Sashe 36
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cikin kuka da tashin hankali ta fara magana kamar haka. "Hakika kamar yanda na gaya maku cewa Queen mahaifiya ta ce, to ba shakka hakan ce, mun kasance kabilar igbo mazauna garin Enugu, kuma mun kasance kiristoci ne, karatu ya kai ni Kaduna state, a nan na haɗu da Abbanku, dama already tun kafin na tafi karatu, na san da gidan Daular Mutuwa, kakana ne ya kirkireta, kowa ya san kabilarmu da tsafi kamar baza'a mutu ba, to muma muna ɗaya daga ciki, Mahaifiyarmu, wato Queen, ita kaɗai kakana ya haifa, Shiyasa da ya mutu, sai ta gaji karagar mulkinsa a Daular Mutuwa, ni da kai'na ina zuwa har cikin Daular, kuma a lokacin babu wani abu na tsafi wanda ban iya ba, duk wata tsubbace tsubbace na iya nima, da ni da kanwata, sai kuma wani ɗan uwan mamana, mune na kusa da ita a Daular, a takaice dai na san komai, Allah da ikonsa, da Allah ya so ni da rahama, sai ya jarrabeni da son karatu, ita kuma kanwata, tana tare da Queen a cikin Daular, a gabana za'a yi tsafi da mace, a gabana ake komai na abubuwan subbace subbace da siddabaru, ko a jikina, dan lokacin zuciyar kafurci ne ke gareni, manyan mutane ne suke zuwa cikin Daular dan a biya masu bukatunsu, da akwai manyan manyan gidan matsafa da suka dogara da Daular, akwai abubuwa da dama wanda ni a yanzu na mance da shi ma gabaɗaya, kuɗi kuwa, habawa ai idan munaso ma mukam, zamu iya yin gadon kuɗi ku kwanta, muna da arziki na wuce misali, mu da mumuke bawa wasu ma, manyan mutane daga kasashen dake makwabtaka damu, suna zuwa neman arziki da abin duniya a wajenmu, wasu su kawo ƴaƴan ƴan uwansu mu yi masu kuɗi da su, wasu kuma ƴaƴan cikinsu, abubuwa dai da dama, mun shahara a duniyar tsafi. To a takaice dai sai Allah ya ƙaddara na tafi Kaduna state karatu, a can na haɗu da Abban Imran, wasa wasa muka fara soyayya, ina son shi sosai kasancewarsa Bature, kun san turawa da mugu mugun shiga rai ga farinjini, ga kyau na wuce misali. Daga karshe dai na musulta, saboda da shi, da ya kasance Allah yana sona da rahma, sai Allah ya saka mani kaunar addinin sosai, na yi karatun Alkur'ani mai girma sosai da sosai, ina jin alokacin da akwai abin da ya ɗaukewa Queen hankali, shi ne yasa bata lura da abin da nake yi ba, idan ba haka ba, wlh duk wani motsinmu tana gani a cikin madubin tsafinta, amma ga mamakina har na musulta, na kuma yi karatun addini, kuma bata gane ba. To a takaice dai, lokaci da muka yi hutu, sai Abban ya ce zai bini muje gidanmu ya gaida iyayena, daga nan ayi maganar aurenmu, da yake ni wlh na mance da ya gidanmu ma suke, sai na yarda mashi kawai, na ce muje, ba tare da sanin iyayensa ba, muka kama hanyar Enugu, a ranar naga bala'in da ban taɓa gani ba, dan da muka je gida, Queen ta ce wlh dani da Abban duk kashemu zata yi, to dama na gaya maku already nima a lokacin na iya tsafe tsafen nasu dukka, hakan tasa na yi fito na fito da mahaifiyata, dan na kare Abba kada su kashe shi, duk da na musulta, hakan bai hana ni na haɗa kayan tsafina dan muyi faɗa da ita ba, domin a lokacin a cewata, tsafin ne kawai zai kwacemu daga hannunta, mun sha azaba ta yanda sai da muka koma yin karatun Alkur'ani mai girma, sannan muka iya kuɓuta daga hannunta, a nan ne na kara yarda cewa tsafin ma dukka shirmen banza ne, tun da ga shi ya kasa kuɓutar da mu daga hannunta, karatun Alkur'ani mai girma ne ya kuɓutar da mu, tun daga lokacin sai na kara nesanta kaina da tsaface tsafacen, ita kuma Queen ta sha alwashin da ni da duk waɗan da suka tallafa mani, sai taga bayanmu, ni kuwa na ce mata idan ta fasa bata cika Queen of Daular Mutuwa ba, abin ya yi tsananin kona mata rai, dama kun san yanda kabilar igbo suke da tsananin zafi idan aka ce yau ga nasu ya musulunta, to haka