← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 168

Sashe 35

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Yadda suka yi tunanin Ummin zata ɗauki abin, sai ya zamana ba haka ta ɗauka ba, sai ma wani irin murmushi wadda da ka ganta, kasan dole aka ƙaƙalota, shi ta saki kafin ta ce "Dama ni bani na bawa kai Nawid ba, Allah ne ya bani shi, kuma duk yanda nake son shi, na san Allah ya fini son shi, ni ba zan taɓa butulcewa Ubangijina wajen yin kuka ko makamancin hakan dan ya karɓi rayuwar Nawid ba, na yi imani ya fi kowa sanin zuciyata, kuma a hakan ya ɗauki ran Nawid, ina farinciki da hakan, kuma ina kara godiya ga Allah, duk wanda bashi da yaro, ina rokan mashi Allah da ya bashi masu albarka, ni kuma ina rokan Allah daya kara mani hakuri, ina farinciki cewa ɗana ya rasu a ranar jumma'a, yanzu kawai ku kai ni naga gawarsa, zan yi mashi addu'a". Baiwar Allah, kowa yasan maganar nan ma da take yi, da kyar take fita, karfin imani ne kawai, da kuma yarda da ƙaddara, ta yarda da Allah shi ne mai yi, tana tawassuli da sunayensa tsarkaka, Allahu Akbar, a gaskiya samun uwa irinta a wannan zamani, zai yi matuƙar wahala, Imran da yake iya matsayin aboki a wajen Dr Nawid ma, sai da ya shiga tsakanin tashin hankali na wuce misali, bare kuma uwar da ta haifesa, kuma shi ne kawai ɗanta, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allah ya kara mata hakuri, a gaskiya ta nuna jarumta da karfin imani.

Sosai suka tausaya mata, kowa sai addu'a yake yi mata, ita kuma Aafia, sai da suka samu aka yi mata alluran barci, sannan ne suka sami zaman lafiya, in ba haka ba, sai buge buge take yi masu.

Brr Naurat É—in ce ta sake shigo da maganar case É—in daddyn Jelly bayan ta sanar da Ummi ai an rigada an kai Dr Nawid makwancinsa, sai dai su je makabartan Ummin ta ziyarce shi a can kawai.

Tambayar baban Muneer Brr Naurat ta yi, a kan shi ya ɗauki Ayla ko ba shi ba? Idan shi ne, ya dubi girman Allah ya dawo da ita, dan tana da karamin ciki wlh. Girgiza masu kai ya rinƙa yi a kan shi wlh ba shi bane, amma bakinsa bata iya yin magana, dan ya kumbura sosai.

Rimsha ce ta katse su da cewa "Nashiga uku, Ayla ta sake ɓata?! Allah dai yasa ba Daular Mutuwa suka mayar da ita ba, shikenan wlh kasheta za su yi, dama Duna ya gaya mana in dai muka kuskura muka bari muka dawo wannan gida, to wlh babu mai iya fitar da mu, wayyo mummyna!!". Ta kai karshen maganar tare da mikewa da sauri ta faɗa jikin daddynta tana sakin wani irin kuka mai tsuna zuciyar mai sauraro.

Tabbas an shafewa Rimsha tunanin Daular Mutuwa a cikin ƙwaƙwalwarta, yanzu ba ita ce ta yi maganar ba, Malika ce ta yi maganar, dan ita ta san Ayla tana can, bata da wata hanya da zata bi ta gaya masu Ayla tana can, dole sai ta hanyar shiga jikin Rimshar, saboda ita ce kaɗai ta taɓa zuwa Daular Mutuwar bayan Aylar, kuma tana son su san cewa head of the familynsu gabaɗaya wato Dr Salman yana can, shi ne yasa ta bi masu ta wannan hanyar ta shiga jikin Rimshar kawai.

