Sashe 54
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya kowa dake cikin wajen suka sauke, Brr Naurat ce ta ce "Sannu É—ana, kasha gwagwarmaya kai ma". Tana magana tana shafa kansa.
Abbi ne ya kai mashi duka yana faÉ—in "Kana ji muna nemanka a lokacin, amma sai ka sheremu ko?". Jinjina masu kai ya yi alamar e É—in ya share.
Nan fa kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa, shiru ya yi masu kamar baya wajen. Haka suka kasance cikin tsantsar farinciki da kuma yi wa Æ´aÆ´ansu dake Daular Mutuwa addu'a.
After some minutes gwaggo ce ta ce "Ni kam wai Aseef bai dawo daga shopping É—in da ya ce mani zai je bane?".
Daddyn jelly ne ya amsa mata da "Gaskiya fa kamar bai dawo ba, wata kila ya wuce wani wajen ne".
Da mamaki Abban Imran ya ce "Kai ba Saif ya ce kada kowa ya fita daga cikin gidan nan ba? Ya za'ayi A'isha ki barshi ya fita? Suma sojojin ya za'ayi su karya maganar Saif? Ko da yake sun fi kusa da shi, kila ya ce masu idan Aseef zai fita su bashi hanya ne"
"Hmmm yaya babba kenan, Aseef É—an rigimar ne za'a hana fita, ai idan suka hana shi fita,to wlh gidan nan babu zaman lafiya, ni kai'na idan na ce ba zai je ko'ina ba, to babu ni babu zaman lafiya, shi ne yasa kawai na ce mashi sai ya dawo". Cewar gwaggo.
"Gaskiya kam Aseef É—an rigima ne wlh". Cewar Abbi.
Abba ne ya tari nunfashinsu da cewa "Ni ne nan zan baku labarin rigimarsa, yaron da ya je ya tasani a gaba ya rinƙa kuka lokacin da na ce ba zan bashi auren AKILA ba, Irfan ya riga shi, hmmmm ni zan gaya maku rigimar Aseef wlh".
Murmushi gwaggon ta yi, ita kaÉ—ai tasan me take tunawa take sakin wannan murmushi. Haka dai suka cigaba da hirarsu na tsawon mintocin kafin nan a kira sallar azzahar kowa ya watse, dan suje su yi sallah.
After some days.
Abubuwa da yawa sun faru a cikin kwanakin nan da suka shuɗe, ciki harda neman Aseef da su gwaggo suka rinƙa yi, amma shiru babu shi babu labarinsa, hakan yasa hankulansu ya kara mummunar tashi, nan fa suka dukufa wajen addu'a babu kama hannun yaro, suma fa sauran sojojin da suke a bakin gate, hankulansu ya yi mummunar tashi ba kaɗan ba, dan idan har Aseef baya gidan, to ba shakka sun shiga uku da Lion idan ya dawo, dan sun karya mashi doka na barin wani daga cikin family ya fita, su kuma wlh sam basu ga fitar Aseef ɗin ba, ba su san time da ya fita ba, Allah ya gani, bayin Allan sun shiga tsananin damuwa na wuce misali.
Daular Mutuwa.
Sun shafe kwanaki a cikinta suna neman Æ´an uwansu, amma san basu gansu ba, duk wani part da zasu faÉ—a a cikin Daular, sai su ga kamar sun bar duniya, ga shi su da suke rayenma sun raba hanya, Aseef ya yi gabas, Areef ya yi yamma, sun sha matukar bakar wahala, har shi kansa Aseef É—in ya wahala, kuma bai gane ina Fadar Queen É—in take ba.
