← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 168

Sashe 149

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani hamshakin alkali ne dake tsaye a wajen nasa speaker ne ya fara magana cikin ƙwararriyar turancinsu wadda tamkar a bakinsu aka kerata. Sallama irin tasu ta Kristen ya yi kafin ya fara da karantowa Lion ɗin abubuwan da ya shafi doka da kuma alkawarin da zai yi ma'ana ya fara karanto mashi cewa "Ni Saif William Jacob, a rana irin ta yau, a gaban dubbanin al'umma, na yi alkawarin rike kasa ta da gaskiya da amana, na yi alkawarin kawo mata dukkan wani cigaba, na yi alkawarin tallafawa talakawa da kula da rayukansu". Irin abubuwan da alkalin yake karanto mashi kenan, Lion ɗin yana maimaitawa cikin wannan cool voice ɗin nasa, tamkar baya son yin magana, da alama ma duk jikinsa a mace take, kuma hakan ce, zuciyarsa tana buga mashi, yana jin tamkar wani abin zai faru da shi, hakan ce ta kashe mashi jiki sosai.

Gabaɗaya ko'ina ya yi tsit, tamkar babu kowa a cikin wajen, duk sun kasa sunne suna sauraton zazzaƙar muryarsa yana maimaita abin da wannan alkalin yake faɗa.

Bayan wannan alkalin ya gama jawabinsa, sai aka buƙaci da Lion ɗin ya faɗa da bakinsa abin da yake so da kuma muradin yi wa kasarsa, wanda kuma dama shi ne a rubuce a jikin takardar da wancan lauya na ɗazun ya bashi yaki karɓa, shi kuma yaki karɓa ne domin ba'a aiki a takarda yake da buƙata ba, baya son kowa ya rubuta mashi abin da zai yi, zai faɗi kayansa da bakinsa, kuma zai jaddada hakan a aikace da izinin Allah, hakan yasa yaki karɓar takardar da lauyan ya bashi, sai kawai ya gyara tsayuwarsa tare da kara matso da Rimsha jikinsa sosai, sannan ya fara magana a daf bakin speaker tasa cikin kwarewa tare da sanyayyar muryarsa.

Daga nan ya buƙaci daddyn Rimsha ma ya zo ya yi nasa alkawarin a matsayinsa na vice president. Haka kuwa aka yi, suka iso wajen shi da mummyn Rimsha, duk da cewa face ɗin Rimsha na sanye da face mask, amma tsabar gulma irin na jama'a sai da suka iya gane cewa sir Nawazuddeen da mummy iyayenta ne, dan kuwa duk wanda ya ga kwayar idanun mummyn Rimsha ya ga na Rimsha sai yasan jini guda ne, yanzu duniya an daina kiwon dabbobi, an dawo kiwon mutane, tsabar gulma da sa ido har sun iya gano cewa vice president dai mahaifin First Lady ce, abin ya yi mugu mugun basu mamaki, wasu kuma abin ya burgesu sosai, musamman ƴan mata, sun ji matuƙar daɗi yadda Lion ya kasance a tare da surkunayensa inuwa ɗaya, a haka ma basu san cewa uncle nasa bane, su dai sun gansu kawai, kuma basu isa su tunkari wani daga cikin familyn da nufin su tambaye shi ba, sai kawai suna ta canki canka.

Cikin ƙwararriyar turanci daddyn Rimsha ya fara magana, dayawa daga cikin jama'ar wajen sun yi mamakin yadda aka yi harshen daddyn Rimsha bata da banbanci data Lion ɗin wajen magana, turancinsu iri ɗaya, ga shi dai suna yi wa daddyn kallon bakin fata, basu san cewa shi ma daddyn harshen nasa duk irin nasu bane, zaman Nigeria yasa ma harshen ta fara sauyawa, domin zamansa a Nigeria yaruka dayawa sun hau kan harshen, ba dan haka ba ai da duk ɗaya ne.

His Excellence ne ya kariwo wajen a in da ya miƙawa Lion ɗin hannu suka gaisa kafin daga bisani ya miƙa mashi takardun gwammati, waɗan nan files ɗin su ne suke nuna cewa ya miƙawa Lion ɗin mulki kenan kamar yadda doka ta tanada!! Sai kallon juna suke yi, His Excellence dai nasa kallon kamar da biyu, kamar ya shirya wani abin, shi kuma Lion nasa kallon tamkar wanda yake isar wa da kakan nasa sakon cewa lokacin wasa ya fara. To babbar magana, kaka da jika ne fa.........🥱

Bayan sun kammala duk wasu alkawaruruka ne manyan manyan shuwagabannin kasashen da suka halarci taron suka fara isowa wajen domin su gaisa da His Excellence Saif William and His vice Sir Nawazuddeen.

Wata Prime Minister kasar England ce ta kariso wajen, kyakkyawar macece mai ɗan shekaru da a kallah zasu kai 40 to 45. Tana zuwa ta miƙawa Lion ɗin hannu domin su gaisa, dama kunsan su haka al'adarsu take, hakance taya murna, ƴan jaridu sai kashe masu hotuna ake yi, ga live kowa yana ganin me yake gudana a cikin fadar.

