← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 168

Sashe 74

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A takaice gwaggon ta ce mashi aljanune suka taɓata. Shiru ya ɗan yi yana maimaita kalmar aljanu, shi sai yau ma ya taɓa jin wannan suna, wai aljanu, abin ma dariya ya bashi, ko meye aljanun? Ya tambayi kansa. Da yaga dai shi ba wani ganewa zai yi ba, sai ya miƙe yana faɗin "Let me go and see uncles".

A takaice gwaggon ta ce mashi "Is good, suna ma shirye shiryen wucewa gidajensu yanzu ne". "Why zasu koma gidansu?". Ya tambaya da mamaki a saman face nasa.

Brr Naurat ce ta ce "E mana zasu koma gidansu, shi ne dai'dai, a nan sun takura sosai ne". Turo baki ya yi yana faÉ—in "Amma without uncle Hossain ko? Dan ni Allah ba zan yarda ya je ko'ina ba, dole duk in da zamu je mu tafi da shi tare, i don't want him to stay out of us". Ya kai karshen maganar kamar zai yi kuka.

Da sauri gwaggo ma ta ce "You are right! Nima gaskiya ba zan iya yin nisa da Nawazuddeen ba, dan haka shi dole ya zauna a tare da mu, dole na gayawa Saif, ina son mu kasance a tare da Nawazuddeen".

Juyowa ya yi ya dawo ya sumbaci gwaggon a kumatunta yana faÉ—in "That's my momma, that's why I love you, uncle babu in da zai je, we are together with him". Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya fice daga É—akin.

Ita dai Brr Naurat da idanu kawai take binsu, Aseef É—an rigima.

A takaice sai da Sheikh Sultan ya shafi kwana uku yana yi wa Rimsha addu'a tare da magunguna irin na addinin musulunci, sannan ne suka sami nasarar cetota ta dawo dai'dai, amma fa anci kwakwa, an wahala ba kaɗan ba, tsayuwa zayyana maku irin wahalar da aka sha ma sai mu cike wannan book 4 ɗin fam, da akwai sauran story a gaba, so ba zan tsaya ɓata lokaci na sosai a wajen zayyano maku ba, just ku yi imagine ya bakar wahala take a ranku, akwai abubuwa da yawa a gabana, ba zan tsaya ɓata lokacina ba!.

A cikin waɗan nan kwanaki ukun fa abubuwa da dama sun faru, wanda suka haɗa da dawowar Tga Nigeria, dan Lion ya ce mashi ya dawo Nigeria zai biyo shi, sannan su Abba kowa ya koma gidansa lafiya lou, yanzu gidan ya rage daga gwaggon, Brr Naurat da Dr Salman, sai Jehan, Rimsha and Akila, matan TRIPLETS kenan, sai Sheikh Sultan mai yi wa Rimsha magani, ita kuma Anaya sun wuce Washington da Mark ɗinta, Lion yasa an mayar da shi can, dama already kunsan Brr ta ce ya karɓi kalmar shahada sai a aura mashi Anayar su tafi a tare, to hakan aka yi, su Abba ne suka ɗaura auren a cikin palo bayan ya musulunta, yanzu sun wuce Washington yana asibiti bawan Allah, yana shan wahala sosai da sosai, sai daddyn Rimsha, shi ma yana nan a gidan bai koma gidansa ba, dan gwaggo ta ce babu in da zai je ya barta gaskiya, shi ne Lion ya ce to ya zauna sai ya dawo kawai, Aylar daddyn Jelly kuwa tana asibiti a kwance, saboda ta samu matsala a cikinta har sai da aka yi mata aiki, ta sha wahala ne, cikinta ya zube, ta zubar da jini, sannan ta ɗauki tsawon kwanaki a sume, ga kuma wahala da jijjiga da cikin nata ya sha, abin dai ba'a cewa komai, Allah ne ma ya kaddara tana da sauran numfashi a gaba, ai da ta jima da mutuwa, yanzu dai shi ne yasa sai da aka yi mata aiki, yanzu haka tana gadon asibiti tare da Aunty matar Abbi, dama kunsan sun koma gidansu. A ɓangaren su Aafia kuma, Abbo ya dawo, ya sakata a gaba, tun da ya dawo ya makale yana zarya a tsakanin gidansa da gidan Abbi, Ummi tana Katsina wajen ƴan uwanta, bata san ya dawo ba baiwar Allah, kuma bai bari ta san ya dawo ɗin ba, dan ba ta ita yake yi ba a halin yanzu, hankalinsa ya karkata a kan Aafia, dan ita ya dawo dama, ana buƙatar ta a wajen tsafin nasu, shi ne ya dawo ɗaukarta, sai safa da marwa yake yi a tsakanin gidajen biyu, sai dai Allah da ikonsa, duk zuwa gidan Abbi ɗin da yake yi baya samun ganinta, ko sau ɗaya bai haɗa idanu da ita ba, shi kuma burinsa kawai su haɗa idanu, suna haɗa ido shikenan ya sami kaso 60 a cikin ɗari na abin da yake so, Allah sarki, so suke yi su hallakata kamar yanda suka hallakar da Dr Nawid, Abbo shi ya bada Dr Nawid, sai dai ba'a son ransa ya bada shi ba, dole suka tilasta mashi, da farko ma ya ce ba zai bayar ba, sai da ya ji matsa da wahala ne ya yarda ya bayar, abin da yasa suka ce sai ya bada Dr Nawid ɗin kuma shi ne, idan baku manta ba Dr Nawid ɗin ya hana shi yin amfani da Jelly, to shi ne abin ya ɓata masu rai, suka ce tun da ya rushe masu shirinsu a kan jelly, to za su yi amfani da shi a madadinta, shi ne yasa suka kashe shi.

