← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 168

Sashe 110

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Bana magana biyu, idan nayi na farko shikenan, in aka matsa sai na yi na biyu, to sai dai hannuna ya sake maimaitawa mutun, so is better for you da ki bani amsa ba ɓata lokaci, because i have a lot of things to do, time nawa yana da mahimmanci a gareni!". Cewar Lion, cikin wannan sexy voice ɗin nasa dai ya sake yin magana, hankalinsa a kwance.

"Who are you? And what do you want?!". Sir Arvin ya tambaye shi cikin É—aga murya.

Tamkar bai san da tsayuwarsa a wajen ba, dan bada shi yake magana ba, kuma kunsan halin Lion, idan ba da kai yake abu ba to ko kai uban waye baya bi ta kanka, bama ka ishe shi kallo ba, so yanzu dai da uwarsa Cherish yake yi ba da sir Arvin É—in ba, saboda haka bai ga dalilin da zai sa ya kula sir Arvin É—in ba!! Babbar magana.

Ganin kamar bata da niyar yin magana ne yasa ya miƙe tsaye tare da harɗe tafukan hannayensa ɗaya cikin ɗaya yana ɗan shafe juna, kafin ya saci kallon sir Arvin ɗin dake ta gefensa ta wutsiyar idanu, sannan ya ɗauke Dr Cherish ɗin da wata iriyar mari wadda ta sanyata komawa saman chair ɗinta ta yi wani irin zaman ƴan bori.

Nan take ta fara ganin wani irin duhu duhu da wasu yana suna gifta mata ta cikin idanuwanta, kunnenta ta gefen da ya mara dai ya tashi a aiki, dan ta dai'na jin sautin komai ta gefen yana tashi, duk da tana zaune sai da ta kalli wani irin ajijiya mai karfi yana wani kwasan chair ɗin nata, da alama ta leƙa lahira ne ta dawo, tama yi ƙoƙari da bata suma ba, saboda zaratan maza ma basu iya shanye marin Lion bare ita mace, ko da yake dama ba zai mareta kamar yanda yake marin maza ba, zai sassauta mata, dan kada ta mutu bai sami amsar da yake so ba!!.

(Oh ni PRINCESS FATEEMA ya zan yi da karfin hali irin na Lion ne?🤔 Kasamu mata ka bata lafiyayyen mari a cikin office nata dake kewaye da security's babu ko ɗar ɗar? Bugu da kari a cikin kasarsu? Sannan a gaban ɗanta? Tana matsayin babban likita uwa ga jama'a?😒 Dole mu nemawa Lion sauki wajen Ubangiji, in dai karfin hali da nuna isa da izza ne daga kansa an rufe kofa, wato shi ko shakkar shiga cikin kasar tasu ma bai yi ba?🤔 Kai lamarin Lion sai shi wlh, sai kuma Rimsharsa ƴar baiwa, dan idan baka da baiwa ba zaka iya ɗaukar zama na minti goma da shi bama)

A fusace sir Arvin É—in ya yi kansa, dama kuma yasan za'ayi hakan, shiyasa ma ya saki kallonsa kafin ya mari Dr Cherish É—in, ya kalle shi ne dan ya ga a yadda yake, saboda ya ji daÉ—in bashi nashi marin da kyau idan ya nufo shi, dan yasan É—an nata ba bari zai yi ba.

Sai da ya bari sir Arvin É—in ya iso gare shi da nufin ya bashi mari shi ma, sai ya rike hannun nasa tare da É—auke shi da marin shi ma, dan idan ba hakan ya yi masu ba, ba zasu yi mashi abin da yake so ba. Babban magana Lion da marin sir Arvin.

Bayan ya mare shi É—in ma sai da ya haÉ—e hannayensa dukka biyu ta baya ya rike da hannunsa É—aya, dama na gaya maku shi sir Arvin kamar Aseef yake, bashi da cika sosai, hakan yasa Lion É—in ya rike hannayensa da hannunsa guda, cikin wata iriyar murya a kwance cikin nutsuwa ya ce "Ka nutsun mani, idan ba haka ba zan turaka in da ba'a dawowa, da uwarka nazo yin magana ba kai ba, so be careful!".

Turo kofar office ɗin da aka yi ne yasa Dr Cherish ta dawo cikin hayyacinta, shi kuma Lion hannu ya kai ya ɗauko wani kyalle fari da yake kusa da Dr Cherish ɗin ya ɗaure hannun sir Arvin ɗin ta baya, har lokacin sir Arvin ɗin bai dawo dai'dai na marin da ya sha ba, jiri ma yake gani, sai ya ji kamar ba shi ba, kamar ba'a duniya yake ba, ya maru ba karya, bawan Allah wannan jajir ɗin kumatun nasa bata taɓa shan mari ba sai yau, yau ɗin ma kuma marin Lion, ai dole ya faɗa wani yanayi na fita cikin hayyaci.

