← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 168

Sashe 7

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

After some minutes, can duniya ta kara yin shiru sosai. Lallaɓawa ta yi ta miƙe zaune, a hankali ta matso kusa da shi, cikin sanɗa ta ɗan leƙo fuskansa, dan ta gani ko ya yi barci. Tana so ne ta yi barci, amma ta kasa, saboda tsoro, shi ne ta zo ta gani ko dai ya yi barci ita ma ta samu ta yi.

Ganin idanuwansa a rufe yasa ta ɗan koma ta zauna zuciyarta na yi mata wasi wasi a kan bai yi barci ba, yana jiran ta yi barci ne kawai ya hake mata. Jin abin da zuciyarta yake raya mata ne yasa ta sake lallaɓawa ta leƙo face ɗin nasa.

Duk abin da take yi yana jinta, sai dai bai motsa ba, dan shi ma yana son ta sami nutsuwa ta yi barci. Amma ina abin ya ci tura, sake leƙo face nasa a karo na uku ta yi, dan ta kasa sakin jiki ta kwanta, ta kasa yarda da ya yi barci.

Jin haka yasa ya bari time da ta leƙo face ɗin nata a karo na ukun, sai ya jawo hannunta da ta kafa a jikin mattress ɗin ta gaban face nasa dan ta sami damar leƙa shi da kyau. Jawo hannun ya yi tare da juyowa gareta ta faɗa saman kirjinsa. Rungumeta sosai ya yi tare da juyowa da ita da kyau da kyau suna fuskantar juna. "My beauty, why zuciyarki bata yarda da ni ba?". Girgiza mashi kai ta yi tana faɗin ba komai.

"Seriously babu abin da zan yi miki, idan ina son na yi miki wani abin, ki sani tsab zan iya yi ba tare da son ranki ba, amma i can't do that, so feel free and sleep kin ji?".

Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗaura kanta a saman gefen kirjinsa, a hankali ta lumshe idanu bayan ta ɗaura hannunta a saman wuyarsa, ta ɗan saƙalo kenan.

Shi ma nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, sai a yanzu ne ya ji zai iya yin barci, ji ma ya yi tamkar kwanciyar nan da ta yi a jikinsa, kamar ta karawa É—akin nata faÉ—i da girma ne, so sai ya ji yanzu yana normal.

Hannu ya É—aura a saman bayanta tare da lumshe idanu shi ma. Ba jinawa barci ya yi awon gaba da su.......ASUBA TA GARI.

Da yake bata yi barci da wuri ba, har wuraren uku suka sami barci, sai bata iya tashi sallar asuba, makara ya kamata, shi dama ba sallah yake yi ba!.

Sai misalin karfe 7 na safe ta farka, a hankali ta waro idanunta, kai tsaye sai saman kyakkyawar face nasa. Sai zuba barcinsa yake yi hankalinsa a kwance, É—an shafa lallausan kumatunsa ta yi tare da yunkurawa zata mike. Duk motsinta yana ji, dan sam bashi da nauyin barci, tun farkawarta ya farka shi ma.

Jin zata bar jikinsa ne yasa ya waro idanunsa a hankali shi ma, kai tsaye sai saman face nata.

Kasa kasa da murya irin na mai barci ya ce "Good morning my beauty". A hankali ya motsa laɓɓan nasa wajen furta maganar.

Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta amsa mishi da "Morning my Dr, how was your night?".

Bai amsa mata ba, sai dai ya tsareta da idanu yana kallonta. Ganin hakan yasa ta yunkura zata miƙe, matsowa ya yi kusa da ita sosai tare da rikota. Can kasan makoshinsa ya furta "Can i have a one kiss my beauty?".

ÆŠan É—aga idanunta sama tamkar mai tunani ta yi.
Bai jira ta bashi amsa ba ya matso kusa da ita sosai tare da haÉ—e fuskokinsu, kafin ta yi wani yunkuri ma har ya fara kissing nata abinsa.

Wani irin duniya suka lula dukkansu biyu, Baturen mutun akwai shegen iya soyayya, ya yi mata wayo sai bata hot kiss yake yi.

Haka ya matseta a jikinsa tare da fara shafa mazaunanta da tun jiya suka tsole mashi idanu, kuma suke É—aukar hankalinsa, cikin kwanciyar hankali yake yin komai.

Karar danna kararrawar kofa ce ta dawo da shi daga duniyar da ya afka. Da kyar ya iya raba bakinsa da nata, idanuwansa sun yi jajir kamar wuta, murya kamar wanda ya yi shaye shaye, a hankali kasa kasa ya furta yana zuwa bari ya duba wanene.

Okey ta amsa mashi tare da miƙewa ita ma ta nufi toilet jiki ba kwari. A nata tunanin Cherish ce ma, ta san ita kaɗai ce take zuwa mata gida without a permission.

Toilet ta shige, shi kuma ya sauko ya nufi palo. Yana buÉ—e kofar suka yi ido huÉ—u da daddynsa, mummynsa, Uncle Herry da kuma Æ´an'sanda guda biyar, masu sanye da kakinsu a jiki, jajir da su kamar tsada. A lokacin mummynsu tana da cikin Tyson, wato Tga kenan.

Hakika babu maraba a tsakanin face É—in Dr William da mummynsa, harta blue eyes É—in nata ne ya É—auko, kyakkyawar mace ce na wuce misali, shiyasa dukkansu suke kyawawa tamkar su suka yi kansu, tana da tsawo sosai, har ta É—ara daddynsu tsawo, a takaice dai wannan blue eyes da tsantsar kyau na wuce misali, tsawo zara zara da su, a wajen mummyn Dr William suka gado shi, ga black cuirly hair sosai, gashin nata kuma har kugunta ta baya.

