← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 168

Sashe 55

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin su fito Aseef ya kashe waÉ—an nan mutane dukka, yana tsaye a harabar wajen yana aikin gyara agogon hannunsa da suka kwance mashi a wajen faÉ—a, ko a jikinsa, bai sha wahalar faÉ—a da su ba sam sam.

Nunawa su Dr Salman Aseef ɗin Areef ya yi yana faɗa masu su je wajensa, shi kuma bari ya nemo sauran jama'ar da suka zo ɗauka. Ba musu suka amsa da to, suka wuce izuwa wajen Aseef ɗin, shi kuma Areef ya sake komawa yana leƙa ɗakunan.

Suna zuwa Aseef ya rungumi Dr Salman yana faɗin "Welcome ɗan tsoho". Duk da cewa Dr Salman bai san su waye su ba a gare shi, bai hana ya rungumi Aseef ɗin ba shi ma. Yana ƙoƙarin yiwa Aseef ɗin magana ne suka jiyo muryar Areef daga ɗaya daga cikin ɗakunan dake wajen yana faɗin "Aseef come and see something".

Kallon Dr Salman Aseef É—in ya yi. "ÆŠan tsoho ku jirani a nan kada ku motsa ina zuwa". Ya kai karshen maganar tare da sakin Dr Salman É—in, da sauri ya nufi in da suka jiyo muryar Areef É—in.

Yana zuwa ya faɗa cikin ɗakin, sai kallonsa Dr Salman yake yi har ya kurewa ganinsa, ɗan tsoho yaga rayuwa iya ganin idanunsa, baki ma ba zai iya faɗar irin abin da Dr Salman ya fuskanta na kalubalen rayuwa ba, sai dai muce Allah ya kuɓutar da su.

Aseef yana faɗawa cikin wannan ɗaki me zai gani? Heartbeat nasa ne a ɗaure cikin wasu sarkoki. Wani irin sanyi ya ji a ransa, da sauri ya karisa gareta, Areef yana ta ƙoƙarin yanda zai yi ya kwance waɗan nan sarkokin, shi kuwa Aseef ɗin yana zuwa ya rungumota yana faɗin ya yi missing nata over. Ita kuwa tana ganinsa ta sa mashi kuka, yi take yi babu kama hannu yaro, haka ya hau rarrashi, sai gaya mashi abin da ta gani da abin da suka yi mata take yi, baya sauraronta ma, shi dai burinsa kawai ta yi shiru, amma ta kiyi sam sam, shi kuma Areef yana ta ƙoƙarin yanke waɗan nan sarkoki.

Can kuma ko me ya tuna, sai ya fara karantawa sarkokin karatun Alqur'ani mai girma, nan take suka fara kwancewa suna zubawa kasa, kan kace me sarkokin duk sun zama gari, hakan kuma tasa É—akin ya yi wani irin haske, sannan kuma ya fara wani irin rugugi tare da surutai da wasu irin muryoyi marasa daÉ—in ji.

Cikin hanzari Areef É—in ya ce "Kai Aseef da matsala fa a dakin nan, ku wuce da wuri mu fita".

Sam Aseef ɗin bai kula shi ba, ya rungume Heartbeat tasa suna kashe juna da shagwaɓa, su gabaɗaya ma sun mance a ina suke, har lokacin sai kuka take zuba mashi, shi ma ya biye mata suna wannan aiki dai da suka saba, wanda already kun san halinsu idan suka haɗu, shagwaɓa babu kama hannun yaro.

"Aseef wai ba zaka barta sai mun fita daga É—akin ba?".

Ko ajikinsa, babu tsoro ko ɗigo a tattare da shi, cikin kwanciyar hankali ya ce "Kai Areef kasan tun yaushe ban yi kissing nata bane? Kai ba zaka bar mutun ya sakata ya wala ba, Allah ba zanzo ba sai na gama kissing nata har na ƙoshi".

Girgiza kai Areef ɗin ya yi tare da nufarsu, Aseef sai ya sa an yi masu kisan walaƙanci sannan hankalinsa zai kwanta, ban da iskanci ma irin tasa, ana ta rai waye kuma yake ta wani kiss? Ya bari su rayu mana, daga baya ayi komai, yana ganin yanda komai yake ƙoƙarin lalace masu, ga shi har yanzu basu ma san ina Lion yake ba tukunna. Yana zuwa ya ja hannun Akilar yana faɗin "Idan kika biyewa Aseef duk sai mun mutu kamar dabbobi a nan, ke daɗi masoyi ko?".

Janyota Aseef É—in ya sake yi yana faÉ—in "Wai kai ka bari mana, ka sani ne ko kiss na karshe zan yi mata, idan bamu kai ga fita ba aka kashe mu kamar yanda aka kashe sauran fa? Ni ka barni na yi abinda zan yi Hai........" Bai rufe baki ba suka fara jin jijjigar ginin É—akin, alamar suma ruguje É—akin ake son yi da su a ciki, tamkar yanda aka yi wa su Mark kenan.

Ihu Aseef ɗin ya kurma tare da shagwaɓe murya yana faɗin "Wayyo Areef mun shiga uku, shikenan zamu mutu ba tare da Heartbeat ta haifa mani baby's ba, wayyo ni Aseef naga ta kai'na".

