Sashe 64
Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A takaice dai sai misalin karfe 3 na yamma, sannan jirgin helicopter ya iso, basu ɓata lokaci ba wajen tafiya, Ayla dai sai ruwan hawaye take yi, cikinta tsananin ciwo yake yi mata, baiwar Allah bata taɓa jin azaba irin haka ba, dan cikin nata ba ƙaramin ciwo yake yi mata ba, shiyasa ma ta kasa daurewa har take kuka. Areef bawan Allah shi ya yi ta fama da ita, ya yi ta rarrashinta har suka dira a cikin Kaduna.
Already su Imran suna airport suna jiransu. Basu ɓata lokaci ba suka fito suka nufi gida, dan akwai majinyata sosai a tattare da su, shi kansa Lion ɗin kamata ya yi ace yana kwance a gadon asibiti, amma saboda dakiya da taurin zuciya tare da karfin imani, yasa ya dake, ya ki yarda ma kowa ya duba shi, ya ce sai ya dawo gida kawai.
Gabaɗaya family suna tsaye a harabar gidan suna jiran isowarsu, Rimsha, Jehan, Anaya, su ne kawai basu a cikinsu, suna ɗaki suna barci, Jehan da Anaya sun ci kuka sun ƙoshi ne har barci ya yi awon gaba da su, ita kuma Rimsha already kun san matsalar da take a ciki, an yi mata ruƙiya ma, amma shiru, farko sun ɗauka aljanu ne suka shafeta, sai da aka yi ta yin ruƙiya aka ji shirune yasa suka fahimci ba aljanu bane, wata matsala ce dai ta daban, dan haka sai suka kyaleta sai Lion ɗin ya dawo, dan sun san halinsa, kada su kira malami ko a kaita wajen magani ya dawo ya sauke masu kwandon aradu a kansu, dan ba ƙaramin aikinsa bane ya ce uban waye ya ce a taɓa mashi matarsa? Waye ya ce wani ko wata ya zo ya dubata? To gudun kwandon bala'insa ne yasa suka bar mashi kayarsa, ya zo ya san yanda zai yi da ita.
Suna dira a gida, Lion ne farkon da ya fara fita daga cikin motar, tun motar bata gama tsayawa a parking space bama ya fice abinsa. Sam bai bi ta kan kowa dake tsaye a wajen ba, cikin gida ya wuce abinsa, kai tsaye bedroom nasa ya wuce. Yana shiga ya nufi toilet, wanka ya yi a gurguje, sannan ya fito ya shirya cikin three cuter sky blue da singlet, singlet É—in fara ce tas, tamkar yanzu ya cirota daga ledarta, abin da ya sanya ya saka singlet É—in kuma, saboda ciwukan dake a kirjinsa.
A box ya ɗauko tare da zama a gefen bed nasa, dan hannunsa in da wuka ta yankar nan ba ƙaramar ciwo take yi mashi ba, hannun ta kumbura, kun san wuka da akwai dafi a jikinta, hakance tasa hannun ta kumbura sosai.
Family kuwa, cikin tsananin murna suka fara rungumar juna, kowa baki ya ki rufuwa, saboda tsantsar farinciki. Areef yana É—auke da Ayla a saman kafaÉ—arsa, bai wani tsaya a wajensu ba, sai ya wuce izuwa cikin gida kawai, dan ya kwantar da ita, ta huta.
GabaÉ—aya family sun sha matukar mamakin ganin Aseef a tare da su, sai dai kuma sun kasa iya tambayarsa ya aka yi hakan? Ga tambayar a cikin ransu, amma ta kasa fitowa fili, abin ya É—aure masu kai, amma haka suka hakura suka daure.
Sai rungumar Dr Salman suke yi tamkar za su mayar da shi cikinsu, Brr Naurat har da ruwan hawaye, sai tsiya su Imran suke yi mata.
Shi ma Dr Salman ɗin ya sha kuka ba kaɗan ba, dan bai taɓa tunanin familynsa suna a raye ba, ya yi zaton komai ya kare ya lalace masu, ashe dai sunanan, sun zama taurari zakarun gwajin dafi ma a cikin al'umma, wannan abin ya yi mugun sanya shi farinciki wanda baki ba zai iya furtata ba. Haƙiƙa farincikin da wannan family suke ciki a yau, sam baki ba zai iya furtata ba, ya wuce misali.
Haka Dr Salman ya rinƙa yin kuka yana faɗin kowa ya yafe mashi, ina Nawazuddeen ɗinsa? Dan Allah Nawazuddeen ya yafe mashi. Anyi anyi ya yi shiru yaki yi, ya ce har sai Nawazuddeen ya yafe mashi. Haka daddyn Rimsha ya rungume shi yana faɗin. "Daddy ni baka yi mani laifin komai ba, idan ma kayi, to ni na yafe maka, ban taɓa ji a ra'ina kamar ka taɓa yi mani laifi ba, kullum cikin yi maka addu'a da fatan alkhairi nake yi, dan Allah ka dai'na kukannan kada ka saka muma muyi kukan".
Sosai Dr Salman ɗin ya rubgume shi yana mai cigaba da matsar kwallah. Da kyar suka samu suka lallaɓa shi ya yi shiru, a tare suka rankaya izuwa cikin gida, kai tsaye bedroom na Lion suka nufa, while shi kuma Areef ya kai Ayla ɗakin gwaggo ya kwantar da ita a kusa da Rimsha, sannan shi ma ya fito izuwa bedroom ɗin na Lion ɗin.
