← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 168

Sashe 118

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sam bai bi ta kansu Cherish ba, cikin nutsuwa ya ce da Dr William da yake a tsaye yana bin parlourn da kallo. "Dad have a seat". Ya yi maganar kuma idanuwansa na'a kan screen ɗin wayar tasa, ya kunnata yana ƙoƙarin kiran number Areef, dan ya sanar da shi sun isa lafiya, saboda yasan halin ƴan uwan nasa, idan ɗaya daga cikinsu baya nan, to basu samun nutsuwa, bare kuma ace basu yi waya ba, duk suna shiga damuwa sosai, shiyasa duk in da zasu je a duniya, in dai sun sami dama to dole sai sun kira juna, hakance kawai yake samar masu da kwanciyar hankali.

Sam Dr William bai yi wa Lion musu ba, saboda duk da baya a cikin hayyacinsa, bai san ma wanenen shi ba, amma yana jin cewa Lion ɗansa ne, saboda kamanceceniya da suke yi da shi kansa, ga kuma kamanceceniya da sir Arvin da suke yi, hakan tasa ya ji cewa lallai Lion ɗansa ne, har cikin ransa yake jin kaunar Lion ɗin sosai, ji yake yi ma kamar yaje ya rungumesa, amma haka ya daure dai, ya sami waje a saman sofa set dake set ɗin kusa da su ya zauna, ya kasa kawar da blue eyes nasa daga kallon Lion ɗin, ya kalli Lion ya kalli Aseef, duk sai ya ji kamar ya je ya rungumi Aseef, yana jin kamar Aseef wani ɓangarene na zuciyar tasa, dama shi Aseef kun san shi da shiga rai kamar Rimshar Lion ɗin, so tun daddynsu bai dawo cikin hayyacinsa bama yake jin wani irin zazzafar kaunar Aseef ɗin.

Shi ma Aseef É—in sai kallon daddyn nasu yake yi, yana son ya yi magana, amma ya yi shiru, saboda yasan ko ya yi magana ma Lion ba kula shi zai yi ba, sai time da yaga damar amsawa zai amsa masu, dan haka sai ya ja bakinsa ya yi shiru tare da zama kusa da Lion É—in.

Sau biyu Lion ɗin yana gwada kiran number Areef, amma bata shiga, hakura ya yi sannan ya kira number gwaggo, a lokacin Rimsha ta tada kanta da cinyar gwaggon tana zuba shagwaɓarta son ranta, ita kuma gwaggon tana biye mata.

Sabuwar waya Areef yasa Tga ya sayawa gwaggon tun kafin yazo Nigeriar, tun time da Rimsha ta yi fushi ta fasa mata wayar tata.

Bugu É—aya gwaggon ta É—auka, dan dama sai neman numbersa take yi a kashe.

"Good afternoon momma". Ya faÉ—a a sanyaye

"Afternoon my son, how was your journey?".

"Alhamdulillah how are you and my wife?". Bawan Allah komai yake yi yana tunanin Rimsha sosai, tana ransa, bai san cewa ma fushi take yi da shi ba.

"Alhamdulillah, your wife gata nan tana zuba mani rigima".
Jin abin da gwaggon ta faɗa ne yasa Rimshar ta miƙe tare da saukowa kasa daga saman bed ɗin, tana ɗingisa kafa ta fice daga ɗakin, dan kada gwaggon ta ce zata haɗata da Lion ɗin, a cewarta fushi take yi da shi, baiwar Allah har yanzu bata iya tafiya da kyau, sai dai ta yi ta ɗingisa kafafu, kuma har yanzu tana ɗan jin zafi, barema idan tana tafiya wajen yana ɗan yi mata zafi, dan ma kullum gwaggo bata barinta sai ta shiga ruwan zafi ta gasu, hakan ce ma tasa abin ya yi mata sauki.

Da kallon mamaki gwaggon ta bita har ta fice daga ɗakin, dai'dai lokacin kuma Lion ɗin ya ce "Momma please give her the phone, i really missed her, i want to hear her voice". Ya yi maganar kasa kasa sosai, dan ko Aseef da yake a zaune kusa da shi saman sofa ɗaya ma bai ji me ya faɗa ba, dama can kullum maganarsa a kasa kasa take, amma fa idan zai yi magana da Rimsha ko zai yi magana a kanta, yana kara yin kasa sosai da muryarsa, ko kai da kake waya da shi idan ba kana da lafiyayyen kunne ba, bazaka taɓa jin abin da ya faɗa ba.

Thank God gwaggon dai ta ji abin da ya ce, sai dai ta rasa amsar da zata bashi, tun farko tarigada ta ce mashi ga Rimshar a kwance a kusa da ita, yanzu kuma ta ce mashi bata nan? Anya kuwa hakan zai yi wu? Ga shi yadda ta ji voice nasa duk a gajiye yake, uwa da É—a, har tana iya fahimtar halin da yake a ciki ko da waya suke yi, Allahu Akbar, wani abin sai uwa! Allah dai ka kara masu lafiya da nisan kwana, waÉ—an da suka rigamu gidan gaskiya kuma Allah ya jikansu ya rahamcesu, ya kai haske cikin kabarinsu, daga karshe ya saka masu da gidan Aljannartul firdaus.

"Yanzu ta shiga toilet, sai ta fito". Ta bashi amsa da haka ba dan ta so ba!.