Wani irin harara Areef ɗin ya wurga mashi. Aseef ɗin nan mugun ɗan rainin wayo ne wlh, ji yanda yake kukan shagwaɓa kamar ba yanzu ya gama jibgan karti maza a waje ba!.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

E15

Date: 25/4/2024

Wani irin harara Areef ɗin ya wurga mashi. Aseef ɗin nan mugun ɗan rainin wayo ne wlh, ji yanda yake kukan shagwaɓa kamar ba yanzu ya gama jibgan karti maza a waje ba!.

"Areef yanzu me abin yi, ni fa wlh bana son na mutu". Ko kallon arziki Areef ɗin bai yi mashi ba, bare ya sa ran zai amsa mashi, hannun Akilar kawai ya ja suka nufi kofar fita da gudun gaske, da ya ga ba zata iya gudun bama, sai ya ɗauketa cak, shi kuma Aseef ɗin yana tsaye yana zuba kukan shagwaɓa.

Bayan Areef ya fita da Akila sun tsaya a waje ne, sai ya sauketa tare da dafa kansa yana faɗin "Dama na sani ai, Aseef our heartbeat kuma our headache, wato da gaske yana tsaye a cikin ɗakin kenan? Ya zan yi dole naje na lallaɓa shi ya fito, Heartbeat ki jirani a nan". Ya kai karshen maganar tare da juyawa da sauri ya koma cikin ɗakin.

Gabaɗaya bangon ɗakin sai ruguzowa yake yi, amma Aseef yana tsaye yana zuba kukan shagwaɓa, shi dole sai Areef ya zo ya rike hannunsa shi ma, a kan me zai kama hannun Akila kawai, wato yanzu sun fi son Akila a kan shi kenan? Shi ne fushin da yake yi.

Da sauri Areef ɗin ya dawo cikin ɗakin, hannunsa ya zo ya riko yana faɗin "Shikenan muje to". Bubbuga kafa ya fara yi yana faɗin "Yanzu ka dai'na sona, sai da ka fitar da Heartbeat shi ne ni zaka ce nazo daga baya, Allah ba zan yarda ba, ni babu in da zanje, kawai ka barni na mutu tun da kun dai'na sona........". Bai kai karshen maganar ba bangon ɓangaren hagu ta ruguzo. A dubu ɗari ya rungumi Areef ɗin yana faɗin "Wayyo daddyna, wayyo my Lion, na shiga uku zamu mutu, Areef ka ceceni bana son mutuwa".

Gabaɗaya kan Areef ya kulle, wai shin Aseef ɗin nan wani irin mutun ne? Yanzu ka ganshi cikakken jarumi, anjuma kuma ya koma shagwaɓaɓɓe na kin karawa, ji yanda yake kukan baya son ya mutu, ya zo su fita kuma ya ce bai san wannan ba, shi ya yi fushi saboda an fara fitar da AKILA, yanzu kenan an daina son shi.

Shi ma Areef É—in rungume shi ya yi yana rarrashinsa a kan ya yi hakuri su tafi to. Bai kai ga rufe baki ba kamar daga sama ya ji Aseef É—in ya sunkuce shi, ya É—aga shi sama sun yi waje a guje. Suna fita É—akin ya rufta mai gabaÉ—aya.

Bai sauke ɗan uwan nasa a ko'ina ba sai a kusa da Akila dake tsaye tana faman sharar kwallah. Mamaki ya hana Areef ɗin yin wani kataɓus, yau kuma ko a ina Aseef ya samo karfin ɗaukarsa kamar ɗan baby kuma oho? Abin mamaki baya karewa.

Shi kuwa Aseef ɗin yana sauke Areef ɗin sai ya faɗa jikinsa yana mai cigaba da kukan shagwaɓarsa kamar ba shi ne yanzun nan ya gwada wata zazzafar jarumta ba.

Ture shi Areef É—in ya yi ya nufi wajen su Dr Salman yana faÉ—in "Heartbeat dama kayanki ne, kin fi kowa sanin halinsa a yanzu, sai ku fama, ki rarrashe shi, ni bari na nemo maku hanyar fita daga wannan bakin kazamin gidan, ku fita, idan ya so zamu biyoku daga baya". Ya kai karshen maganar dai'dai lokacin da ya karisa wajen Dr Salman.

Matsowa Akilar ta yi ta faÉ—a jikin Aseef É—in tana mai cigaba da zuba mashi kuka babu kakkautawa. Rungumeta sosai ya yi tare da dai'na nashi kukan ya hau rarrashinta, ta tsorata sosai baiwar Allah, ta sha wahala, duk ta fita a hayyacinta, a haka ma fa dan tana matsayin jika ga Queen É—in kenan, ba dan haka ba, da sai yaya? Taga kaÉ—an daga cikin abubuwan da Rimsha ta gani, a gaban idanunta aka fasa cikin wasu mutane biyu aka É—ebi wasu abubuwa, a gaban idanunta aka shanya gawa kamar busasshen kifi, a gaban idanunta aka yi abubuwa da dama, ita ma dan Allah yasa tana da tsawon kwana ne, da ita ce a kan layi yanzu, ba dan zuwansu Aseef ba, to da ba makawa ba zata kai gobe ba.
Chapter 55 · 0% Book details