Sashe 61
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jingina kansa da jikin itacen Lion É—in ya yi, a hankali ya lumshe idanuwansa, wani barcin wahala ce ta É—an É—aukesa a wajen, ita ma Akila kwanciya ta yi a kasar, tare da tada kai da laps na Heartbeat nata, tana kwanciya sai barci, shi ma Dr Salman kwanciya ya yi, ya yi barci bawan Allah, ita Ayla, dama already a sume take.
Kafin Areef ya dawo, duk sun yi barci, ya É—ebo ruwa a cikin wata gora da ya gani a wajen, sai a lokacin ya tuna da jakarsa da ya barota a fadar Queen, har ruwa da akwai a cikin jakar. Ajiye ruwan ya yi, sannan ya zauna dan ya mike kafafunsa ya É—an huta, shi ma ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi.
After some hours.
Can cikin barci Lion ya ji motsi a kusa da su, duk da ya san suna da yawa a wajen, amma wannan ba motsin mutun bane, mutsin wata dabba ce, kunsan shi dama already bashi da nauyin barci, dan haka sai ya farka. A hankali ya buÉ—e idanuwansa. Wata zabgegiyar kunama ce a kusa da Aseef dake jingine da jikin itacen yana barci shi ma, ga Heartbeat ta yi barci a saman cinyarsa, shi Lion already dama ya saba da irin wajen nan, wanda ya fi haka haÉ—ari ma sun zauna a ciki kafin ya taka matsayin da yake a kai yanzu, ai dama soja bai kamata ya ji tsoro ko kuma ace waje irin wannan ta zamar mashi bakuwar waje ba, musamman ma sojoji irinsu na Usa.
Dan haka sai ya kai hannunsa ya kama kunamar, tana ƙoƙarin kai mashi harbi, ya yi maza ya damki karin nata, da karfi ya tsige daga jikinta ya gefar gefe guda. Yana gefarwa sai ya ji wani motsi daga ɗan nesa da su, alamar tafiyar mutane ne. Lumshe idanuwansa ya yi yana mamaki mutane kuma a wannan dajin?.
Bai buÉ—e idanu ba har sai da ya ji isowar mutanen kansu. A hankali ya waro idanuwansa a kansu. Mutanene sun kai su 10, kaÉ—an ne daga cikin mutanen da su Areef suka taimaka a cikin Daular Mutuwar, su ne waÉ—an da Aseef ya buÉ—ewa kofa suka fita.
Sannu suka yi wa Lion ɗin cikin harshen yarabanci. Mayar da idanuwansa ya yi ya lumshe, a cewarsa basu ishe shi kallo ba, ba zai ɓata idanuwansa wajen ganinsu ba.
Wata daga cikinsu ne ta yi magana cikin harshen turanci, a in da ta ce "Laaa kuga abin mamaki, ga shi yana zaune a wajen, ga kuma zanen face nasa a jikin itacen da yake zaune É—in! Ko dai shi ne ya zana? Amma kuma kamar zanen ya jima!".
Jin sun ambaci sunan zane ne yasa ya waro idanuwansa, dan shi dai yasan Meeshansa ce kawai ta iya zana shi, kuma ba shakka ya ga tulin zanensa da ta yi a cikin Daular Mutuwar, a hanyarsa ta zuwa neman Queen, a lokacin ya ci karo da wani É—aki, yana shiga ya tatda zanen face nasa da yawa a ciki, duk tabi jikin bango ta zana, wannan É—akin kuma ba ko'ina bane face É—akin da Rimshar ta zauna, idan baku manta ba dama ta yi zanensa sosai a wajen.
A hankali ya juyar da kallonsa izuwa kan in da matar take nunawa, dan ya kalli zanen da idanunsa. Bai yi mamaki ba, kuma da kallo ɗaya ya yi wa zanen ya gane tabbas zanen Rimsha ce, saboda zanenta baya ɓuya mashi, tana barin alama guda ɗaya a jikin zanenta idan ta yi, wannan alama kuma ba komai bane face a duk in da ta zana face nasa, to sai ta zana mashi lips nata a saman kumatunsa, alamar ta yi kissing na zanen, so a dukka zanensa da ta yi a rayuwarta, da akwai wannan alamar ta kiss ɗin.
Mai da idanuwansa ya yi ya lumshe yana tunani yanzu duk irin wannan wahala ta wannan hanya haka Meeshansa ta biyo? Yanzu haka ta keta wannan kungurmin daji haka? A gaskiya Queen ta cuce shi dayawa, ta wahalar mashi da pleasurensa, dole Rimsha ta ce ba zata dawo Daular Mutuwa ba, ashe azaba ta sha na kin karawa baiwar Allah, ya zama dole idan ya koma gida ya kula da ita sosai.......
Yana tsaka da tunanin ne mutanen suka katse mashi tunanin da cewa sun zo su taimaka masu ne, da akwai abinci da ruwan sha a masaukinsu, su zo suje sai su ci.................Lallai rashin sani yafi dare duhu, basu san wanenen Lion ba, da sam bama za su zo in da yake ba bare suce ya zo ya ci abincinsu da suka girka da ita ce duk hayaki, abincin ma a dajin suka samo shi, sai Allah ne yasan menene ma, sai kuma su da suka girka, to shi Lion da ma bai iya cin abincin Nigeria ba! Ai ko sau ɗaya bai taɓa gwada cin abincin Naija ba, bai iya ba, baya ma son kamshinta, ina da tabbacin ko yunwa zata kashe shi ba ci zai yi ba, komai haɗin da za'ayi wa abincin Naija da wuya ya iya ɗanɗanawa, abinci mai rai da lafiya wadda ta amsa sunanta abinci ma kenan, ina ga kuma wannan abincin nasu na ƴan gudun hijira? Ai ko kallo ma ba zai yi ba bare ci, zai ce datti ce, kuma kun san shi da bala'in kyankyani, ai idan ya gani da ido ma, ya rinƙa sheka masu amai kenan har sai abin da hali ya yi kuma.