Kowa na cikin palon mamakin jin sunan Daular Mutuwa yake yi, nan take Imran da Areef suka tuna da labarin da ta taɓa basu a baya, tabbas sun tuna da zancen, dan haka sai suka fara bawa jama'ar palon labarin irin ukubar da su Rimshar suka sha a wajen, shi ma daddyn Jellyn, sai a lokacin ya tuna da cewa tabbas Ayla ta taɓa gaya mashi zancen Daular Mutuwar nan, sosai abin ya dawo masu cikin kwakwalensu. Ganin hakan yasa Malikar ta fita daga jikin Rimshar, tun da sun tuna komai, sai ta kyalesu ta koma gefe kawai tana kallonsu.

Jin sunan Daular Mutuwa yasa Hjy Umaiya ta yi wani irin firgita sosai, a tsananin razane ta fara tambayar ina Akila, Akil, da kuma Imran?.

Da mamaki suke tambayarta lafiya, bata iya bawa kowa amsa ba, ita dai kawai tambaya take yi ina yaranta. Imran É—in ne ya ce "Ammie gamu nan ai, lafiya meyake faruwa?".

Banda girgiza kai babu wani abin da take yi.

"Kai ina Akila? Ya ban ganta a nan ba?". Cewar Akil.
Nan fa suka fara waige waige. Shi dai Lion binsu da idanu kawai yake yi, ya rasa meyasa gwaggo ta ce sai dai yazo anyi magana da shi, suna ta surutu suna kara mashi ciwon kai a banza.

Wasa wasa suka fara neman Akila, shiru babu ita babu labarinta, nan fa Hjy Umaiya ta birkice masu, ta yi masu karamar hauka, faÉ—i take yi wlh Queen ta dawo mata da Æ´arta, idan ba haka ba, to a wannan karon za su yi kare jini biri jini!!.

Zuba mata idanu kawai suka yi suna kallon ikon Allah. Brr Naurat ce ta tambayi Abban Imran wai matar nan tasa lafiyarta kuwa?.

Shiru shi ma ya yi ya kasa yin magana, dan kuwa bai san me zai ce ba.

Gwaggo ce ta miƙe ta riko Ammien tana tambayarta lafiya? Wacece kuma Queen?.

Cikin kuka ta basu amsa da mahaifiyarta ce, kuma ita ce shugabar wannan Daular Mutuwar da Rimsha ta ambata a yanzu.

Daga Imran har Areef sai da suka zaro idanu tamkar idanun nasu zai faÉ—i kasa, irin wannan bala'i na cikin Daular Mutuwar dukka Ammie ta ce uwarta ce shugabansu? Lallai kuwa, akwai cakwakiya.

Ita kuwa Rimsha miƙewa zaune ta yi tana karewa Ammien kallo, sai a yanzu komai yake dawo mata sabo, sai a yanzu take kallon tsananin kama na Ammien da kuma Duna, hakan na nufi duna ɗa ne ga Queen? Ko kuma ɗan uwanta ne? Dan sun yi kama sosai......WATA SABUWAR CAKWAKIYA KENAN, ME KUMA YA HAƊA AMMIEN DA DAULAR MUTUWA?.

"Abba menene ya haÉ—a Ammienmu da Daular Mutuwa?". Cewar Imran, da yake shi yasan labarin Daular a wajen Rimsha.

Zubawa Abban idanu kowa ya yi yana jiran amsa daga gare shi.

"Imran nima ban san me zan ce maku ba, amma ita Ammien taku ce kawai zata iya yi maku bayani".

Juyo da kallonsu a kanta suka yi, yau suna ganin tashin hankali, labarin yau kuma ya juya ta kansu Imran.......... TRIPLETS GIDAN SURPRISE, YAU KUMA LABARIN MU YA JUYA TA KAN SU IMRAN, SHIN AKWAI WANDA YA TAƁA TUNANIN QUEEN MAHAIFIYAR AMMIENSU IMRAN CE? TO YAU MA DAI SABUWAR BABIN CAZA KWAKWALWA MUKA BUƊE😂 KU DAI KU KASANCE DA PRINCESS TEEMA KAWAI, NI CE KAƊAI ZAN WARWARE MAKU WANNAN CAKWAKIYA!.
Chapter 35 · 0% Book details