Areef ne ke a kan wata hanya yana tafiya, sai wuce ɗakuna da abubuwa na ban tsoro da tsafe tsafe yake yi, tunanin ina Lion yake kawai yake yi, wani irin azababben yunwa yake ji, akwai snacks and drinks a cikin jakar dake goye a bayansa, amma ya kasa saukewa ya samu waje ya nutsu ya ci ya ƙoshi, shi burinsa kawai yaga ƴan uwansa. Duk wannan wahala da yake sha, bai dai'na ambato sunan Allah ba, hakan yasa Queen ta kasa ganin wai shin a ina ma yake, ya ɓace daga idanun tsafinta, sai nemansu take yi shi da Aseef, amma ko alamar mai kama da su bata gani ba.
Ya zo dai'dai wata mararraba, hanyoyi ne suka rabu gida biyu, ɗaya ta yi gabas ɗaya ta yi yamma. A dai'dai wajen ya tsaya yana tunane tunane ya zai yi a yanzu? Shi dai ko mutuwa zai yi wlh sai dai ya mutu, amma ba zai taɓa yarda ya bar cikin Daular nan ba tare da ƴan uwansa ba. Idan ma ya ce zai bar cikin Daular ta ina ne hanyar fita?.
A hankali ya fara jin motsi ta hanyar dake kallon yamma, shiru ya surara yana son tantance motsin menene?. Jin kamar sautin numfashin mutane ne yasa ya nufi hanyar babu tsoro ko miskala zarratin a tattare da shi.
Ko da ya isa wajen sai ganin su Mark ya yi gabaÉ—ayansu da sauran sojojin a É—aure da sarkoki masu karfin gaske, sai dai babu Lion a cikinsu. Hamdala ya yi ga Allah, ko ba komai ya ga wasu daga cikin tawagarsu, saura su Ayla da kuma Lion, sai Heartbeat nasu, wato Aseef shalele É—an rigima.
Ba tare da ɓata lokaci ba, cikin kwarin gwiwa ya fara ƙoƙarin buɗe kofar karfen, a rufe kofar take ruf da matakan tsaron Queen. Sai kuma me? Yana ƙoƙarin sakawa kofar karfi ya buɗe ta, kamar daga sama ya ji wani uban jijjiga da ginin ya fara yi, kafin nan ya yi wata yunkuri ginin ta rufta, kofar ɗakin ya toshe.
Hakika a wannan karon ba ƙaramar tashin hankali ya shiga ba, ya shiga ruɗu ta yadda kwata kwata baya iya gane ina ya dosa. Da sauri ya bar wajen saboda wani irin turnukin kura da ya taso, dan ma Allah yasa kofofin ɗakunan irin na karafunan nan ne masu kama da prison, so kofar ta tare ginin bai ruguzo a kansa ba.
Da sauri ya fito daga hanyar idanuwansa sun yi jajir tamkar wuta, sai wani huci yake yi, Hakika ya ji takaicin mutuwarsu Mark, har wani pat, pat, pat zuciyarsa take harba mashi, wani irin tukukin bakin ciki ne ya tokare mashi maƙoshi, da kyar yake haɗiyar wahalallen yawu, kansa sara mashi take yi tamkar zata fashi, har wani irin jiri ya fara gani.
Yana fitowa daga wannan hanya ya faɗa cikin wata tapkekiyar waje, wannan waje kuma ba ko'ina bane face wajen da su Rimsha suka taɓa zama, already dama kunsan ya yanayin wajen yake, ga faɗi da girma, ga kuma ɗakuna da yawa a cikinsu.
Zubawa wajen idanu ya yi yana kallon yanda yake, kamar daga sama ya ga dirowan mutane a gabansa. Jiga jigan matsafane masu ji da karfi, dama Queen ta turosu ne su nemo shi, tasbihi da yake yi ne yasa basu iya ganinsa ba, to a yanzu kuma ya dai'na ambaton Allah, saboda bala'in da ya shiga na ganin abin da ya faru da su Mark, a lokacin ne ma ya kamata ya ambaci sunan Allah da kyau, sai kuma tashin hankali ta hana shi, ya shiga ruÉ—u na ganin yanda wannan gini ta ruguzo.