Lion yana zama a bakin bed ɗin nasa yana ƙoƙarin fara duba hannunsa, sai ga family gabaɗaya sun shigo cikin ɗakin, duk sun biyoshi, gabaɗaya fuskokinsu ɗauke yake da tsantsan annuri da farinciki, yau Dr Salman ya dawo cikinsu, ga shi ba su rasa ko mutun ɗaya ba a cikin ƴaƴan nasu, abin ba karamar daɗi ta yi masu ba. Sun shigo ne dan su duba lafiyar Lion ɗin, dan kunga shi bai tsaya a wajen nasu ba, suna sauka ya wucu bedroom nasa kawai.
Kallo É—aya Lion É—in ya yi masu ya kawar da kallonsa gefe guda, ya cigaba da aikin da yake yi.
Ganin abin da yake ƙoƙarin yi na yiwa kansa magani ne yasa gwaggo da Areef suka kariso kusa da shi da sauri. A tare suka zauna a gefe da fefensa, suka sanya shi a tsakiya kenan.
Gwaggo ce ta fara karɓar A box ɗin tare da kama hannunsan tana dubawa, ba shakka ya ji ciwo sosai. A hankali ta ɗago da kallonta a kansa, hannu ta kai ta shafa lallausan kumatunsa kafin ta ce "Let me do something". Shiru ya yi bai yi mata magana ba, ya dai zuba mata idanu, shi ya mance da cewa ita ma babbar likita ce kamar daddynsu, sai da ta ce bari ta yi mashi wani abin ne yasa ya tuna ashe ita ma babbar likita ce sosai, dan haka sai ya miƙa mata hannun ya bita da idanu kawai.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta fara yi mashi aiki, duk wani magani da zata zuba mashi sai ta ɗago kai ta ce mashi sannu, dan tasan da akwai bala'in zafi ba kaɗan ba, bare kuma yanda hannun ta ɗauki lokaci, ta jiƙa sosai ciwon, dole zai sha zafi, sai dai kuma shi wayarsa ma ya ɗauko yana latsawa da hannu ɗaya, a cewarsa duk zafinta bata kai harbin bullet zafi ba, dan haka shi bai ga abin cewa da zafi a nan ba.
Haka gwaggo ta yi mashi treatment na wajen da kyau da kyau, sannan ta ce ya kwanta bari ta duba lafiyar jikinsa gabaÉ—aya. Sai sannu family suke yi mashi, sam bai É—aga idanu ya kalli ko mutun É—aya daga cikinsu ba, dan yana cikin wani irin yanayi wanda shi kaÉ—ai yasan me yake ji bawan Allah, da yake shi kullum a siffa É—aya yake ne yasa sam sam ba wanda ya gane cewa yana cikin tsananin damuwa, kullum face nasa a haÉ—e take, baka gane farincikinsa bare bakin ciki, harta TRIPLETS nasa ma basu iya rabe yana cikin farinciki ko bakin ciki, saboda kullum dai yanda yake a haka yake babu canji.
Bai yi wa gwaggo musu ba, ya miƙe ya kwanta a saman bed ɗin da kyau, dan a agajiye sosai yake. Duba lafiyar jikinsa ta fara yi ita da Areef, ya rufe idanuwansa yana tunanin duniya.
"Momma where is Meesha?". Kamar daga sama su gwaggo suka ji sanyayyar muryarsa ya gefo masu wannan tambayar, ya yita kuma idanuwansa a lumshe.
Kallon kallo jama'ar cikin bedroom É—in suka fara yi, ita kanta gwaggon sai da gabanta ya faÉ—i na jin tambayar nan tasa. Ganin yanda suke kallon kallo a tsakaninsu ne yasa Aseef da Areef har suna haÉ—a baki wajen cewa "What is happening? Where is our Rimsha? Ya naga kuna ta kallon juna, is there any problem?". Kamar abin haÉ—in baki suka jera masu tambayoyin, Areef kam har da mikewa tsaye yana binsu da kallo, dan wlh idan wani abin ne ya sameta yau za'ayi yaki ba kaÉ—an ba, saboda ita É—in tamkar bugawar zuciyar TRIPLETS É—in take, dukkansu ukun suna tsananin sonta fiye da tunanin mai tunani, akwaita da mugu mugun shiga rai na wuce misali ne.
Kara datse idanuwansa gam Lion ɗin ya yi, kansa na yi mashi ciwo sosai, yana jin duk abin da suke faɗa, amma ya kasa buɗe idanuwansa, dan ƙwaƙwalwarsa ba zata iya ɗaukar wani abin ya sami Rimsha ba, shiyasa ma ba zai buɗe idanu ba bare ya ga fuskokin family su kara jefa shi cikin wani raɗaɗin.
"Areef nothing happened to her, just she is not feeling well, tana ma cikin bedroomna tana kwance, she is sleeping now". Cewar gwaggon kenan.
Kusan a tare Aseef da Areef ɗin suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya, da sauri Aseef ya ce bari ya je ya ganta ya tabbatar. A tare suka fita da Areef ɗin dan su je su dubata. Ita kuma gwaggo, sai ta cigaba da duba ɗan nata, Dr Salman ne ya ce su fita su bar Lion ɗin ya huta, dan ya gaji matuƙa. Haka kuwa aka yi, duk suka fita, ita ma gwaggon da ta gama yi mashi duk abin da ya dace, sai ta fita ta kyale shi, yana jin fitarta, amma bai ce mata komai ba, saboda yana da bukatar ya huta ɗin ne, ga salloli na la'asar da mangariba a kansa bai samu ya yi ba. Ransa cike da tunani barci ya yi awon gaba da shi, bawan Allah ya yi matuƙar gajiya na wuce misali, dole ne ma barci ta ɗauke shi.