← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 168

Sashe 113

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga Dr William har Dr Cherish ɗin sun kasa iya nufar in da sir Arvin yake a kwance a sume, saboda tsoron Lion suke ji sosai, suna son duba lafiyar ɗan nasu su ga menene yasa ya suma? Amma sun kasa iya koda ƙwaƙƙwarar motsi, haka zalika shi ma Handsome, yana son tambayar menene ya sami yayan nasa? Amma kuma ruɗani da tsoro sun hana shi, yana cikin ruɗanin ganin mai kama da yayan nasa da kuma daddynsu over, ga Pinky a gefe, sannan yana tsoron tambayar me ya sami sir Arvin ɗin, dan bai ga fuskar da za'a kawowa wargi ba a tattare da Lion!!.

A takaice dai a haka jirginsu ya ɗaga, tafiyar dole, tafiyar da bada son ransu ba, tafiyar da basu shirya mata ba, dan ma dai Lion ɗin ya shirya masu tafiyar ce tun kafin ya zo, dama ya shirya a kan idan ya zo dole ya koma da Cherish U.s, sai dai shi kansa bai san da su Pinky ba sai da ya zo, dole ya sake shirya tafiyar har da su, dan ba barinsu zai yi ba, dole ya ɗaukesu ko dan su karɓi kalmar shahada, ba yadda suka iya tun da ubansu ɗaya, dole kawai su rikesu hannu biyu.

To tun da jirginsu ya É—aga bari mu koma Nigeria muga me ake ciki, wata kila kafin mu dawo sun sauka a U.s lafiya.

NIGERIA❤️

Areef dai bai kyale Jehan ba sai da ya sami nutsuwa, ta yi kukanta har ta gaji, ya yi ta juyata son ransa, bayan ya sami nutsuwa kuma sai ya hau rarrashinta a kan ta yi hakuri ba zai sake ba, ƙin kula shi ta yi, ta ki yi mashi magana, sai da ta ga ya miƙe zai kunna wutar ɗakin ne ta yi maza ta rike hannunsa, a kule ta ce "Ni ka mayar mani da kayana jikina kafin ka kunna wutar".

Kamar zai yi dariya, sai kuma ya fasa, saboda yanzu ma ya yi laifi sosai, idan ya yi dariya kara yin wani laifin zai yi, dan haka sai ya rufawa kansa asiri kada ya kara takalo faÉ—a, yasan halin kayarsa sarai.

Ita kuma Jehan abin da baku sani ba shi ne, ba dan Allah ta kawo kanta gare shi ba, ba dan Allah ta biye mashi ba, abu take nema a wajensa, kuma kunsan Jehan haka kawai wlh ba zata durkusar da kanta kasa ba, taurin kanta ya wuce tunaninku, duk da yes tana son shi, amma ba zata zo ta bashi hakuri cikin sauki haka ba, kawai tana so ne ta yi amfani da shi ta fito da su Adiva daga gidan Hjyr daɗi, tasan dai shi kaɗai ne zai iya taimaka mata da gaskiya, tana ganin hukuma ba zasu yi gaskiya a kan al'amarin ba, ta yarda da shi sama da kowa, ko daddynta bata yardanwa da zuciyarta ta gaya mashi ba, saboda idan ta gayawa daddyn nata ma bai wuce ya ce su shigar da kara ga hukuma ba, kunga ta gudu ne bata tsira ba, ita kuma tasan da cewa Hjyr daɗi tana da manya manyan mutanen da hukuma ba zasu iya yi mata komai ba, maganinta kawai sai dai a sami tantiri irinta, wannan shi ne dalilin dayasa Jehan ta bada kai lokaci guda, saboda kullum da tunanin su Adiva take kwana take kuma tashi, abin yana ranta sosai, shiyasa ta yi wa Areef kwanciyar ɗaukar rai. Sai dai abin da bata sani ba, shi ne sarai Areef yasan dole da akwai abin da take so yasa ta yarda ta bashi hakuri, ya san halinta sarai fiye da kowa, saboda yasanta a ɓaɗini, idan kasan mutun a baɗini to shi ne kasan shi ba'a zahiri ba, yadda aka yi ya santa a baɗininta kuma shi ne, yana ganin duk abin da take yi a lokacin da take ita kaɗai, a lokacin da kake kai kaɗai shi ne ainahin halayyarka take bayyana, ainahin wanenen kai yake bayyana, so yasan ta a wannan lokaci, yana ganinta ta Camera, ita ce dai bata sani ba, so a takaice ya yi mata sanin da su mummynta ma basu sani ba, dan su zahirinta suka sani ba baɗini ba, yasan abin da zai sanya Jehan ta karya maganarta ta duƙar da kai ba ƙaramin abu bane, dan ta faɗa wa kanta sai dai Yah Areef ya nemeta ba dai ta neme shi ba koda zata mutu, so abin da zai sa ta karya wannan magana ba ƙaramin abu bane, koda kuwa zata mutu, haka take tamkar kanwar Lion a shegen taurin kai.

Kayan nata ya É—auko ya mayar mata a jikinta, yana yi yana ce mata sorry, kin kula shi ta yi, ta ce dai fushi take yi da shi. "Zaki yi wanka a tare da ni?" Ya raÉ—a mata hakan ne a kunne.

Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a ba zata yi ba. Why ya tambaya, mikewa zaune ta yi tana faÉ—a mashi babu wani dalili, kawai ba zata yi bane. Kara jawota jikinsa ya yi yana faÉ—in "Please mana my Jehan".

Ɗan ture shi ta yi. "Ni karabu da ni mun ɓata".

