← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 168

Sashe 153

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ban san cewa zasu É—auki uncle ba, abin da na sani kawai shi ne dole zasu so É—aukar É—aya daga cikin family, kuma na yi hasashen maza zasu É—auka ba mata ba, hakan yasa dukkanku na sanya maku na'urar bi diddigi a jikinku ba tare da saninku ba, duk wani namiji da yake a cikin gidan nan to akwai wannan na'urar a jikinsa, na yi mamakin ya aka yi tsawon watanni na'urar dake jikin uncle bata aiki sai yau, i think in da suka kai uncle É—in da farko suna amfani da software na hana bin diddgi ne, a yanzu kuma sun canzawa uncle É—in waje, sun fitar da shi zuwa wani wajen, sun yi hakan ne kuma domin su É—auki hotonsa su turo mun kamar yadda suka yi É—in, sun yi hakan ne kuma dan hankalina ya tashi, na shiga damuwa, sai dai basu san cewa hakan da suka yi shi ne zai kawo karshensu ba, dan fitar da Uncle É—in da suka yi daga in da suka kai shi da farko ne yasa na'urar jikinsa ta fara aiki, dan haka ga location da komai da komai a jikin computer nan, sai ku fara aikinku, kada ku kuskura ku bar ko mutun É—aya da rai face Anderson and His Excellence, su biyun nan kawai nake son ku kawo mun su a raye, saura duk ku kashesu, ku yi bombing na wajen kaca kaca".

Cikin sauri Areef ya tari numfashinsa da cewa.

"Amma Lion uncle Herry fa? Ka ce mu kashe kowa! Kuma kasan uncle Herry shi ne king nasu a wajen, ya zamu yi da shi".

Nisawa ya yi kafin ya ce. "Uncle Herry ai namu ne ba nasu ba, what i mean here is, duk wasu mutanensu ku kashe dabbobi banza, namu kuma ku dawo dasu, Anderson and His Excellence ina da bukatarsu a raye, saboda hukuncin mutuwa ta yi masu kaÉ—an". Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya nufi hanyar fita waje.

"Amma Lion yaushe zamu tafi?". Cewar Mark.

Ba tare da ya tsaya daga tafiyar da yake yi ba ya basu amsa da. "Now". Ya kai karshen maganar tare da ficewa daga room É—in.

Kallon juna suka fara yi a tsakaninsu. Sir Safwan ne ya katse masu kallon da cewa. "Zan iya rakaku?".

"Gidan biki or party ne da zaka rakamu?". Cewar uncle T

Girgiza mashi kai Areef ya yi yana faÉ—in. "Ka kula mana da matanmu kawai, kila mu dawo da wuri, kila aka sin haka, amma daga yanayin wajen akwai haÉ—ari sosai, zamu É—auki kwanaki ko watanni, anywhere ka kula sosai".

Uncle T ɗin ne ya sake karɓar zancen da cewa. "Ba shakka zamu iya ɗaukar watanni muna fama kam, amma dai ina sa ran nasara, ya kamata mu fara aiwatar da abin da ya dace, Safwan kada ka gayawa Dr William ga in da muka tafi, dan hankalinsa zai tashi sosai, kuma bana son hakan".

Areef ya ce. "Yeah dama nima abin da zance kenan, kada ku sanar da family ga in da muka nufa, ku barsu a kan mun yi tafiya kawai, let's go uncle T". Ya kai karshen maganar tare da nufar hanyar fita.

Rufa mashi baya Mark and Tga ɗin suka yi, sir Safwan kuwa ya tsaya ƙasaƙe yana kallonsu har suka fice, sannan shi ma ya ja dogon numfashi tare da saukewa a hankali ya rufa masu baya.

A takaice haka suka shirya rundunar sojoji guda, tamkar waɗan da zasu tashi duniya, a wannan rana suka nufi wannan ƙungurmin bakin dajin, sun yi shahada dan kawar wa da kasarsu ɓata gari bayin Allah.

Shi kuwa Lion dukufa ya yi da yi masu addu'a tare da fatan Allah ya dawo mashi da su lafiya, ba halin ya bisu ne da wlh ba zai iya bari su tafi su kaÉ—ai ba, dole ce tasa ya zauna shi, domin kujerar President ba wasa ba, ya sanya Sheikh Sultan sai yi masu addu'a yake yi babu kama hannun yaro.

Wasa wasa sai da suka shafe watanni kamar yadda suka faÉ—a kafin su tafi, ga shi shi Areef ma ko sallama da Jehan bai yi ba, ya barta tana barci, kuma da gangan yaki tashinta, dan yasa zata tsayar da su ne ta hanasu tafiya a kan lokaci, zata yi ta yi mashi kuka tasa ya tafi da tunaninta tare da damuwa a ransa, shi ne yasa kawai ya bawa Lion É—in amanarta sannan suka wuce.

Tun da suka tafi kuma gabaɗaya wayoyinsu bata aiki, ba network a wajen, babu wani connection da suke samu tsakaninsu da ƴan uwa, shiru kake ji tamkar an ɓallawa sama harara.

Har Akila ta haifi Æ´aÆ´anta santala santalan guda uku, wato TRIPLETS, dukkansu kuma maza kyawawan gaske, su Areef shiru basu dawo ba.