To a takaice dai Abbo ya dawo, yana neman ta yadda zai yi ya É—auki Aafia ido rufe.

A ɓangaren Lion kuwa, a cikin waɗan nan kwanaki uku da suka wuce, ya aikata abubuwa da dama, ciki kuma har da rubuta takardar ajiye aikinsa na soja da ya yi, wannan abin ya yi mugu mugun ɗagawa jama'ar kasar hankali, saboda Lion soja ne wanda kowace kasa take buƙatar jarumi kuma jajirtartce irinsa, tsayayye namiji ne kuma jajirtartce a kan aikinsa, yana da adalci da gaskiya, ga rikon amana, babu zancen cin hanci a lamuransa, kuma babu ɗaga kafa a wajen yanke hukunci, ko kai ɗan uban waye idan ya kamaka da laifi, ba shakka sai ya hukuntaka, babu uban da ya isa ya taka mashi burki, ko his excellence baya ɗagawa kafa, kaifi ɗaya ne shi, babu mai iya tankwara shi, rashinsa a hukumar soja babbar ci baya ne ga kasar U.s gabaɗaya, yana da matuƙar farinjini, al'umma suna tsananin kaunarsa saboda gaskiyarsa, da sama masu kwanciyar hankali da cigaba da yake yi, kowa begensa yake yi, jin cewa ya ajiye aiki yasa wasu har suma sai da suka yi, saboda shiga tashin hankali, wasu kuwa har da rashin lafiya, kowa sai tambayar dalilinsa na ajiye aiki yake yi, amma sam yaki yarda ya fito daga gida ma bare ya yi hira da wasu, duk sojojin dake gidansu ya tarkatasu ya mayar da su headquartersu, sannan ya ɗauko wasu jibga jibgan bodyguards lafiyayyu masu jini a jika ya jibge a cikin gidan nasu, bodyguards ne masu lafiya karfafa masu kiran samudawa, abin ya ɗaurewa jama'a kai, his excellence ya shiga ruɗe sosai, yasan Lion sarai, shi mutun ne da baya yin abu haka kawai, dolen dole sai da kwaƙkwaran dalili, to menene dalilinsa na ajiye aiki? Meyasa? Wannan shi ne tambayar da His excellence ɗin yake ta yi wa kansa, ya haɗa taron gaggawa a white house, ya kuma turawa Lion ɗin saƙon gayyata, amma ya ki zuwa, ko kallon takardar gayyatar ma bai yi ba, dan ya ce bata da amfani a wajensa, his excellence yana tsoron ya sanya karfin mulki ya tursasa Lion ɗin a kan yazo taron dole, dan shi dai yasan waye jikansa, idan ya gwada mashi karfin mulki, to shi kuma ba shakka zai gwada mashi karfin jini, dan Lion baya barin ko ta kwana, dan haka sai His excellence ɗin ya haɗa malaman jikinsa, bai tursasawa Lion ɗin zuwa taron dole ba, haka suka ɗan yi maganganunsu suka watse, anyi anyi da Lion ɗin ya fito ya yi magana a kan meyasa ya kashe kakansa, nan ma yaki buɗe bakinsa, da his excellence ya ga dai Lion fa wani abin yake shirya masu, sai ya lallaɓa ya wankesa a kan zagin kashe kakan nasa da ake yi mashi, duk Lion ɗin yana ganin komai da yake faruwa, amma sam bai yi yunkurin saka baki ba, ya tada kura, a jijiiga gari ya koma gefe ya lafe shiru kamar babu shi, daga shekaran jiya zuwa yau ko'ina idan ka zaga a cikin birnin Washington da kewayenta, maganar Lion ake yi, ko ta ina zancensa ne kawai yake tashi, gidan jaridu kafafen yaɗa labarai, da ko'ina, ya tada tarzoma ba kaɗan ba.

Ya koma gefe guda ya yi shiru kamar ba shi ba, abin da ya sanya ya ajiye aikin soja, saboda ya san ta hakan ne kawai his excellence zai yi ƙoƙarin horar da shi, yasan cewa zasu yi ta ce mashi zasu tuɓe mashi kaki, ko kuma su saka shi yin wani abin a gwammatance, to shi ne yasa kafin ma su fara wannan diramar ya ajiye aikin, yanzu ba kaki da gwamnati ce zasu yi faɗar ba, farar hula ce da gwamnati. Wannan shi ne cakwakiya, shi ne ake kira da ainahin game. Tsafinsu ba zai iya kama shi ba, babu abin da suka isa su yi mashi, dole ne sai sun ajiye tsafi sun yi ta kulla mashi manakisa, shiyasa shi kuma ya biyo masu ta karkashin kasa, Allah ne kaɗai yasan shirin da yake shirya masu!!.

His excellence ya so haɗuwa da Lion ɗin a koma ina ne, sai dai ina bai samu damar haɗuwa ba, hasali ma Lion ɗin ko waje baya fita, yana cikin gida abinsa, gabaɗaya faɗin U.s ta ɗauka a kan ajiye aikin nan nasa, ta girgiza kasar girgiza mafi girma, amma shi ko a jikinsa, sai ma barci da yake shararawa, yana hutawa, har wata ƴar kiba ya kara abinsa, ban da tunanin gwaggo, TRIPLETS nasa da kuma Meeshansa, to baya tunanin komai a rayuwarsa, hankalinsa a matuƙar kwance, kai daga gani kasan ba karamar abu yake shiryawa ba, komawa da baya ga zaki ba tsoro bane, shirin yaki ne, his excellence ya san da hakan, shi ne yasa hankalinsa ya yi mummunar tashi, shi kansa Anderson a tsorace yake.
Chapter 74 · 0% Book details