← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 168

Sashe 144

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin dariya ne ya so kubce mashi, amma sai ya danne, dan kada ya kara laifi a kan laifi, yasan idan ya kuskura ya yi mata dariyar nan to fa sai an jisu a rana, Jehan sarkin rigima, uwar kishi kuma.
"Baby i don't know her, kawai new number na gani, kuma ai ga wayar nan ki duba mana ki gani, you should have call her and ask her ma idan kina so, ask her a ina ta sami numberta zata gaya maki". Ya kai karshen maganar yana É—an shafa bayanta.

Shiru ta yi mashi bata sake kula shi ba. Ganin hakan yasa ya fara yi mata raÉ—a tare da kalamai masu sanyaya zuciya a cikin kunnenta. Sai dai kuma sam taki kula shi.

Da yake É—an yi ne kuma ya iya duniyanci, tuni yasan yadda zai yi ya shawo kanta har ma ta mance da fushin da take yi ta biye mashi, bata ma san lokacin da suka fara wasa da juna ba, sai dai har lokacin da akwai tsoronsa cike tap a ranta, amma ta danne ta biye mashi dan dole ba dan ta so ba.

A ɓangaren gwaggo da Akila kuwa, nasiha mai ratsa jiki ta je ta yi mata, sannan ta ce to ta yi wanka ta shirya maza ta wuce wajen mijinta. Haka kuwa aka yi, ta yi wanka tare da shiryawa cikin wasu kayan barcin, sai tashin kamshi take yi ta nufi bedroom nasa.

Yana kwance a saman bed yana latsa waya, hira yake yi da Haroon abokin karatunsa. Kasa kasa kamar mai ciwon baki ta yi sallamar tata.

Bata jira ya amsa ba kawai ta shigo cikin bedroom É—in, bata kula shi ba ta nufi saman bed É—in kawai ta kwanta ta baki bakin gadon, sai aikin turo baki take yi.

ÆŠaura wayar tasa a saman bedside drawer ya yi tare da matsowa kusa da ita, tamkar zai sa mata kuka ya ce.
"Heartbeat yanzu fushi kike yi da ni? Ni ɗin naki? Shagwaɓatinki ne fa!".

Kin kula shi ta yi, sai ma runtse idanuwanta gam da ta yi.
Hannunsa ya kai ya jawota jikinsa, sannan ya cigaba da cewa.
"Please my heartbeat ki dai'na fushin nan kin ji? Please ki yafe mun mana, na tuba fa, kuma ai ba laifina bane, kece nan kika yi daÉ—i dayawa, shi ne yasa duk na ruÉ—e". Yana magana yana turo mata baki tare da shafa mazaunanta.

Duka ta fata kai mashi a saman kirjinsa tana faÉ—in. "Wato ma daÉ—i nayi maka ko? Lallai Heartbeat ka iya mugunta, da na mutu fa?".

Hannun nata da take dukan nasa da shi ya riko yana faÉ—in. "Bazaki mutu ba, kin manta da cewa tare zamu mutu ne? Idan kika mutu ai dole na biki, kin san adadin son da nake yi maki kuwa? Kin san ya nake ji a zuciyata kuwa? Allah Heartbeat ba zan iya jure rashinki ba, please ki yafe mun".

Kara shigewa jikinsa da kyau ta yi kafin ta ce. "A'a ba zan yafe maka ba gaskiya, sai ka yi mun tausa to".

Da sauri ya ce "Tausar ita kaÉ—ai kike so?".
Kai kawai ta gyaÉ—a mashi alamar e ba tare da ta yi magana ba.

Miƙewa ya yi zaune tare da fara yi mata tausar babu kama hannun yaro, yana yi yana kallon face nata. Sai da ta gajiyar da shi sosai, sannan ta ce to ya isa ya zo su kwanta. A hanzarce ya mannata da jikinsa suka fara aikin da suka saba, suna yi suna zubawa juna shagwaɓa kamar ba gobe.

A ɓangaren Aafia kuwa, a parlourn kasa ta sami uncle T, daga shi sai kayan barci a jikinsa, hannunsa na rike da cup mai ɗauke da coffee, ya saki kyakkyawar gashin kan nan nasa har baya, sai tashin kamshi yake yi.

Tun da ta sako kafarta a saman stair case É—in ya tsareta da idanu yana kallonta, sanye take a cikin kayan barci ita ma, sai dai ta É—aura hijabi mai É—an girma zuwa laps nata a saman, sai tashin daddaÉ—ar kamshi ita ma take yi.

A saman sofa É—an nesa da shi ta zauna tana yi mashi barka da dare. ÆŠaura cup É—in hannunsa a saman table dake a kusa da shi ya yi kafin ya amsa mata tare da ce mata ta dawo kusa da shi mana.

Kai ta girgiza mashi alamar a'a a in da take ɗin nan a nan zata zauna. Miƙewa shi ya yi ya koma kusa da ita ya zauna, yana ƙoƙarin fara yi mata magana suka jiyo muryar Dr William ta bayansu yana faɗin. "Sudais baka kwanta ba har yanzu?".

Shiru Tga É—in ya yi yana tunanin sunan Sudais, da alama shi ma an mantar da shi addinin Musulunci, bare kuma yanzu da su Anderson É—in suka juyo da aiki a kansu, so da wuya ya iya tuna sunan, shi kuma Dr William kunga yanzu ya koma ainahinsa, a yanzu shi cikakken musulmi ne mai ilimin addini dai'dai gwargwado.

Ganin ya kasa iya tuna sunan ne yasa kawai ya amsawa yayan nasa da cewa suna hira ne da matarsa, amma yanzu ba jimawa zasu shiga.
Kamar Dr William É—in zai sake yin wata magana, sai kuma ya fasa ya juya izuwa saman kawai.

