← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 168

Sashe 27

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Areef, Imran, da kuma Irfan ne suka nufi Kanon tare da tallafawan daddyn Jelly da ya basu number wayar babban yaronsa, wato engr Muhammad Imam, a kan idan sun je Kanon su nemesa, zai yi masu karin bayani a kan wanene Baban Muneer, zai ma kaisu har companynsa. Da farko daddyn Jelly ya ce da wuya idan baban Muneer É—in ne ya É—auketa, dan shi a Kano yake, sai da Areef ya gaya mashi cewa, ai zai iya turowa a É—auko mashi ita, dan wlh mai son abinka, ya fi ka sanin hanyar kula da shi, dan ya É—auka, shi ne sai hankalinsa ya yarda a kan hakan.

Da kyar Abba ya lallaɓa matan suka koma cikin palo, su kuma mazan, wato su Abbi, sai suka fita gari nemanta, ko Allah zai sanya a ganta, daga nan su kai report station da sauransu........NIMA PRINCESS TEEMA INA TAYAKU DA ADDU'AR ALLAH YASA A GANTA ƊIN, AMMA ƁATAR AYLA BA KARAMIN ABU BANE, DAN DOLE DAI HANNU NE YA ƊAUKETA, SABODA BAIWAR ALLAH NAN KO HARABAR GIDA BATA FITA, TO WAYE YA ƊAUKETA? ALLAH SARKI, GA KARAMIN CIKI, GA UBAN LAULAYI.

A ɓangaren Lion kuwa. Bayan sun kammala cin abinci, Rimsha ta kwash kayan abincin ta fitar, ta gyara wajen tsab, sai ta dawo ta haye saman bed nasa, a kusa da shi ta kwanta, tare da lumshe idanu, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita, saboda daren jiya bata samu damar runtsawa ba.

Shi kuma Lion, yana can yana aikin latsa laptop nasa, Tyrone ya É—auko mashi wannan memory da camera ta naÉ—i komai, sai dai, da kyar aka samu memoryn, dan ma dai babu nai shiga gidan nan, kuma dama ana ajiye storyn camera irin haka sosai, so suna nan a É—akin computers É—in, an dai ci kwakwa ne kafin a nemosu.

Miƙewa Lion ɗin ya yi tare da ficewa daga bedroom ɗin. Ɗakin gwaggo ya koma, tambayarta ya je ya yi a kan zata iya tuna ranar da abin ya faru a tsakaninta da Dr William, ma'ana ranar da ta kai mashi TRIPLETS ɗin gidansa. Cikin sauri ta ce ai bazata taɓa manta wannan rana ba, biyu ga watan biyu ne.

Jinjina mata ya yi da ƙoƙarinta na ruke komai na tsawon shekaru a kanta, sannan ya juya ya koma bedroom nasa. Cewa Tyrone ɗin ya yi da ya saka memoryn a laptop, ya duba mashi videon biyu ga watan biyu a shekaru 32 baya.

Okey ya amsa mashi tare da fara aikin babu kama hannun yaro. Cikin ƙanƙanin lokaci ya samo video ya turowa da Lion ɗin.

A hanzarce ya buÉ—e video, dan dama jira kawai yake yi. Shiru ya yi ya zubawa video idanu yana ganin komai kamar a gaske a gabansa ake yin komai. Tun daga shigowar gwaggon gida, tun wayewar garin ranar, har shigowar gwaggon da TRIPLETS É—in, yanda ta faÉ—a, ga yanda ta kwantar da su a saman sofa, komai da komai yana gani kamar a zahiri.

Dai'dai lokacin da Dr William ya bugawa jariri ɗaya santa, sai da Lion ɗin ya datse idanunsa, saboda har cikin ransa ya ji saukar wannan sandar, babu irin azabar kalolin kisa da Lion bai gani ba, amma ba zai iya jure gani ko ɗan ƙaramin bulala ne ya taɓa TRIPLETS nasa ba, shiyasa lokacin da ya ga Dr ya kwalawa ɗaya ɗaga cikinsu sandar, sai da zuciyarsa ta amsa, ji ya yi tamkar shi aka bugawa.

