← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 168

Sashe 88

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin serious ɗan uwan nasa yana a cikin damuwa ne yasa ya kawar da duk wata shiririta tare da gyara nutsuwarsa ya tattare hankalinsa wajen guda, cikin sanyin murya ya ce "Sorry our Lion, ba laifinka bane, kuma ba laifin Rimsha bane, dama kowace mace sai ta fuskanci makamancin haka, amma ba irin naka ba, naka ai ya wuce tunani, fatana dai yanzu Allah ya bata lafiya yasa kuma mun samu baby's, yasa kwallo uku kamar mu ka zura a raga........" Kasa karisa maganar ya yi sakamaƙon wani irin kallo wanda ya fi harara kuna Lion ɗin ya wurga mashi, dan kawai ya yi maganar babys, idan baku manta ba shi fa Lion baya son yara, sam sam baya son hayaniyarsu ko kaɗan, so baya shiri da duk wanda zai yi mashi addu'ar samun yara, a tunanin Areef tun da yanzu sun kai ga yin aure, wata kila Lion ɗin ya sauya yana son yaran a yanzu, bai san cewa babu abin da ta sauya ba, har yanzu yana a kan bakarsa na baya son yara. Tashin sense lallai akwai kura ba kaɗan ba.

"Sorry our Lion ba baby's nake son cewa ba, mantawa na yi, sai ya yi mani kamar da Aseef muke hira ne".

Shiru ya yi bai sake tanka mashi ba, dan shi kaɗai yasan me yake ji. Sosai Areef ɗin ya yi ta rarrashinsa tare da kwantar mashi da hankali, har karfe 8 ya cika, sannan ne ya miƙe tare da yi wa Areef ɗin sallama, ya katse kiransa ya nufi cikin gida.

Kai tsaye bedroom nasa ya nufa. Bakinsa É—auke da sallama ya shiga, a nan ya isko gwaggon a zaune kusa da Rimshar, har yanzu dai Rimsha ko motsawa bata yi ba.

Wajen bed É—in ya kariso, barka da safiya ya yi wa gwaggo, yana magana yana kallon face É—in Meeshan tasa, har yanzu dai tana nan yadda take ba sauyi.

Miƙa mashi takardan duk abin da zai sayo mata ta yi, tana mai karfafa mashi gwiwa tare da kwantar mashi da hankali, ta lura zai iya jure komai na rayuwa, amma banda damuwar TRIPLETS and Rimsha, daga kanta ita gwaggon, TRIPLETS nasa da kuma Rimshar sune rauninsa a rayuwa.

Karɓa kawai ya yi ya fito waje, kai tsaye bedroom na uncle T ya nufa, dan su tafi a tare. Ita kuma gwaggon mikewa ta yi ta fita izuwa nata bedroom ɗin, saboda gari ya waye tasan yanzu Jehan zata zo ta fara zuba mata shagwaɓa, so bata son su san abin da ya faru da Rimshar ma bare su kuma su tsorata.

Tana shiga bedroom nata Jehan ɗin ta shigo bakinta ɗauke da sallama tana aikun turo baki, kayan barci riga da wando dogaye ne a jikinta, launin pink color masu matuƙar kyau, ga cup mai bala'in kyau a hannunta,

A dubu ɗari gwaggon ta ce "Jehan mekike sha?". Ba tare da ta kalli in da gwaggon take ba ta bata amsa da "Abin da kuka haɗa mana nan ne, ba dama kafin mu ci komai da safe shi muke fara sha ba? Wai gwaggo ko dai kin fara tsufane waɗan nan idanun naki manya manyan kamar na Dr Salman ɗin nan sun dai'na gani? Ka gansu manya manyan da su kuma ace baki gani sosai, sai na kai ki asibiti". Ta kai karshen maganar tare da hayewa bakin bed ta zauna tana ƙoƙarin kai cup ɗin ɗan bakinta.

"Ke dakata tukun nan". Gwaggo ta faÉ—a a hanzarce. ÆŠago fararen idanuwanta ta yi tare da saukesu a kan face É—in gwaggon, fuskarta cike da mamakin meyasa ta dakatar da ita daga sha kuma.

Zama a gefenta gwaggon ta zo ta yi, cikin sanyin murya ta ce "Jehan kada ki ɓoye mani, faɗa mani gaskiya, shin kun taɓa kwanciya ta sunnah da Areef ne?".

A É—ari ta zaro ido tana kallon gwaggon, kafin kuma ta tuntsure da dariya tana faÉ—in "E lallai yau dai gwaggo bake bace, Queen ta canzo mana ke, au ashe Queen É—in ta mutu ma, yanzu gwaggo kawai sai ki tambaye ni?".

Harara gwaggon ta wurga mata kafin ta fara magana "Ke bada wasa nake yi ba, faÉ—a mani gaskiya yanzun nan".

Girgiza mata kai ta yi tana bata amsa da "A'a bamu taɓa ba......."
Ai tun bata kai karshen maganar ba gwaggon ta kwace cup É—in daga hannunta tana faÉ—in "Daga yau kada ki kara shan wannan abin, komai ma da muka haÉ—a kada ki sake sha, maza jeki duba idan Akila ta tashi daga barci ki kira mani ita".

Mamaki sosai ne ya bayyana a saman face nata, tambayar kanta take yi shin meyasa gwaggo zata hanata sha? Ita da kullum take takura masu a kan su sha maganin nan sosai, kada su tsallake kona minti É—aya, shi ne yau kuma zata hanata? Abin da mamaki.