Ko kallon in da suke bai sake yi ba, tamkar ma babu shi a wajen, da suka ga bai amsa ba, sai suka yi tunanin bai ji su bane, sai suka sake yi mashi magana. Wani irin tsawa ya daka masu na su tashi su bashi waje, dan sun ishe shi. Bayin Allah har wani firgita suka yi, su da suka zo taimako, dama sun ga cewa Areef da Aseef sun taimaka masu ne, shi ne suma suna ganin a yanzu sun sami dama, bari suma su taimaka masu, basu san waÉ—an nan ba'ayi masu goninta ba, ai TRIPLETS barsu kawai a yanda ka gansu, dan sun wuce tunaninka, sai kana tunanin yau zaka gansu a fari, sai ka gansu a ja, haka suke, baka gane ina suka dosa, sam su ba'a yi masu goninta, kuma ba'a burgesu, idan ba yanzu ma da suka sami mata bane abin ya ragu, da a baya ne ai ba'a ma magana.
Tsawar nan da ya daka masu ne yasa su Areef suka farka daga barcin da suke yi. Kallon sama da kasa Areef ya watsawa mutanen, a lokacin kuma already sun juya zasu koma wajensu.
Miƙewa ya yi ya ɗauko robar ruwan da ya ajiye, a gaban sojojin ya dawo ya tsugunna, a hannunsa ya tarbo ruwan tare da fara yayyafa masu a face nasu.
Kusan a tare bayin Allah suka farka, ganin sun farka ne yasa ya ajiye ragowar ruwan, ya koma kusa da Ayla dake kwance bata ko motsi.
Shiru ya É—an yi yana tunanin, shin ya dubata ne? Ko dai ya barta kawai sai sun isa gida? Dan ko ya ce zai dubata ma, sam babu kayan aiki, babu komai a tattare da su, ga shi kuma cikin jikinta ne ya fita, aiki take bukata na musamman. Daurewa dai ya yi ya kyaleta ba dan ya so ba, bawan Allah yana da tausayi sosai.
Mikewa Lion ya yi ya nufi cikin dajin, dan ya duba ya wajen yake, bayan ya karɓi Jacket ɗin dake jikin Aseef. Shi kuma Areef ya fara ƙoƙarin tattare kansu, dan su tafi, ya yayyafawa Mark ma ruwa, bayan ya farfaɗo, sai ya saɓesa a saman kafaɗarsa, kasancewar ya sami karaya a kafar tasa, da haka suka mike suka fara tafiya, Lion kuma ya shige cikin daji, Areef ya ce su je Lion ɗin zai samesu a gaba ai, ya san halinsa sarai, ga sauri a wajen tafiya, zai yi saurin cin masu.
Haka suka cigaba da tafiya, Lion bai sake haÉ—uwa da su ba har sai da rana ta kusa faÉ—uwa, a can gaba da nisa sosai ya cin masu, ya wanke jikin dake jikinsa, ya wanke face nasa sosai, ya yi salloli dake a kansa da sauran abubuwa, ya saki dark black cuirly hair nan nasa, ga shin ma yanzu ta kara tsawo sosai, ya jima bai rage tsawonta ba.
Ya sha ruwan mamaki yanda ya rinƙa ganin zanen face nasa a wannan daji, abin ya yi matuƙar burge shi, wani irin azababben kaunar Meeshantasa ya kara ji a ransa, burinsa kawai ya je gida ya ganta, yana tsananin kewarta, ji yake yi kamar a kan kaya yake da bata nan a kusa da shi, baiwar Allah, duk ta bi ta zane face nasa abinta, ba shi kaɗai ya yi mamaki ba, har da sauran abokan tafiyar tasa, kowa ya yi matuƙar mamaki na ganin zanensa a jikin itatuwan dake a dajin, ga zanen ya fito ɓaro ɓaro gwanin birgewa, kamar ka kira shi ya amsa, sai dai babu wanda ya yi gigin yi mashi magana a kan zanen, ko Areef bai yi mashi maganar ba, dan bai ga fuska ba, ya bari sai sun je gida, idan suka huta zai yi mashi tsiya a kan zanukan, sojojinsa sai kallon zanen suke yi suna satar kallonsa, Meesha ta ja mashi, Allah ma yasa sojojin kwara biyu ne kawai suka gani, sai Mark wanda already ya san komai.
A haka suka kwashe kwanaki suna tafiya a cikin wannan dajin, banda ƴaƴan itatuwa babu wani abin da suke ci. Da kyar suka iya kaiwa cikin wani ɗan ƙaramin kauye dake kusa da dajin.
Tun da suka sako kafafuwansu a cikin wannan kauye, kowa dake cikin kauyen ya zuba masu idanu, sai kallonsu suke yi tamkar sun ga bakin halittu daga wata duniya ta daban, su kuwa ko kallon mutanen kauyen basu yi ba, suka cigaba da tafiya a galabaice.