A hankali ya waro idanunsa ya cigaba da kallon video, yana ganin gwaggo ta fice waje da gudu, shi kuma Dr William ya yi kan yaran da gudu bayan ya jefar da sandar, ita ma Josephine da gudu ta kariso cikin palon.

ÆŠaukar jaririn Dr ya yi, da gudun gaske ya nufi waje da shi, sai zubar da jini kansa yake yi, kai tsaye asibiti ya nufa shi da Uncle Herry, ita kuma Josephine, kan sauran jarirai biyun ta nufa, da sauri ta É—auko É—aya ta ruke a hannunta tana shafa É—ayan da yake kwance a saman sofar da hannunta, dan ta tabbatar da lafiyarsu.

Sai ruwan hawaye take yi. Kamar daga sama wani mutun ya faÉ—o cikin palon, wani dogo da shi, yana sanye da bakaken kaya, long cut ce baka a jikinsa, daga ta cikin kuma T-shirt ce mai karamar hannu, ita ma baka, ya sanya wata hula mai gashi a kansa, fuskansa na a sanye da black mask, hannayensa dukka biyu suna sanye a cikin hands gloves bakake kirin suma, kafarsa na'a sanye cikin Booth baka kirin, baka iya ganin komai na daga jikin mutumin nan fa ce idanunsa da suke ashe color masu tsananin haske kamar glass, tamkar ba na mutun ba.

Hannunsa na ruke da jariri sabon haihuwa cikin towel baka kirin, ga jaririn fari kal da shi, kasancewar yana jikin bakar towel ga shi fari kal, sai ya haska sosai.

Kai tsaye Josephine mutumin ya nufa, yana zuwa ya miƙa mata jaririn da yake a hannunsa, karɓa ta yi, ita kuma sai ta miƙa mashi ainahin cikon TRIPLETS da yake a hannunta, tana yi tana shafa kan baby ɗaya da yake kwance. Juyawa mutumin ya yi da ainahin cikon TRIPLETS ɗin a hannunsa, ta kofar da ya shigo, ta nan ya fita, ita kuma Josephine, sai ta cirewa jaririn da mutumin ya kawo waɗan nan bakaken kayan da suke jikinsa, sai ta ɗauko wani towel fari daga cikin ɗaki ta rufe shi da shi, sannan ta kwashi bakaken kayan ta nufi waje da su.

Jim kaÉ—an ta dawo, kusa da jariran ta dawo ta zauna tana kare masu kallo, babu wanda zai iya banbanta su, babu wanda zai iya cewa su ba TRIPLETS bane, wancan É—in ya saje da É—ayan.

Wani irin datse idanuwansa gam Lion ya yi da karfin gaske, tamkar zai fashe idanun nasu, karo na farko a rayuwarsa da ya fara danasanin gani abu, da ya sani, da bai kalli video nan ba, dan wlh ba zai taɓa yarda ace ɗaya daga cikinsu ba cikon TRIPLETS nasa bane, da bai kalla ba, da ya rufe maganar sun tafi a haka har su mutu, ba zai iya taɓa rabuwa da ko ɗaya daga cikin TRIPLETS nasa na yanzu ba, yau an zo gaɓar da ya kasa, ba zai iya ba. Toma a cikinsu wanenen jaririn da mutumin nan ya kawo? Kuma ina shi wanda aka ɗauka? Me aka yi da shi? Meyake faruwa ne? Josephine ta sadaukar da shi kenan? Ko yaya ne? Wanne ma wannan mutumin? Meyasa dukka hakan ta faru?. Wannan shi ne tashin hankali.

