← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 168

Sashe 155

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasa fita waje ta yi, sai ma kara matsowa da ta yi tana ƙoƙarin riko Jehan ɗin.

Wani irin nishi Jehan ɗin ta sake yi tare da riƙo wuyar rigar Lion ɗin, dan ya fi kusa da ita a kan Rimshar, Rimsha tana ta gefenta ne, shi kuma yana tsungunne ne a ta gabanta in da ya ɗauki baby, hakan yasa da azaba ta yi azaba bata san lokacin da ta damko wuyar rigarsa tana sakin wani irin numfashi mai matuƙar razanarwa ba, tamkar mutuwa zata yi, baiwar Allah.

Cikin zafin nama Lion ɗin ya janyon duv ɗin a dubu ya kwnatar da babyn tare da kai hannunsa dukka biyu ya riƙo shoulders ɗin Jehan ɗin yana mai dakawa Rimsha tsawa a kan ta fita a ɗakin kamar yadda ya faɗa mata tun farko.

Wannan tsawa da ya daka mata ya yi dai'dai da faÉ—owar baby a karo na biyu, ita kuma Rimshar tsabar tsorata da tsawar, sam bata san lokacin da ta kwasa a guje ta bar room É—in ba, daga ita sai towel a kirji.

Yau dai Lion da baya kaunar yara a rayuwarsa, saboda kaunar Areef da yake yi tasa ya karɓi haihuwar Jehan da kansa, shi da ya ce ko kallon yaran baya son yi, sai ga shi da Allah ya tashi kamasa a hannunsa aka haifo yaran Areef, daga karshe ma gabaɗaya jikinsa ta yi dama dama ta yi wanka da jini, dan kuwa ba ƙaramar damka Jehan ta rinƙa yi mashi ba, saboda azaba, babynta na uku dana huɗu kam ma kusan a jikin Lion ɗin ta haifosu, duk ta fita daga cikin hayyacinta, hasalima bata san waye ne a wajen ba, Allah ya bata haihuwar QUADRUPLE a saukake, dan kuwa a saukake za'a ce, duk wannan azaban da ta sha wlh ya zo mata da sauki, saboda ba kowace mace ba ce zata iya haihuwa ƴan uku da kanta ba ma bare QUADRUPLE, wannan sai ikon Allah da ya bawa gwaggo da Jehan ɗin damar yin hakan, idan baku manta ba, ita ma gwaggon hakan ce, Jehan ƴar ɗakinta ta yi gado sosai sosai, a komai ta gaji gwaggon, bata rage komai ba abinta.

Duk taurin zuciya irin ta Lion wlh sai da idanunsa suka ciko da kwallah, ya yi matuƙar tausaya mata, dan daga karshe ma sai da ya bata iskar bakinsa ta iya cigaba da numfashi, a haihuwar na karshe ta kasa samun numfashin da zai riketa ta iya haifar baby, sai da Lion ɗin ya tallafa mata, ga shi su gwaggo basu kusa, dan gwaggo ma tana can sama hawa ta karshe ita da Josephine suna tsara yadda tafiyarsu Nigeria and Dubai zai kasance, sam bata kawo cewa haihu zai zowa Jehan ɗin a satin nan ba, a nata kissafin sai cikin next week, shi ne yasa suka ɗan matsa kusa da ita.

A lokacin da Rimsha ta fita daga bedroom ɗin, kai tsaye bedroom na gwaggon ta nufa, sai dai ko da ta je bata sami kowa ba, abin ku da yarinta, a maimaƙon ta fita ta nemi gwaggon a cikin gidan, dan ta gaya mata halin da ake ciki, sai kawai ta haye gado tana kuka tare da addu'ar Allah yasa kada Jehan ta mutu, Allah yasa ba mutuwa zata yi ba.