Miƙa mata hannunsa Lion ɗin ya yi da nufin su gaisa, kamar a mafarki ya ji Rimsha ta saki ɗayar hannun nasa da ta rike tana ƙoƙarin juyawa ta bar wajen. Ai kuwa wannan Prime Minister ta kawo hannunta kenan zata rike nasa hannun ya yi saurin kaucarwa ya riko hannun Meesharsa dake ƙoƙarin barin wajen, ya bar hannun Prime Minister a saman iska tana kame..........(😂 Gaskiya Lion da Rimsha ƴan duniya ne, ya shanya hannun mata basu gaisa ba🤔😂)

Kamo hannun Rimsharsa ya yi tare da jawota jikinsa yana kallon idanunta. Cikin harshen Hausa ya furta mata. "Ina zaki je?".

A dubu ɗari ta yi wani irin zaro idanu waje, mamaki ne ya bayyana a saman face nata, ya aka yi ya iya Hausa?. Ba shakka yana jin Hausa tun bai je Nigeria ba, yana jin yaruka da dama waɗan da suka ɗaukaka a duniya, sai dai Hausar ba sosai ba, sama sama yake ji, and kuma duk cikin QUADRUPLE shi ne kawai yake jin Hausar, su Areef basa ji, bai taɓa magana da yaren da wani ba sai yau da ya yi mata.

Ganin ta tsare shi da idanu ne yasa ya É—an yi kasa da face mask nasa ya hura mata iskar bakinsa a idanun nata. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Noorish shi ne zaka gaisa da wata ina wajen ko? A gabana". Ta yi mashi maganar cikin harshen Hausa ita ma.

Mayar da face mask nasa ya yi yana faÉ—in. "Ki yi mun magana da English, Hausar kaÉ—an na iya, yanzu haka ban ji me kika ce ba". Ya yi maganar cikin harshen turanci.

Hararar wasa ta wurga mashi, dama ba wani kwarewa ya yi a Hausar ba, kawai neman magana ne.
Ganin yawan hasken cameras a saman face nasu ne yasa ya ɗan saketa tare da riƙo hannunta suka juya ga jama'a, sai a lokaci ya fahimci ashe wai ya ci mutuncin Prime Minister kasar England daya barta shanye da hannu a saman iska tana jiran su gaisa, kawar da kansa daga kallon jama'a ya yi abinsa, dan shi a kan Rimsharsa sun daɗe basu ce duk abin da suka ga dama ba, matsakarsu ce, dan shi bashi da lokacin shirmensu.

After some minutes an kammala taro za'a wuce wajen cin abincin da aka kawata aka shirya shi shiri na musamman a cikin wani katafaren hall dake a cikin fadar, kujerun da aka tanadawa His Excellence da First Lady ya yi bala'in É—aukar hankali jama'a a wajen, abin ya kawatar.

Zama suka yi cikin class da izza suka fara cin abinci, sojoji ne ta ko'ina suke serving nasu abincin. Sai da kowa ya ci ya ƙoshi, abincin da aka shirya masu kawai ya kai kuɗin budget na state, an kashe kuɗi ba karya.

Bayan an kammala komai jiga jigan sojoji ne suka raka su Lion zuwa gida, dan ba yau zai dawo white house da familynsa ba, a cewarsa su barshi ya sa rana tukun nan. Bayan motocinsu sun tashi sai motocin jiga jigan sojoji sama da guda goma suka rufa masu baya, a can gaba kuma motocin Æ´an'sanda ne suka wuce gaba, ta ko'ina jiniya aka sake tamkar filin yaki zasu tafi.

Suna isa gida family suka É—unguma suka wuce cikin parlourn kamar yadda suka fito, jiga jigan sojojin nan kuwa suka kewaye gidan ta ko'ina, ga jiga jigan bindigu a hannunsu, abin dai ba'a magana.

Bayan sun shiga parlourn ne Lion ya ce "Where's uncle? I want us to discuss something". Ya yi maganar yana kallon su Areef da suke ƙoƙarin zama a saman sofas.

Nan fa kallo ya koma kallon kallo a cikin parlourn, ina daddyn Rimshar yake to? Babu shi kuma babu mummyn Rimshar ma.

A dubu É—ari Lion É—in ya juyo da kyau tare da sake hannun Rimshar yana bin familyn da kallo, sai juye juye suke yi suna neman daddyn.

A hanzarce Areef ya ciro wayarsa, jikinsa har tana kerma wajen kunna hasken screen ɗin wayar, da kyar ya iya laluɓo number daddyn domin ya kira, a tunaninsa ko dai daddyn yana wani waje mafi kusa ne, dan yasan babu familyn da ya rage a waje bai shigo cikin parlourn ba, sai dai idan a white house suka baro daddyn.

Sai dai kuma ko da ya kira number daddyn, a kashe wayar take, tamkar zai yi hauka ya sake gwada kira, amma a kashe, shi ma Aseef a dubu ya saki hannun Akila tare da fito da nasa wayar.

Shiru Lion É—in ya É—an zuba masu idanu yana kallonsu, wani irin azababben sara mashi kansa ta fara yi, ji yake yi ma wani irin jiri tana É—ebarsa, cikin hanzari ya ce su kunna mashi Tv da yake a parlourn bari ya ga lokacin da aka rantsar da su da duk abin da ya faru a wajen, tun da live ce, so tana nan kuma yasan gidan jaridu zasu yi ta maimaitata ne.

Uncle T ne ya kunna Tvn, gabaÉ—ayansu sun kasa zama, suna tsaye cirko cirko, kowannansu tashin hankali ne ya fara bayyana a saman face nasa.
Chapter 149 · 0% Book details