Cikin tsananin zafin rai Lion ɗin ya ɗauki laptop ɗin ya makata da jikin bangon ɗakin, ji kake yi war, ta tarwatse, dafe kansa dake yi mashi barazanar tarwatsewa ya yi, cikin fitar hayyaci ya miƙe tsaye, wani irin azababben jiri yake gani, duniya juya mashi take yi, gara ace mashi mutuwa ɗaya daga cikinsu ya yi da wannan bakin abin da ya gani, wlh sai dai ya rufe maganar nan, amma ba zai taɓa iya rabuwa da Areef ko Aseef, su ne bugawar zuciyarsa, shi kam ya yarda sune TRIPLETS na sa, a bar mashi su kawai........ Ba shakka da akwai ciwo na wuce misali a cikin rayuwar TRIPLETS tamkar yanda Malika ta gayawa Rimsha a baya, to a hankali dai ga shi abubuwa sai bayyana suke yi, mu je zuwa dai, ku kasance da PRINCESS TEEMA, dan ni kaɗai ce zan iya warware maku wannan babbar al'amari, kun dai ga abin da Dr William ya karyata na cewa bai san gwaggo ba, to ga gaskiya ta fito, ga komai kamar yanda gwaggon ta faɗa!! Lallai akwai wani abu wai shi ruɗanin kwakwalwa a cikin TRIPLETS!!.

Waje ya nufa, sam baya ganin gabansa, dan wani irin jiri da uban duhu da yake gani, ji yake tamkar zai haɗiye zuciya ya mutu kawai ya huta. Ɗakin gwaggo ya nufa, da hannu biyu dukka ya dafe kan nasa da ƙarfin gaske, yana tafiya yana huci tamkar ransa zai fita, iska mai tsananin zafi ce take fitowa daga bakinsa, ya ilahi ya lillahi!!.

Da sauri gwaggo ta mike tana tambayarsa lafiya. Ina ai bai kai ga karisowa in da take ba, ya zube kasa wanwar, baya numfashi!.

A dubu gwaggon ta kariso wajen da yake kwance, shi ma Aseef da yake kwance yana aikin zuba shagwaɓa, a ɗari ya sauko daga saman bed ɗin, bai ma san time ɗin da ya iso wajen ɗan uwan nasa ba.

Sunansa suka fara kira babu kama hannun yaro, ina ko motsawa bai yi ba, tamkar rai ne ya yi halinsa. Fridge Aseef ya nufa da sauri.

Ruwa mai bala'in sanyi ya ɗauko, tsabar shiga tashin hankali har kerma jikinsa yake yi, da kyar ya iya ɓalle bakin robar ruwan. Tashin hankali ya hana shi ma ya iya tarbo ruwan a hannunsa, da bakin rofar ya fara zazzagawa ɗan uwan nasa, ita kuma gwaggo, sai ambatar sunansa SAIF!! SAIF!! SAIF! take yi.

Tas Aseef É—in ya zazzaga mashi ruwan, amma ina ko motsawa bai yi ba.

Ganin duk wannan uban ruwa mai bala'in sanyi da ya zuba mashi bai farka bane yasa ya zunduma uban ihu tare da fara jijjiga shi da karfi yana kiran sunansa da ya tashi, kada ya mutu ya barsu, ba zai iya rayuwa babu shi ba, dan Allah ya tashi.

Wannan ihun da ya zunduma ne yasa Uncle T ya shigo É—akin a guje. Ganin abin da yake faruwa ne yasa ya kariso ciki da sauri. Sai kuka Aseef yake yi tamkar ransa zai fita, bawan Allah!.

Babu ɓata lokacin TGA ya naɗe hannun rigar jikinsa tare da sanya karfi ya saɓi Lion ɗin a kafaɗarsa, kai tsaye sai waje ya nufa. Da sauri suka rufa mashi baya.

Bai tsaya tambayarsu me ya faru ba, kawai ya sanya shi a cikin mota tare da bawa Mark umarnin a kan ya ja su zuwa asibiti. Kafin su gwaggon ma su iso harabar gidan, har Mark ya tashi motar. GabaÉ—aya sojojin da suke gidan, kowa ya nufi sauran motocin dake cikin gidan dan su rufa masu baya.
Chapter 27 · 0% Book details