Kada kuga laifin Rimsha, ita bata san menene haihuwa ba, yarinya ce, ko cikin ma bata san ya ake ji idan aka É—auke shi ba bare kuma tasan zafin haihuwa, ita dai kawai addu'a take yi Allah yasa kada Jehan É—inta ta mutu.

Shi kuwa Lion babu halin ya fita ya bar Jehan ɗin ya je naman gwaggo, duk dakiya irin tasa ya ji ba zai iya matsawa daga kusa da Jehan ɗin ba, dan yana ganin kamar idan ya matsa daga kusa da ita ya karya amanar da ya karɓa daga hannun Areef, yana ganin kamar yana barin wajen zata mutu kafin ya dawo, dan haka sai ya dakata kawai ya kasa tafiya, ya cigaba da riketa har ta haife cikin nata complete QUADRUPLE.

Baby na ƙarshe yana faɗowa ta saki jiki ta sume a jikin Lion ɗin, baiwar Allah.

Shi kansa Lion É—in wani irin nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sake shoulders É—in nata tare da zareta daga jikinsa.

A kasa saman duv ɗin kusa da baby's ɗin nata ya kwantar da ita, sannan ya miƙe tsaye, gabaɗaya ya yi wanka da jiki tamkar shi ne ya yi naƙudar.

Har zai bar ɗakin idanuwansa suka sauka a kan yaran, complete QUADRUPLE, suna kwance shiru. Lokaci guda ya ji wani irin tsananin son yara ya kama shi, barema yadda ya kalli yaro ɗayan nan mai matuƙar kama da Areef ɗin, sai ya ji ba zai iya tafiya ba, juyowa ya yi tare da sake tsugunnawa a gaban baby's ɗin.

Tamkar mai tsoron taɓa abu, haka ya kai hannunsa zai taɓa kumatun wannan baby mai kama da Areef ɗin, ga yaran da cibiya a jikinsu.

Ai kuwa yana taɓa fuskar yaron ya fara tsallara mashi ihu, a hanzarce ya miƙe kamar wani mara gaskiya, da sauri ya fice daga cikin ɗakin.

Kai tsaye bedroom nasu ya koma. Yana shiga ya hau cire kayan jikinsa, sam bai nemi Rimsha ba, saboda bata kanta yake ba a yanzu.

Sai da ya cire kayan ya rage daga shi sai short ne, ya ɗauko wayarsa ya rubutawa Sir Safwan sako a kan ya kira gwaggo Jehan ta haihu. Yana tura sakon ya wuce toilet abinsa, zuciyarsa a cike tab da tunanin baby's ɗin, sun yi matuƙar shiga ransa ba kaɗan ba.

Har ya yi wanka ya fito tunanin baby's É—in yake yi, sake sabon shiryawa ya yi, har lokacin kuma bai nemi Rimsha ba, yama mance da cewa ya daka mata tsawa.

Bayan ya kammala shirin nasa ne ya zo ya tsaya a gaban Tv dake manne a bangon yana kallon yadda su gwaggon suke ɗawainiya da baby's ɗin, yaran kawai yake ta kallo, ji yake yi kamar ya je ya sake taɓa yaron nan mai kama da Areef ɗin, tunanin Areef ya dawo mashi sabo gal.

Ya jima sosai yana kallon su gwaggon, har suka gama shirya baby's É—in suka kwantar da su a saman bed, sannan suka hau gyara Jehan É—in, gwaggon a tare da Josephine suke aikin.

Ganin cewa sun kawar da yaran daga idanun Camerar zasu fara gyara Jehan É—in ne yasa ya kawar da kallonsa tare da juyawa ya bar wajen.

Sai a lokacin ne kuma ya tuna da cewa ashe Rimsha bata a cikin É—akin, dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali kafin ya sa kai ya nufi waje.

Kai tsaye bedroom na gwaggo ya nufa, dan yasan a can kawai zai sameta.