ÆŠan bakinsa ya sake mayarwa saitin kunnenta ya fara yi mata raÉ—a "Haba nana my baby, na ce fa na tuba ba zan sake ba, please mana, mu yi wanka a tare, zan kashe wutar toilet É—in sai na kunna blue light, kinga shi babu haske sosai".

"Kana son mu yi wanka a tare? Kuma kana son na dai'na fushi?". Ta tambaya tana ɗaura hannunta a saman ɓul ɓul ɗin breast nasa, dan ma kada ya yi mata musu a maganar da zata gaya mashi.

(Ba shakka Jehan ta cika ƴar duniya 😂 bafa abin da bata sani ba yarinyar nan😂 harda fara matsa mashi ɓul ɓul nasa dan kada ya yi mata musu idan ta faɗi bukatarta 😂 Maman Yasmin come forward, irin tarbiyar da kika bata kenan ba?🤔😂 Yaudara kiri kiri😂 zata cuci bawan Allah bai ji bai gani ba🧐😂)

"Yeah my baby, ina son muyi wanka a tare".

"Okey promise me that duk abin da nace kayi mani zaka yi?". Shiru ya ɗan yi, dan yasan halinta sarai, yanzu sai ta jefa shi cikin wata cakwakiyar, amma tun da yana sonta, sai ya ce "I promised you in dai abin bai kaucewa Shari'a ba, bai kuma saɓawa Allah ba, to tabbas zan yi maki my baby".

Kara matsa mashi ɓul ɓul ɗin breast ɗin nasa da ɗan ƙarfi ta yi har sai da ya ce "Wash my baby, so kike na koma ruwa ko?".

Hannu ta kai ta É—aura a saman kyakkyawar lips nasa tana faÉ—in "To ai ko ka koma ruwan ma kayan ka ne, ni taka ce, yanzu dai muje mu yi wankar, sai kazo na baka abinci a baki kafin na gaya maka abin da nake son ka yi mani, nasan kana jin yunwa sosai, ka bari can cikin dare sai ka koma ruwan".

Haƙiƙa ya yi mamaki sosai da jin maganar nan tata, saboda bai taɓa tunanin ta iya magana har haka ba, wai zata bashi abinci a baki dan tasan yana jin yunwa, kuma da tsakar dare ya koma ruwa, wato cikin dare zasu yi wasa, bai taɓa tunanin ta iya waɗan nan abubuwa dukka ba, yarinyar nan ba shakka idan aka barta da namiji sai ta kwance mashi notikan kwakwalwa, dama an ce ka guji mutun mai shiru shiru, dan ya wuce tunaninka, wannan shiru shirun da yake ɗin ka barshi a haka, idan ka sake ka bari ya buɗe baki, to sai ka zama wawa a gabansa, kuma ba shakka hakance, idan namiji ya kuskura ya shiga hannun Jehan, wlh sai Allah ne kawai zai kwacesa, dan ta iya duk wani duniyanci, barema idan tana da bukatar ayi mata abu, tamkar mage mai kwanciyar ɗaukar rai take zama, sa'ar Areef ɗin dai ɗaya da Allah yasa da iya gaskiyarta take son shi, tsakani da Allah take son shi, banda haka da zata wahalar da zuciyar bawan Allah'n nan ba kaɗan ba, sai dai Allah ba azzalumin bawansa bane, sai dai bawa ya zalinci kansa, da Allah ya tashi kamata sai ya cusa mata son mijin nata kamar hauka, ba zata iya rayuwa babu shi a gefenta ba.

Ganin ya yi shiru ya faɗa duniyar tunani ne yasa ta shige cikin Lion chest nasa tana saka mashi kukan shagwaɓa tare da fara shafa ɓul ɓul nasa. Rungumeta sosai ya yi yana faɗin "Menene kuma?". "Katashi muje mu yi wanka mana, amma ka zauna kana wani tunani, yanzu tunanin me ma kake yi? Ba dai na wata macen ba ne?".

Nisawa ya yi kafin ya miƙe tare da ɗaukarta cak, duk kaifin ƙwaƙwalwa irin nasa yau Jehan tana neman sanya shi ya ji duk tunaninsa ta tsaya cak, tana neman kwance mashi lissafin ƙwaƙwalwa, ya rasa a wani point zai ajiyeta, ga shi ma taki yarda ya kunna wutar ɗakin bare ya ganta ido da ido, bai san cewa gara mashi ma da bai kunna wutar ba, dan idan ya kunna waɗan nan shegun sexy eyes ɗin nata kara birkita shi zasu yi, dama can yana kaunar idanuwan nata, shiyasa yake ce mata da idanunta kamar ball, to idan ya kunna wuta suna ganin juna, idan ta juta mashi fararen idanun nan sama cikin kisisina ai sai ya kara ruɗewa ya birkice ya rasa ina zai sa kansa.

(Akwai ƴan duniya kala kala a TRIPLETS, amma bana jin akwai biyun Lion da Jehan 😂 kamar dukkansu nonon gwaggo suka sha😂)

Bai sauketa a ko'ina ba sai a cikin tsakiyar toilet, da yake da akwai haske wuta a toilet ɗin, sai ya zubawa face nata idanu yana kallonta cike da tsantsar so da kauna. Wani irin kallon soyayya ta wurga mashi tare da ɗan turo baki a shagwaɓe ta ce "To me kake wani kallona kuma? Kafa ce zaka kashe wutar toilet ɗin".

"Ina, ina my baby, ba zan iya kashe wannan wutar ba, barni na kalli matata". Ya kai karshen maganar tare da jawota jikinsa sosai, sai a lokacin ta lura da babu kaya a jikinsa, tamkar zata zunduma mashi ihu, sai kuma ta daure ta cije ta kwantar da kanta a saman Lion chest nasa tare da runtse idanuwanta gam.
Chapter 113 · 0% Book details