Bayan ya kammala É—aure shi ta wutsiyar idanu ya kalli wanda yake shigowa É—in. A dubu É—ari ya saki sir Arvin É—in tare da juyowa da kyau ya kalli mutumin da ya shigo É—in, shi kuma sir Arvin saboda yana É—aure zubewa kasa ya yi a saman gwiwowinsa da Lion É—in ya sake shi.

Cikakken Dr ne, kyakkyawan Bature tas da shi, yana sanye da suit masu tsada launin white color, ya ɗaura rigar aikinsa a sama, idanuwansa na sanye cikin white Medicated glass mai shegen tsada, hannunsa na ruke da wasu files dayawa, dark black curly hairnsa a ɗaure a bayan wuyarsa, sai sheƙi yake yi. From head to toe Lion ya fara kare mashi kallo, bai tsayar da kallon nasa a ko'ina ba sai a cikin dara daran blue eyes na wannan Drn, ɗan ciza lips nasa ya ɗan yi kafin ya dukar da kansa kasa yana wani irin sauke numfashi mai wuyar fassaruwa.

"Cherish what's happening here?". Cewar wannan Dr da ya shigo yanzu, ya yi tambayar yana mai do da kallonsa a kan Lion, cikin hanzari ya sake kai kallonsa a kan Arvin da yake durkushe a saman gwiwowinsa.

Zaro idanuwa waje sosai ya yi, cikin sauri ya ce "Cherish who is this guy that look like our Arvin over?".

Kasa magana ta yi, sai zare idanuwa take yi. Matsowa kusa da table ɗin nata Lion ya yi, cikin tafasar jini ya ɗago da idanuwansa da suka yi jajir, ya saukesu a kanta, fuskarsa tamkar wanda aka aikowa da sakon mahaifiyarsa ta mutu, jikinsa har wani irin tsuma yake yi, kansa na wani irin sara mashi, yanzu ko ba'a bashi amsa ba ya sami amsarsa, domin wannan likitan da ya shigo yanzu ba kowa bane face ainahin Dr William, kuma ga dukkan alamu mijin Cherish ne, a yanzu komai ya bayyana, abu ɗaya Lion yake son sani, tayaya aka yi hakan?!! Shi dai yasan Dr William a wajen matsafan can yake, to ya aka yi ya dawo wajen su Cherish? Shi fa Lion dama ya zo bincike ne a kan Cherish ta gaya mashi ina ne gidan tsafin kakan nasu, dan a binciken da ya yi tana da masaniyar in da gidan yake, kuma tabbas before ta taɓa aiki da su, bai taɓa kawowa ransa Dr William yana tare da ita ba, to ya aka yi hakan?!!.

"How!!! How you did all this?!! How Cherish?!!!" Cewar Lion É—in, ya faÉ—a cikin É—aga murya.

Tsawa Dr William É—in ya daka mashi a kan waye shi? Kuma waye ya bashi dama ya shigo cikin office na matarsa ya yi magana da ita? Har kuma ya É—aure mashi yaro da kyalle?.

Wani irin mahaukacin tsawa Lion ɗin ya dakawa Cherish ɗin har sai da ya sanyata ta buɗe baki babu shi, sam bai bi ta kan Dr William ɗin ba, yanzu daga bakin Cherish yake son jin magana, shi kuma sir Arvin yana ta ƙoƙarin kwance hannunsa dan ya yi faɗa da Lion ɗin a kan iyayen nasa da yake ƙoƙarin cinwa zarafi, duk cikinsu an rasa wanda zai iya kiran security's, da alama duk jini ne yake fusgarsu yasa suka kasa kiranwa Lion ɗin security's.

Murya na kerma Cherish É—in ta ce zata gaya mashi gaskiyar abin da ya faru, ya zauna. Cikin tsawa ya ce mata ba zai zauna ba, babu ruwanta da shi, kawai ta gaya mashi gaskiya ko kuma yanzu ba sai anjuma ba ya kasheta har lahira!!.

Cikin sauri Dr William ya tambayeta wai wanene Lion É—in nan? Daga ina ta san shi?.

ÆŠaga wa Dr É—in hannu ta yi, alamar ya yi shiru kawai su saurareta su ji.

Shirun suka yi, suna sauranta, ita kuma zama ta gyara tare da fara yin magana kamar haka.
Chapter 110 · 0% Book details