Akila kuwa tana bedroom na Josephine ne, kada ku manta Aseef dai na Josephine ne, hakan yasa Josephine É—in ta ce a bedroom nata matar Aseef É—in zata zauna ta yi jego, dole gwaggo ta bar mata Akilar, Anaya kuma tana wajensu Brr Naurat, a can tafi yawan zama, su Aafia kowa tana part na mijinta.

Tana kwance kamar yadda ta shigo ta kwanta, bata motsa daga wajen ba sai ruwan hawaye da take yi.

Kasa kasa ya yi sallamar da babu wanda zai iya jinta face shi da ya yi kayansa, sai zuba uban kamshi perfume nasa yake yi tamkar ba daga É—akin haihuwa ya fito yanzu ba jimawa ba.

Tana ganinsa ta miƙe zaune tana mai cigaba da kukanta, hawaye suna gudu a saman face nata kamar ruwan famfo aka buɗe.

Ɗan tsura mata idanu ya yi kafin ya ƙariso wajen nata.

Kasa ta yi da kanta tana shesshekar kuka.

Yana isowa wajen ya miƙa mata hannunsa. Ɗago kai ta yi ba tare da ta yi magana ba, kuma bata iya miƙa mashi nata hannun ba.

Ganin hakan yasa shi ya kamo hannun nata tare da jawota a kan ta sauƙo kasa, dan baya jin kamar zai iya hawa saman bed ɗin gwaggon.

Ba musu ta sauko kasan. Cak ya É—auketa ba tare da ya yi magana ba. Bedroom nasu suka koma.

Bai direta a ko'ina ba sai a saman katafaren bed nasa. Zama shi ma ya yi a bakin bed É—in tare da jawota jikinsa yana faÉ—in.

"Ya isa kukan nan haka, calm down sarkin rigima".

Cikin dashewar murya ta ce.
"Noorish ina Jehan É—ita take? Bata mutu ba ko? Ya take?".

"Jehan É—inki bata mutu ba, sai dai ma haifa mana kyawawan baby's har guda huÉ—uda ta yi, juya ki ganta a jikin Tv". Ya kai karshen maganar yana shafa kanta.

A dubu É—ari ta zaro idanuwanta tana kallon Tv, su gwaggo kawai ta gani suna aikin gyara kasan wajen, Jehan É—in tana saman bed suka mayar da ita, saboda har lokacin tana sume ne, hakan yasa suka mayar da ita saman suna aikin gyara kasan kafin su koma ta kanta.

"Noorish ban ga Jehan É—in ba, in je bedroom É—in in dubata?". Ta yi maganar muryarta cike tab da zumuÉ—i.

Kai kawai ya gyaɗa mata tare da sakinta a kan ta je. Da gudu ta miƙe da nufin ta fita.

A hanzarce ya riƙota yana faɗin. "Saka kayanki tukun nan mana".

Nisawa ta yi tare da nufar dressing room nasa. A gaggauce ta zura abaya a jikinta tare da fitowa da sauri, har tana haÉ—awa da gudu.

Da kallo kawai ya bita da shi har ta fice abinta, sai zumuÉ—i take yi.

Bayan ta fita ne ya miƙe da nufin ya fita waje shi ma, zuciyarsa cike tab da tunanin baby's ɗin nan, da hannunsa yau ya karɓi haihuwa, Allah mai iko, idan ba dan Areef ba yaushe zai yarda ya kusanci mace mai ciki ma, amma sai ga shi ya kusanceta har ya karɓi haihuwa, Allah da ikonsa kuma har soyayyar yara ta dasu mashi a cikin zuciyarsa, dama ance wani sanadi shi yake kawo wani, to shi dai sanadin ya karɓi haihuwa Jehan, ta haihu a hannunsa, wannan sanadi tasa ya fara son yara, Allahu Akbar.

Parlourn kasa ya sauko, babu kowa a ciki, dan Æ´an gidan nan wasu suna kaiwa 12 na rana basu tashi barci ba wani lokaci, so babu kowa a parlourn.
Chapter 155 · 0% Book details