Sai dai fa ranar haihuwar Akila an yi ƙaramin yaki ba kaɗan ba a gidan, dan kuwa sun ga dirama wajen Aseef, likitoci jiga jigai aka ɗebo daga hospital ɗin Dr William, aiki aka yi mata aka cire ƴaƴan, ba zata iya haifarsu da kanta ba, ba yadda ba'ayi da Aseef ba a kan ya tsaya a waje, ya ce wlh ba zai tsaya ba, ɗakin ya shige abinsa, ya je ya zauna kusa da Heartbeat ɗin tasa, ya ɗaura kanta a saman laps nasa tare da ƙanƙame hannunta yana ta kallon duk wahalar da take sha, ya sha kuka kam hawaye bibbiyu, sai faɗi yake kada likitocin nan su yarda su bari ta mutu, idan ta mutu sai ya kashe su ɗaya bayan ɗaya suma, sai kace su ne suka ɗaura mata ciwon, yana neman sauke haushi a kansu.

Ai su gwaggo sunga ikon Allah, dan fa Aseef ya yi masu karamar hauka, dan ma Allah yasa aiki aka yi mata, da da kanta zata haifesu ai da ina ga zuciyarsa ce zata buga idan yaga halin da zata shiga, aikin ma ya bi ya wani ƙanƙameta ya takurawa likitoci basu samu su yi aikinsu yadda ya kamata.

Sai dai kuma fa abin dariya abin takaici, ana ciro mashi baby's ɗin ya saketa ya koma wajen yaran abinsa, wai ya je ganinsu, har ya manta yanzu ya gama zubar mata da hawaye har yana cewa shi fa baya son baby's ɗin, ya fi sonta, dan haka shi a ceci rayuwarta kawai, ba ruwansa da baby's ɗin, har da cewa ba zasu sake haihuwa ba daga wannan, amma da yake ɗa mai daɗi ne, ana cirosu har ya manta da surutan da ya rinƙa yi a kan nasu, ya wani shige gaba yana ta kallon yaran, sai tsallara ihu suke yi, shi kuma sai masifa yake yi wa likitocin a kan su saka mashi yara su yi shiru ko kuma ya hukuntasu, dan shi ba zai iya hakuri ya ji baby's nasa suna kuka ba.

Izuwa yanzu dai kowa na family ya dai'na mamakin halin Aseef, sun zuba mashi ido kawai suna kallon ikon God, dan ya wuce tunaninsu, daga wannan sai wannan, a kan waÉ—an nan TRIPLETS É—in nasa zai iya kashe mutun.

A gaban idanuwnasa aka yi wa baby's and maman baby's komai, yana tsare da kayansa yana kallonsu. Ko da aka gama gyara su ma ya hana family É—aukar yaran, wai kada su yi su karya mashi yara, dan kashin yaran ba kwari ne da shi ba.

Gwaggo kawai ya yarda ya bari ta É—auki na farko da aka fara haifa, dukka yaran wlh kama da Aseef É—in sak suke yi, kamar an tsaga kara, babu wanda ya É—auko Akilar, harta kwayar idanuwansu da yake brown irin nasa, duk sai suka fito a turawan, babu kalar Akila a cikinsu.

Ita kuma Jehan tana nan tana aikin tura uban ciki haihuwa ko yau ko gobe, ga cikin nata ita ma kato da shi, an yi mata scanning, sai dai ta ki yarda kowa yaga result ɗin abin da yake a cikin nata, ta ɓoye kayanta, daga ita sai gwaggo suka sani, ta ce kowa ya barta ta sarara, sai cikin ya fito duniya zasu ga menene a ciki, haka suka hakura suka rabu da ita.

Ba yadda gwaggo bata yi da Lion ba a kan ya zo ya ga yaran Aseef, amma ya murje idanuwansa ya ce shi wlh ba zai je ba, kuma kada a kawo mashi su É—aki baya so, ita kam gwaggo yanzu al'amarin Lion a kan tsanar yara ya fara bata tsoro, ga Maryam matar Sir Safwan har tana da É—an kara min ciki, amma shi Lion shiru, hakan yasa gwaggon ta fara zarginsa a kan anya ba wani abin yake bawa Rimsha yasa bata É—aukan ciki ba?.

(Nima Princess Teema na yi wannan tunani🤔 gwaggo ki binciko mana gaskiya, ina dalili? Mu muna son muga little Lion)

Kowa yasan da cewa Lion ya fi Kaunar Aseef sama da kowa a cikin Æ´an uwansa, amma kuma duk wannan uban kauna da take a tsakaninsu Lion É—in yaki yarda ko da ido ya kalli Æ´aÆ´an Aseef É—in, da yake Aseef É—in yasan tun farko Lion baya son yara, sai bai yi gigin kai mashi labarin Akila ta haihu ba, sai ya rabu da shi kawai ya rungumi Æ´aÆ´ansa abinsa, sai murna yake yi ya sami TRIPLETS tashi É—aya.

Ita kuma Rimsha Allah ya gani tana son yara, kullum sai ta yi zancen cikin Akila da Jehan É—in, amma da zarar ta fara yi wa Lion É—in zancen haihuwar zai canza masu topic na hira, shi zancen yaran ne sam baya so, amma kuma duk da haka yana tsananin bawa Jehan kulawa na wuce misali, a yanzu haka tana a part nasu da zama, saboda yana ganinta tamkar Areef, dan maganarsa ta karshe da Areef É—in ma kenan a kan Jehan É—in ne da abin da yake a cikinta, amana É—an uwan nasa ya bashi na Jehan É—in, dole ya kula da wannan amanar ta É—an uwan nasa, saboda bashi da tabbacin Areef É—in zai dawo a raye ko kuma zai mutu?.

Hakan yasa yake kula da Jehan ɗin over, bedroom ɗin da take ma sai da ya saka mata camera, duk da a cikin part ɗaya suke, yana iya jiyo motsinta, amma bai wadacesa ba hakan, sai ya kara mata da camera dan ya rinƙa kallon duk wani abin da take yi.
Chapter 153 · 0% Book details