Shiru ya ɗan yi, duk da mommarsa ce, a wannan magana tata ya fahimci ba dai'dai ta gaya mashi ba, dan shi akwai shi da fahimta over, kuma gwaggon bata saba yin karya ba, dama haka ne, idan baka saba yin karya ba, in kayi sai an gane, duk sai ya ji jikinsa ya yi sanyi, zuciyarsa tana gaya mashi cewa akwai wani abin a kasa, ko Rimsha bata da lafiya, ko kuma dai fushin da ta yi da shi ne har yau bata sauko ba, tabbas akwai wani abin da aka ɓoye mashi, duk sai ya ji ya damu, sai ya ji zuciyarsa babu daɗi, haka dai ya daure ya ce mata "Okey momma let me go and take a bath, daga nan zan yi barci kaɗan, sai dare zamu yi waya, and kada ki manta gobe zaku taso fa kuma, because i really missed you over, and then there's important thing that's waiting for you here".

"Okey my son, take good care of yourself, and ka kula mani da my autana sosai, komai yake so ku tabbatar kun bashi".

(Bala'i lallai gwaggo, wai komai Aseef yake so a bashi? Dama yaya lafiyar kura bare kuma ta yi zawo?😂)

Nisawa ya yi a cikin zuciyarsa yana godiya ga Allah dayasa ba'a gaban gwaggo Aseef ya taso ba, da iskancin nasa sai ta wuce haka, yanzu ma ya suka kare da shi? Amma a haka Gwaggon take cewa ayi mashi komai da yake so? Lallai kuwa da ita ta rene shi lalacewarsa sai tafi haka.

Jin ya yi shiru ne yasa ta ce "Son are you okey? What are you thinking?". "Nothing momma, see you later". Ya kai karshen maganar cikin kasalalliyar murya tare da katse kiran. Sai bayan ya katse kiran ne ya É—ago da kallonsa izuwa kan su Handsome dake tsai tsaye cirko cirko, sun kasa zama, ganin parlourn suke yi tamkar ba'a duniya suke ba.

Miƙewa tsaye ya yi tare da nufar saman bene yana sanar da Aseef a kan ya kula dasu Handsome ɗin, ya basu wajen zama da ruwan sha tare da abinci, shi bari ya yi wanka ya kwanta ya yi barci.

Okey kawai Aseef ɗin ya bishi da shi, sannan ya ce su samu waje su zauna mana, sai a lokacin kuma ya sauke idanuwansa a kan Cherish, ɗan zuba mata idanu ya yi, yanzu kam ko ba'a gaya mashi meyake faruwa ba ya gane, dan gabaɗaya ƴaƴan Dr William shegen kaifin kwakwalwar bala'i ke garesu, yanzu ya fahimci in da komai ya dosa, saboda yasan Cherish a hoto, kuma yaji labarinta, ya san alaƙar dake a tsakaninta da gwaggon, kallon ɗai ɗai ya fara yi wa su Handsome ɗin, dan ya kara tabbatarwa da kansa abin da yake zargi. Alama ya yi wa Pinky da hannu a kan tazo.

Da farko kamar zataki zuwa, sai kuma ta tuna cewa ai gidansu suka zo, dan haka bata isa ta yi mashi musu ba, kuma taga su ba masu mugunta bane, tun da sun zubawa sir Arvin ruwa ya farfaÉ—o daga suma ya faÉ—a barci bawan Allah.

A hankali ta nufesa tana É—an É—ari É—ari. Kusa da shi ya zaunar da ita yana mai cigaba da kallon face nata. Suma su Cherish zama a saman sofa guda É—aya mai zaman mutun uku suka yi ita da Handsome É—in.

Welcome Aseef É—in ya yi masu kafin nan yasa bodyguards su kawo masu ruwa da kayan cima.
Bayan ya tabbatar ankawo masu, sannan ya miƙe tare da haurawa sama yana faɗa masu yana zuwa.

Okey handsome ha amsa mashi da shi, sannan suka fara cin abubuwan da aka zube masu a gabansu a saman carpet, yunwa suke ji yasa dole suka ci.

Sun ɗan yi nisa a ci abinci, miƙewa Cherish ta yi tare da nufar in da take zaton shi ne kitchen, tambayarta lafiya ina zata je? Handsome ya yi, "Am coming i want to check some type of their food". Ta bashi amsa.

Shiru ya yi bai sake yin magana ba.

Cikin kitchen ɗin ta shiga. Babu kowa a cikin kitchen ɗin, duk sun kammala aikinsu sun fita waje. Su kuwa su Pinky sai cin abinsu suke yi, dole tasa suke cin abincin ma ba dan yayi masu ba, sai dan yunwa da kuma basu da zaɓi, basu isa su ce bai yi masu ɗin ba.

After some minutes, bayan sun kammala cin abincin nasu, shiru shiru Dr Cherish bata dawo cikin parlourn ba, miƙewa Handsome ya yi domin ya je ya dubata lafiya bata dawo ba tun ɗazun, da kallo suka bishi har ya shige cikin kitchen ɗin.

Wani iri razababben ihu ya kurma tare da fitowa daga kitchen ɗin da gudu, a tare Dr William da Pinky suka miƙe tsaye suna tambayarsa lafiya?. Da gudu Aseef ya sauko kasa daga sama shi ma yana tambayar lafiya kuwa suke yin ihu?.

A tsananin ruɗe Handsome ɗin ya gaya masu abin da ya gani a cikin kitchen ɗin. A dubu ɗari kusan a tare Aseef da Dr William suka nufi cikin kitchen ɗin. Cherish ce kwance cikin jini malala a kasa, ta daɓawa kanta wuƙa a ciki, da alama ma ta ɗan ɗauki ƴan mintoci da mutuwa.

Zaro idanuwa waje sosai Aseef ya yi, cikin tashin hankali yake tambayar waye ya yi mata hakan? Waye ya kasheta?.
Chapter 118 · 0% Book details