← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 168

Sashe 28

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Donal Aseef ya kira cikin kuka, ya ce mashi ya ɗauko mota su bi su TGA, sai ringin wayar Aseef ɗin take yi, amma ina hankalinsa baya a tattare da shi, kuma Areef ne yake kiransa, dan ya kira wayar Lion yafi sau a kirga, amma bai ɗauka ba, shi ne ya kira Aseef ɗin dan ya ji ko lafiya, saboda a jikinsa yana jin tamkar basu lafiya, kamar akwai wani abin. Amma ina Aseef ɗin ma yaki ɗaukar kiran, shi burinsa kawai Lion ya tashi....... MASU KARATU, WANNAN SHI NE ASALIN CAKWAKIYA, LITTAFIN TRIPLETS YANZU ZAI ƊAUKI ZAFI JAU KAMAR WUTA, KADA KU MANTA BOOK 4 MUKE, KUMA SHI NE LAST IN SHA ALLAH, TO MUNA FATAN AYI KOMAI A NAN A GAMA, HAR KULLUM PRINCESS TEEMA TAKU CE TA AMANA.💋

Gwaggo babu ko mayafi a kanta, daga É—ankwalin doguwar rigar jikinta, shikenan, haka ta bi su a motar Donal É—in. Bayansu TGA suka bi, Uncle Herry kuwa, yana can yana kula da Dr William, bai ma san abin da yake faruwa ba, John da Jay kuwa basu ma a gidan gabaÉ—aya, sun tafi yawonsu!. Rimsha sarkin rigima, tana can tana barci ga Noorish nata tamkar rai ya yi halinsa!

WANNAN KENAN, ABIN DA YAKE FARUWA A GIDAN LION, BARI MU LEƘA GIDAN ABBO, WATO WAJENSU DR NAWID, WATA KILA KAFIN MU DAWO, ABUBUWA SUN ƊAN YI SANYI, GIDAN ABBA BA SAUKI, AYLA TA ƁATA, GIDAN LION KUMA YA MA KAMA DA WUTA BAL, BAL NE MA GABAƊAYA, SABODA BALA'IN TASHIN HANKALI DA SUKE A CIKI, TO BARI MU JI GIDAN ABBO KUMA KO DA ƊAN SAUKI SAUKI.

GIDAN ABBO.

GabaÉ—aya familyn Abbo, wato Ummi, Dr Nawid da Aafia, suna a cikin tsananin tashin hankali, suna tsaka mai wuya, yau tsawon kwana uku kenan Dr Nawid yana kwance rai a hannun Allah, ko motsawa baya yi, ga idanuwansa a buÉ—e garau, amma baya iya ko motsawa, likitoci daban daban Ummi ta kira, amma kowa ya zo, sai ya ce babu wani abin da yake da munsa, su basu ga ciwon komai ba, ga shi Abbo dai baya nan, shiru babu shi babu labarinsa, haka Ummi ta daure ta fara shirye shiryen fitar da Nawid É—in kasar waje.

Abin da ya faru shi ne, suna tsaye a kitchen suna aiki shi da Aafia, ranar bai je office ba, sai ya bita kitchen yana tanaya aiki kamar dai yanda suka saba, sai zuba soyayyarsu suke yi kamar ba gobe, bawan Allah lafiyarsa lou wlh, babu ko ciwon kai a tattare da shi. Haka kawai ya yanke jiki ya faÉ—i kasa, sai wani bakin ruwa ya fara fito mashi daga bakinsa, abin ya yi mugu mugun girgiza su Ummi, Aafia ba'a magana, ta yi mummunar rama yarinyar nan, dan kun sani, tun farkon littafin nan, tana bala'in son Dr Nawid, Ummi kuwa, shi kaÉ—ai ne ke gareta, bayan shi bata da wani yaro, dole ta shiga tashin hankali na wuce misali, bayin Allah, wannan shi ne abin da ya faru.

