shiyasa yake ganin babu kamarsu, amma ni ai nasan babu kamar masu jajayen kunnuwar, ga kuma shaida nan kun gani".
Tamkar mummyn Rimsha ta nutse cikin kasa, haka ta ji sabida kunya, daddyn Rimsha ya ja mata.
Alex ne ya ce "Gaskiya bro ni ma Æ´ar Maidugurin nan zan aura, sabida daga jin yadda ka canza akala to fa ba'a banza ba".
Daure fuska gwaggo ta yi tana faÉ—in. "Kai duk ku tashi ku bamu waje tun da kun gama breakfast É—in, ni zaku sakawa É—an uwa a gaba? To wlh baku isa ba, ku tashi ku wuce".
Ba dan sun so ba Alex da sir Arvin suka miƙe suka bar wajen, sannan Jay da John ma suka rufa masu baya. Miƙewa ita ma gwaggon ta yi tana faɗin
"Bari na duba jikin Jehan".
ÆŠan zaro idanu daddynta ya yi yana faÉ—in. "Meyasameta?". Ya yi maganar cikin murya mai kama da wanda ya shiga damuwa.
Shap gwaggon ta mance da cewa basu san komai ba, da ba zata yi maganar ba, abin ya yi mata ne kamar sun san meyafaru shiyasa ta yi magana.
"Ba wani abin bane, É—an ciwon kai ne". Ta basu amsa.
Yadda ta yi maganar yasa Brr Naurat ta zargi cewa ba gaskiya ta faÉ—a masu ba, bata saba yin karya ba, shiyasa da ta yi ma maganar bata zauna ba.
"Jeki abinki A'isha kai kuma Nawazuddeen ina ruwanka ita da Æ´arta? Ba ra'inonta bace?". Cewar Brr Naurat.
Shiru ya yi yana tunanin meyasami Jehan? Yana kaunarta ne fiye da kansa, sabida idan baku manta ba ya binne yara dayawa kafin ita, dole ya sota sosai fiye da tunanin mai tunani, dan har ya fidda rai da samun yara Allah ya kawo mashi ita.
Wucewa gwaggo ta yi ta nufi part É—in Areef. Tun daga parlourn take jiyo muryar Jehan É—in tana kuka, abin ya yi mugun bata mamaki, saboda bata yi zaton zata farko a yanzu ba, to amma meya sakata kuka?. Da sauri ta karisa cikin bedroom É—in.
Kwance Jehan ɗin take kamar yadda ta kwantar da ita tun farko, ga Areef kuma ya duka a saman gwiwowinsa ya riko hannunta yana bata hakuri, ta datse idanuwanta gam wai bata son ganinsa, shi kuma ya ce ba zai tafi ba har sai ta hakura ta yafe mashi, ya tuba ba zai sake ba. Sam taki kula shi, ba dan wani azababben tsoronsa da take ji bama kuma ba zata iya tashi ba ai da babu abin da zai hana bata gudu ta bar mashi dakin ba, mugun tsoronsa ne yanzu yake cike fal a ranta, da ta buɗe idanu ta gansa a ɗakin sai da ta ji wani azababben jiri tare da ciwon kai saboda tsoronsa, tsoron nasa ne ma yasa ta kasa yi mashi magana, ta dai datse idanu bata son ganinsa, amma tana tsoron yi mashi magana, karo na farko a rayuwarta da tsoronta ya fito fili ɓaro ɓaro, kana ganin face nata kasan a tsananin tsorace take.