Nisawa uncle T É—in ya yi, haka suka cigaba da zuba hira cikin nuna tsantsar so da kulawa.

A ɓangaren Lion and Rimsha kuwa, abin ba'a magana, idan aka ce shakuwa ma an rage, sun haɗe sun zama chewing gum abinsu, zuba soyayyarsu suke yi son ransu, sam Lion baya jin kunyar kowa, a gaban kowa zai ɗauki matarsa su wuce ɗaki, yanzu ta fara sabawa da Brady, har aikansa tana yi ya kaiwa Jehan ko gwaggo abu, sai dai bata taɓa yarda ya hau mata jiki, ɗan nesa nesa dai ake abotar.

After some months.

Election time.

An yi zaɓe lafiya lou Alhamdulillah, gabaɗaya kasa ta rikice zaɓen da aka yi, kowa burinsa kawai ya ji sakamako, ga shi Lion ya tashi kan al'umma ya jijjiga kowa da kowa a in da ya tsayar da daddyn Rimsha a matsayin mataimakinsa, dama da biyu ya ce ayi wa daddyn Rimshar ktakardan ɗan kasa da komai da ya shafi doka, ashe abin da yake shiryawa kenan, masu cewa baya son daddyn Rimsha yanzu ya rufe masu baki, dama shi wlh yana kaunar daddyn nata kamar yadda yake kaunarta, musamman ma da gwaggo ta ce tafi son daddyn sama da kowa a cikin ƴan uwanta, sai ya kara son shi sosai, rashin jituwa da basu samun nan kuma hakan ta samo asali ne da dukkansu suna jiji da kai, izzar bala'i ke garesu, shiyasa ba zasu shirya ba, ba zasu zauna waje guda ba, dan ba wanda zai yarda ya duƙawa ɗan uwansa a cikinsu.

Gabaɗaya faɗin U.s ta girgiza na jin cewa bakin fata Lion ya fitar a matsayin mataimakinsa, sannan kuma a halin yanzu kasa ta dulmuye cikin kura na jiran sakamakon zaɓe, shi kuwa Lion hankalinsa a kwance yana gida tare da rigimammiyarsa, ya sakata a gaba yana ta kallon kayarsa, ta wani kara kyau abinta, ta yi ƙiba dumur mur da ita, komai nata ya kara cikowa, sai aikin zuba mashi shagwaɓa take yi yana biye mata.

Kwance suke a saman bed nasa, tana kwance a saman Lion chest nasa tana aikin zuba mashi kukan shagwaɓa a kan lallai ita sai dai su tafi yawo, sai dai ya kaita bakin ruwa su je su huta a can, tana son zuwa bakin teku.

Kawai ya zuba mata idanu ne yana kallon É—an bakin nan nata, sai aikin turo shi take yi, ya kasa iya ce mata ko uppan.

Ganin bashi da niyar yi mata magana ne yasa ta yunkura zata bar jikin nasa.
Da sauri ya riƙota yana faɗin. "Zaki fara ko?".

Kamar zata yi kuka ta ce.
"Noorish kai ne fa ka fara, kaki ka canza hali, nafi 30 mins ina yi maka magana amm kaki ka ce mun ko uppan, to ya kake son nayi? Sai dai nayi ta magana ni kaÉ—ai kamar mahaukaciya?". Ta kai karshen maganar idanuwanta sun ciko tab da kwallah.

Lumshe idanuwansa a hankali ya yi tare da É—an sake buÉ—esu a kanta, sumbata ya fara kaiwa É—an bakin nata kafin ya fara magana kasa kasa a nutse.
"I really like your lips my Meesha, sarkin rigima, kina ji ko? Ni ban iya godon magana bane, amma i will try my best wajen ganin ina amsa maki, and maganar muje yawo kuma zamu je, amma ba yanzu ba, kinga gobe za'a saki sakamakon zaɓe, fitarmu a yanzu babban haɗari ne, ki bari sai komai ya lafa, zamu je duk in da kike so Queen of my heart".

Tsananin farinciki ne ya bayyana a saman face nata, wani irin cool murmushi ta sakar mashi tare da bashi hot sumbata a saman lallausan lips nasa.
"I really love you my Noorish, king of my heart".

Tongue nasa ya fitar tare da fara aikin lasar lips É—in nata yana mai jin tsananin kaunarta tana kara ratsa shi, a haka manne da juna suka yi barci, tamkar zasu shige cikin jikin juna.

Washegari da safe, gabaɗaya kasa sun zuba idanu suna jiran sakamaƙon zaɓe da za'a saki, kowa yana fatan Allah yasa nasa zaɓin ya ci, while su kuma su Anderson suna can suna faman yadda za'ayi ko ta halin ƙaƙa ne su ɗauko Gwaggo, har yanzu sun kasa iya ɗaukarta, saboda yawan zama da alwala da take yi, ga askar na safiya da maraice wanda duk wuya duk daɗi bata bari ya wuceta bata yi ba, haka shi ma zama da alwalar, duk wuya duk daɗi da alwalarta take tare, hakan yasa suka kasa iya ɗaukarta, sai suka koma suna rakuɓe rakuɓe suna neman wanda zasu ɗauka a cikin gidan, wanda yake kusa da zuciyar Lion sosai.

Maryam kuwa an sallamota daga aaibiti ta dawo gida, tana part na gwaggo, Areef ya É—auko masu aiki mata guda biyu suna kula da ita. Ita kuma Adiva har yanzu tana wajen Sheikh Sultan, yana ta fama dan ya ga ya ceto baiwar Allahn nan.
Chapter 144 · 0% Book details