nima dangina suka ɗauki wannan zafin, akwai wani ɗan uwanmu da dama shi zan aura, to da ya ji abin da ya faru, sai ya ce shi ma ba zai kyale Abba da gabaɗaya familynsa ba. In takaice maku dai haka muka baro garin Enugu babu daɗi, da kyar ma muka iya kaiwa airport muka dawo Kaduna, babban abin da ya kara sakawa naji ina son addini musulunci sosai, shi ne yanda iyayen Abba suka karɓeni, basu ji kyamata ba, dan na kasance Kristen kuma ƴa ga magicians, sam ba su guje ni ba, mahaifinsa Dr Salman yana da kirki sosai, ita kuma matarsa Amarya tana da bakar zuciya, sai dai ni ba zata iya cutar da ni ba, saboda already a dafe nake, jinin Queen ce ni, ta dalilina ma asirin da ta yi wa Dr Salman ɗin ya karye, dan wannan a jininmu yake, mune gidan asiri, mune asiri da kanta, duk girman asiri in dai ina wajen, to ba zai yi tasiri ba, ni ban san me Queen ta yi mana a jininmu tun muna yara ba, to haka gabaɗaya su Imran suka taso, ba'a iya cutar da su, saboda jina ne su, in takaice maku ita kanta amaryar sai da ta zo ta kaunace ni fiye da ƴarta Batula, ta soni tamkar ta yi mani numfashi, a gidansu Abba na cigaba da rayuwata har muka yi aure, ƴan uwansa dukka suna kaunata sosai, barema Dr Salman bawan Allah, yana sona sosai, a lokacin ya ce mani yana son matarsa Naurat, amma bai isa ya je kasar Russia ya ce zai ɗauketa ba, idan ya je, ƴan uwanta za su kashe shi, dole ya hakura da ita, sosai a lokacin suka nemi ɗan uwansu Nawazuddeen wanda ni banma san shi ba, na dai ji labarin ya bar gida, amma basu gan shi ba, bayan aurenmu da Abban Imran, daga nan abubuwa suka fara faruwa, haɗarin da Dr Salman ya yi shi da amarya, ina da tabbacin da sa hannun Queen, a lokacin na cewa Abban Imran zan sake komawa ruwa, wato zan haɗa kayan tsafina, dan na yi maganin Queen, saboda idan ba fito na fito muka yi ba, in dai ban rushe Daular Mutuwa ba, to ba zata barni ba, dan ba zata iya yafe ni ba, sosai Abba ya yi mani nasiha, ya kuma yi mani faɗa a kan ko bayan ransa bai yarda na sake komawa tsafi ba, kamar yanda na barta, to ya zamana na barta kenan har abada, sosai naji nasiharsa, dan haka sai na hakura, muka cigaba da rayuwa muna karatunmu cikin farinciki, amma mutuwar Dr Salman ya girgizani, ina tuna bawan Allah nan, mutun mai farar zuciya, sai dai fa har gobe ina jin kamar bai mutu ba, ina ji kamar wata sharrin Queen ta haɗa mana, amma dai Allah masani.
(Masu karatu i hope yanzu kun fahimci dalilin kasancewar Dr Salman a Daular mutuwa?)
Tun daga wannan lokacin muka cigaba da yin rayuwarmu cikin farinciki, na rike kannan Abba kamar kannena, na mance da tawa kanwar da mahaifiyata, na sami sabuwar ahali, a haka muka kasance har Abbi wato Deen shi ma ya yi aure, ya auro wata Æ´ar Katsina da suka haÉ—u ita ma a school, ita ce mahaifiyarsu Irfan, mafadaciya ce sosai, da ta nemi ta kawo mani wargi, na taka mata burki, akwai wata rana da na yi mata dukan mutuwa har sai da aka kai ta asibiti, daga lokacin aka rabamana gida da ita, Abbin ya É—auketa zuwa É—aya daga cikin gidajen Dr Salman, in takaice maku labari ni ban sake waiwayar iyayena ba har rana mai kanata yau, na rufe babinsu, kuma nasan wlh Queen ba zata rabu da ni ba, ba shakka ita ce nan ta É—auki Akila, kuma ita ce ta É—auki matar Maik, sai dai fa sun canzawa Daular Mutuwa tasu waje, bata a in da na santa da, tun kafin na bar gida dama na ji suna shirye shiryen kara mata wasu matakan tsaro, sannan kuma su canza mata mazauni, a yanzu ita Rimsha ita kaÉ—ai ce zata iya gaya maku in da Daular Mutuwar take, saboda ita ce ta shiga cikin ta kwanannan, amma kuma a gaskiya duk wanda ya shiga Daular Mutuwa ya fito da rai, to dole a jinjina mashi!! Dan duk yanda kuke tunanin Queen ta wuce hakan wlh, sam bata san menene imani or tausayi ba!!.