Sai shirin fitar da shi kasar waje suke yi. Yau ta kasance ranar Friday, bayan an sauko daga sallar jumma'a, Aafia tana zaune a gefensa a saman bed nasu, ta yi mashi alwala dan ya yi sallah ko da da idanu ne, dama haka take yi mashi kullum, tana yi mashi alwala idan lokacin yin sallah ya yi, ita kuma Ummi bata nan, tana gidan Abbin Irfan, dan suma sun san abin da yake faruwa, Abbin ne ma yake shirya masu fita kasar waje dan neman lafiyar Nawid É—in, so ta je su yi magana da Abbin.

Shiru Aafia ta zauna tana ta kallon mijin nata, shi kuma sai kallon sama yake yi, dan ko juya idanun nasa ma baya iya yi. Hawaye masu matuƙar zafi ne suke gangaro mata daga cikin idanunta, duk ta bushe ta yi wani irin baki tamkar mai cutar kanjamau, sai idanu kawai zaka gani dara dara a face nata, duk wanda ya ganta sai ya matsa mata kwallah.

Yau tsawon kwana uku Dr baya motsawa, ta yi nisa cikin tunanin da take yi, kamar daga sama ta ji voice nasa yana faɗin "Aafia ba zan tashi ba, mutuwa zan yi, ki yafe mani idan na taɓa yi maki wani laifi, sannan ki roka mani gafara a wajen Ummi, ta yafe mani, ina tsananin sonku, amma ba zan rayu da ku ba, sannan ki sani wannan cuta da ta kamani........" Bai kai karshen maganar ba ya sake yin shiru ɗiff tamkar an ɗauke wutar nepa.

Tun da ya fara magana, a tsakanin razane Aafia ɗin ta ɗago tana kallonsa, still idanuwansa suna kallon sama, sun kafe, bai iya motsasu, kuma bakinsa ma bata motsawa, kawai dai ga muryarsa nan tana fitowa ana magana da ita, amma sam sam babu wata gaɓa da ta motsa daga jikinsa!. Toh fa!!

Ta tsorata sosai na ganin hakan, sunansa ta fara kira, Yah Nawid, Yah Nawid, amma ina shiru bai amsa mata ba, tana ƙoƙarin ta sake yi mashi magana, sai ta ga idanuwansa sun sauya color izuwa purple eyes. Zaro idanu sosai waje ta yi, tamkar idanun nata za su fito su faɗi kasa, tana ƙoƙarin gudu ta sauka kasa, sai ta sake ganin idanun nasa sun sake sauyawa izuwa bakin kirin, babu ɗigon fari ko kaɗan a cikin idanun nasa, wani irin hayaki ne mai matukar warin gaske ya fara fitowa daga bakinsa, bakin ruwa mai kaurin gaske ya fara zuba mashi daga hancinsa, haka zalika kunnuwansa ma hayakin ne ya fara fitowa.

Wani irin uban ihu ta zunduma tare da sauka kasa da uban gudun gaske, a dubu ta nufi waje. Tamkar zararriya haka ta bazama izuwa harabar gidan, dai'dai lokacin kuma motar Ummi ya danno kai, ta dawo daga gidan Abbi, ta je ma bata samu ganawa da shi ba, saboda suna cikin tsananin tashin hankali na ɓatar Ayla, so suma yau ba'a zaune suke ba.

Ganin yanda Aafiar ta fito a gigice tana zunduma ihu ne yasa Ummi ta dakatar da motarta ba tare da ta karisa parking space na gidan ba. A hanzarce ta fito daga cikin motar, Aafia kuwa bata ma bi ta kanta ba, ta nufi waje da gudu, tamkar ƙwaƙwalwarta ya taɓu ne, da alama ta zauce.

A hanzarce Ummin ta ce mai gadi ya rufe gate É—in, kada ya bari ta fita, sannan ta yi maza ta rikota tana ambatar sunanta, amma ina banda wannan ihu da take zunduma, babu wani abin da take yi.