Da sauri mum É—in nasa ta ce "My son, what brought you here? What are you doing in this dirty place? What happened to your eyes?".

Harara ya wurgawa uncle Herry dake tsaye a gafe kafin ya ce "What are you doing here Herry?".

Tun bai gama rufe baki ba Uncle Herry ya juya ya bar wajen, dan fa yasan É—an uwan nasa sam bashi da sauki.

Dawo da kallonsa a kan dad da mum É—in nasu ya yi, É—an É—aure fuska ya yi yana faÉ—in "Mum why are you disturbing your self like that? Ni fa ba yaro ba ne, you have to be.........." Katse shi ta yi da cewa lallai shi yaro ne a wajenta, kuma ya zo su tafi gida.

Make mata kafaÉ—a ya yi a kan shi dai ba zai tafi ba, daga karshe ma sai ya ce suje gidan yana zuwa. Sun yi sun yi ya gaya musu me yake yi a cikin wannan kurkukun gidan, local da shi. Amma ina, sam yaki faÉ—a, sai ce musu ma ya yi, idan basu tafi ba, shi zai yi kuka tun da haka ne.

Basu da zaɓi, dole su tafi, dan suna mugu mugun son farincikin ɗan nasu fiye da komai a duniyarsu, su ne nan suka ɓata shi da kuɗi, suka sanya yana yin abin da ya ga dama, ya taka kowa, babu wanda ya isa ya taka mashi birki.

Bayan sun tafi sai ya dawo cikin É—akin, saman bed É—in ya koma ya zauna yana tunanin abubuwan da suka faru a tsakaninsa da gwaggo tun daren jiya zuwa yanzu, mamakin kansa yake yi, tamkar ba shi ba, mace ta canza shi a lokaci guda. A haka ta fito ta same shi, jikinta na É—aure da towel white color mai É—an girma zuwa gwiwa.

Binta da kallo ya yi babu ko kyaftawa. Har ta kammala shafa Lotions nata yana ta kallonta, da yake sam ita ma bata san kunya ba, sai ya zamana ko a jikinta, bata damu dan yana cikin É—akin ba, haka ta shafa duk abin da zata shafa a gabansa kafin ta nufi dressing room na cikin É—akin nata. Sai da ya ga shigarta dressing room É—in ne ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya tare da jingina kansa da jikin headboard na bed É—in yana sauke numfashi a hankali hankali.

After some minutes. A haka ta fito ta same shi. Shirye take cikin wandon jeans baki da riga mai ƙaramin hannu pink color, ta yi matuƙar kyau sosai, ta ɗaure gashin kan nan nata a tsakiya, sai tashin fitinannen kamshi take yi. Kamshin perfume ɗin nata ne ya daki hancinsa ya sanya shi ɗagowa yana bin in da ya ji kamshin da kallo.

Wow ya furta da É—an karfi tare da É—aga mata gera É—aya. Murmushi kaÉ—an ta yi hannunta na rike da dadduma da hijabi. Ta kusa da mirror ta je ta shimfuÉ—a daddumar tare da sanya hijabi ta tsaya ta tada sallah. Zuba mata idanu ya yi yana kallon yanda take sallar babu ko kyaftawa.

Har sai da ta kammala kaf a kan idanunsa tamkar mai karanta wani abin, bayan ta kammala ne ta miƙe tare da naɗe daddumar ta nufo in da yake zaune. Cikin sanyin murya ta ɗaga mishi gaisuwa tamkar mijinta na sunna.

Fuska ba yabo ba fallasa dan baya dariya, haka ya amsa mata. Duba kyakyawan ƙaramin watch dake ɗaure a hannunta ta yi tana faɗin "Dr muna da class karfe 9:30 fa, yanzu kuma 8:30, remain 1 hour, ya kamata ka je gida ka shirya, sai mun haɗu a school ko?".

Nisawa ya yi tare da miƙewa tsaye, nan take ta dawo tamkar Rimsha a gaban Lion, dan ya fita tsawo sosai shi ma, kamar dai Lion da Rimsha, gara ma Dr William da gwaggo, ratar shekaru babu yawa a tsakaninsu, shi kuwa Lion ratar shekaru dake a tsakaninsa da Rimsha suna da yawa. 31 to 32 years Lion yake da shi, ita kuma Rimsha 14 to 15 years, kun ga kuwa da akwai rata sosai a tsakaninsu, so gara Dr William da gwaggo.

"Bana jin zan iya tafiya na barki, dan ban gaji da ganinki ba". Ya faÉ—a a sanyaye, shi kansa baya sanin time da wasu kalamai suke fitowa daga É—an bakinsa nan, bawan Allah ya faÉ—a tarkon mace lokaci guda, ji yake yi tamkar ba zai iya tafiya ya barta ba.

Juya idanunta sama ta yi tamkar mai tunani. Shiru ya yi yana ta kallonta.

"Ai zamu haÉ—u a school ko?". Gera É—aya ya É—aga mata ba tare da ya yi magana ba, idanuwansa a shanye kamar wanda ya yi shaye shaye.

"Tom shikenan ka je kawai kada ka damu ka ji my Dr?". Dogon numfashi ya ja tare da buÉ—e mata hannayensa a kan ta zo su yi bye bye.

Da sauri ta faɗa jikin nasa tana ɗan murmushi, rungumeta gam ya yi na ƴan mintuna kafin ya ɗan sassauta riƙon nata da ya yi tare da ɗago haɓarta suna fuskantar juna.
Chapter 7 · 0% Book details