Ganin mutanen yasa ya kara shiga tashin hankali, dama already bai dawo dai'dai ba.
Kafin ya yi wani yunkuri waÉ—an nan jiga jigan matsafa, É—aya daga cikinsu ya sanya hannu ya sunkuce shi sama, wurgi ya yi da shi can gefe, ta fiya ya yi zai bugu da jikin wannan gunki na karfe mai kifiyoyin tsafi a jikinsa.
Tamkar wani walkiya haka Aseef ya bayyana a wajen ya tare shi, a tare suka faÉ—i kasa ba tare da sun isa ga wannan gunki ba. Ash suka furta a tare. Shi Aseef da Areef ya faÉ—o a kansa ma yana a cikin hayyacinsa sosai, shi kuma Areef É—in saboda already yana cikin ruÉ—ani, sai hakan ta kara gusar mashi da hankalinsa daga jikinsa, hakan yasa ya kasa koda motsawa.
Kwantar da shi a gefe Aseef ɗin ya yi tare da mikewa tsaye, a hankali ya ɗago da dara daran brown eyes nasa izuwa kan waɗan nan matsafa, sun kasance su biyarne cif, jibga jibga da su madaka karti. Kallon up and down ya yi masu kafin ya mai do da kallonsa a kan Areef dake motsi yana ƙoƙarin dawowa dai'dai.
Wani irin taunan hakwara waÉ—an nan matsafan suka fara yi, tare kuma da wani lankwashe kasusuwan jikkunansu, tamkar wasu macizai. Shiru Aseef É—in ya zuba masu idanu yana kallonsu, har suka gama duk abin da za su yi, sannan suka tunkare shi da nufin su yi kutsi kutsi da su, su cinyesu É—anye. Dai'dai lokacin shi ma Areef ya mike tsaye, ya dawo cikin hayyacinsa bawan Allah, ga uban yunwa da yake ji.
Wucewa gaba Aseef É—in ya yi, ya tari waÉ—an nan matsafa gadan gadan suka fara faÉ—a babu kama hannun yaro. Areef ya so ya taimaka mashi, sai dai kuma faÉ—ar tafi karfinsa, ta wuce tunaninsa, daga karshe sai ya rabu da su suna faÉ—ar, shi kuma ya fara duba É—akunan da suke wajen, a cikin zuciyarsa yana ta mamaki tare da tunanin a ina Aseef ya samu wannan karfi har haka, sai dai kuma a baki ya kasa furta hakan, ya kasa iya tambayar Aseef É—in komai, sai dai kawai ya bishi da idanu, komai zai yi ba zai iya tambayarsa menene yasa ya yi ba....... E lallai da akwai cakwakiyar gaske kenan.
Binciken É—aku nan da ya fara yi ne, a nan ne ya cikaro da Dr Salman da kuma Ayla a É—aki É—aya suna zauna, sun buga uban tagumi, dama idan baku manta ba, Ayla mutuniyar Dr Salman ce sosai, sun saba tun zamanta a Daular a shekarun baya, dan haka ko da ta sake dawowa a yanzu, sai kawai ta koma É—akinsa ma da zama tun da bata da abokan hira. Bayin Allan, da kallo É—aya zaka yi masu kasan suna cikin tsananin firgici da tashin hankali, sun wahala over, duk sun yi wani tsuru tsuru da su.
Da kallo É—aya ya yi wa Dr Salman duk da tsufan da ya yi, ya gane cewa shi ne kakansu, dan babu in da Abbi ya baro shi a kamanni, akwai kaman Æ´aÆ´ansa a tattare da fuskarsa.
Bai ɓata lokacin ba ya faɗa cikin ɗakin tare da yi masu bayani a tsaitsaye na cewa sun zo fitar da su ne, sannan ya ce su je ba ɓata lokaci, suma basu ɓata lokaci ba wajen mikewa su bi bayansa, saboda Allah ya gani sun gaji da wannan bakar gida ta bakaken azzaluman.