"Akila nace ki kira mani ne ko kuma tunani na ce ki shiga yi?". Turo baki ta yi kafin ta ce "Gwaggo Akila fa bata tashi daga barci ba, kin sani sai almost 12 take tashi fa".

Da Akila da Aseef dai sarakan barci ne, su ne last na tashi barci a gidan, da daddare kwana suke yi manne da waya suna kashe juna da kalaman love, duk iya soyayya na Areef ya basu hanya, dan fa su macewa juna suke yi, sai su kwana makale da waya, sai anyi sallar asuba suke samu su kwanta, shi ne idan suka fara barci sai 12 na rana, suna tashi kuma ko abinci basu nema suke sake makale waya, wani lokaci ma suna wayar video call suna breakfast, Aseef and Akil halinsu babu wani banbanci, duk zani ne ta tattada muje, shagwaɓaɓɓune na gasken gaske, na kin karawa, haka zasu yi ta zubawa juna kukan shagwaɓa kamar ba gobe, kuma haka zasu rarrashi juna, da yake sun saba ma abin ya zamto masu jiki.

"Gwaggo ina son muje shopping, za'a saya mani kaya da kuma waya, mafiya yawan kayan da nake sanyawa a gidan nan fa kayan Rimsha ce, to ni gaskiya na gaji da saka kayanta". Tana magana tana haÉ—e gerar sama da kasa.

"Dama basu yi maku lefe bako?". Cewar gwaggon. "Menene kuma lefe?". Ta tambaya tana bin wayar gwaggon dake ringing da kallo.

"Lefe kayan da maza suke sayawa mata kafin aure mana". Ta bata amsa tare da jawo wayar tata dan ta ga wanenen yake kiranta?.

"Mu babu wani lefe da suka yi mana, kawai ni gwaggo ki kira daddy a waya muje shopping hai, ina ruwana da wani lefe? Mu ba muna da kuÉ—in sayan kayan ba? Dole sai su ne zasu saya mana?". Ta kai karshen maganar tana turo baki tare da É—aure fuska.

Duk abin da ta faɗa Areef ɗin yana jinta, saboda shi ne ya kira gwaggon a wayar, kuma already ta yi picking call ɗin, ga shi da English suke magana, so ya ji komai. Jehan sarkin iyayi da nuna isa, wato ita lefenma bata ce Areef ya yi mata ba, daddynta yana da kuɗi, dan haka su sun wuce ayi masu lefe. (Ni ko nace ba shakka duk wannan izzar da isar tata tana taka bakin gate na farko na gidan Lion na Washington zata zama ƴar kauye, dan gidansa ginine da babu kwatankwacinsa a Nigeria, maƙudan dukiya aka narka na kin karawa, Daula ce guda, idan kana cikinta sai ka yi tunanin ba'a duniya kake ba, Allah ka yi mana arziki mai albarka mai amfani da zamu taimaki Al'ummar musulmi Al'ummar manzon rahma manzon tsira.)

"Good morning momma". Ya faÉ—a cikin sanyin murya, duk da lokaci time na agogo namu da nasu daban daban, amma ratar bata da yawa sosai, kuma ya san safiya ce yanzu a Nigeria, shiyasa kawai ya ce mata good morning.

"Morning how are you and my auta?". Nisawa ya yi kafin ya amsa mata da "Autanki yana can yana aikin barci da ya saba, Momma please help me give my baby this phone, jiya taki yin magana da ni, fushi take yi da ni, dan banzo ba".

Kallonta gwaggon ta yi da mamaki a saman face nata, wato Jehan ta cika ƴar duniya, sai tazo ta nuna masu tamkar bata damu da Areef ɗin ba, tamkar bata son shi, ashe ma saboda bai zo ba har da yin fushi da shi ta ɓata rai, kai Jehan ba'a iya mata, kuma baka gane mata sam sam, ta sanya bawan Allah a cikin tunani, kuma sarai ita ma abin yana damunta, kawai dakiya ce, ita ma jiya ta ji a jikinta na rashin wayar da basu yi da daddare ba, ta dake ne ta nuna kamar ba komai, dan ma kada a ra'inata. (Allah mai iko, Jehan duniya, ta iya dakewa ta shanye abu kamar Lion, sai ta yi kamar bata san komai ba, alhalin tana azabtuwa daga ta cikin zuciyarta 😂)

Miƙa mata wayar gwaggon ta yi tana faɗin "Karɓi za'ayi magana dake". Harara ta wurga wa wayar tana faɗin "No need".

Nisawa ya yi kafin ya ce "Please my baby, ya isa haka wahalar da ni É—in kin ji, i can't agree irin wannan avoiding nawan da kike yi, ina shan wahala sosai fa, wai baki jin tausayi nane?".

Wani irin sanyi ta ji a ranta na jin muryarsa, har da sauke nauyayyar ajiyar zuciya, amma saboda taurin kai sai ta ce ita fa ta gama magana kenan ba zata karɓi waya ta yi magana da shi ba.

Gwaggo baiwar Allah tana ganin rayuwa wajen ƴaƴan nan nata da matansu, kowa da kalar tasa rashin kunyar. Katse kiran gwaggon ta yi tare da fara yi wa Jehan ɗin nasiha a kan ba'a yiwa miji haka, ta sani Allah zai kamata, tun jiya ta sanya mijinta cikin damuwa, ya kwana cikin ɓacin rai, sannan yau da safe ma ta tashi ta kara mashi wani? Bata da hankali ne? To wlh ta bi duniya a hannu.
Chapter 88 · 0% Book details