Da kyar Ummin ta jata izuwa cikin palo, É—aki ta sakata ta rufe kofa, sannan ta É—auko wayarta, cikin tsananin tashin hankali ta kira Abbi dan ta sanar da shi abin da ta zo ta tarar a gidan again.

Ta yi sa'a ya É—aga kiran, bayan ta gaya mashi, sai ya ce mata to Akil yana zuwa yanzu, daga haka suka yi sallama, sannan ta kira Æ´an uwanta a Katsina ta gaya masu halin da yau kuma suke a ciki.

A palonta ta zauna, ta kasa shiga ta sake duba Aafiar, shi dama Dr Nawid bata san me yake faruwa da shi ba, bata san me Aafiar ta gani ta haukace haka ba, baiwar Allah, tana zaune ta buga uban takumi tana jin yanda Aafiar take yi mata watsi da kayan É—aki har Akil ya kariso.

Tana ganinsa ta miƙe a hanzarce tana kara yi mashi bayanin abin da yake faruwa. Ina Aafiar ya tambaya, da sauri ta nuna mashi ɗakin da take, ba ɓata lokaci ya nufi cikin ɗakin.

Yana buɗe kofar Aafiar tana gefo mashi kwalbar perfume a goshinsa, nan take ya fashe wajen, jini ya fara tsastsafa. Salati Ummin ta fara yi, komai na cikin ɗakin Aafiar ta yi watsi da shi, har kayan jikinta ta cire, ya rage daga ita sa underwears, suma sai ƙoƙarin ciresu take yi.

Sam Akil bai damu da ji mashi ciwo da ta yi ba, karisawa cikin É—akin ya yi tare da yin bismilah ya damkota da karfi, kokawa ta fara yi da shi da iya karfinta, shi ma saka karfi ya yi sosai ya murÉ—e hannayenta izuwa baya, sannan ya kaita kasa, dan ta kwanta, hakan zai taimaka mashi wajen danneta ya yi mata addu'a.

Ummi kam ban da kuka babu abin da take yi.

"Ummi jeki waje". Cewar Akil É—in, dan ya lura idan bata bar wajen ba, ba zata dai'na kukan ba. Jiknta har kerma yake yi ta koma palo ta zauna. Shi kuma ya fara tofawa Aafia É—in adduo'i har barci ya É—auketa a wajen.

Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali na ganin ta yi barci, runtse idanuwansa ya yi yana tunanin meyake shirin faruwa da FAMILYNSU ne? Ayla ta ɓata, gwaggo ta kira waya cikin tsananin tashin hankali ta sanar masu Lion yana asibiti tamkar babu rai a tattare da shi, yanzu kuma ga Aafia ta haukace, anya kuwa ba wani gagarumin bala'in bane yake shirin afkuwa? Anya lafiya kuwa? Meyasa kuma dukka abubuwan a lokacin guda rana ɗaya?! Sannan a hankali abubuwan suna ta shafar kowa da yake a cikin familyn? Wai shin menene gaskiya? Waye zai warware mana wannan rikicin?........ Alkalami PRINCESS TEEMA ce kawai zai warware maku menene ainahin abin da yake shirin faruwa dama wanda yake faruwa a yanzu, ku dai ku kasance tare da ni!!.

Ganin ta yi barci ne yasa ya saketa tare da fitowa palo wajen Ummi, har lokacin sai kuka take yi, hakuri ya bata tare da tambayarta ina Dr Nawid yake bari ya duba jikinsa, sannan zai wuce gida da Aafiar dan a ragewa Ummin wahala.

To kawai ta ce mashi, sannan ta wuce gaba zuwa É—akin Dr Nawid É—in, bayanta ya bi cike da tausaya mata.

Baki ɗauke da sallama suka shiga, yana kwance tamkar yanda yake kullum, idanuwansa sun koma yanda suke, kamar basu taɓa canza launi ba, wannan hayaki da Aafia ta gani ta zauce, duk sun dai'na fita, komai ya ɓace, ya koma kamar yanda yake.
Chapter 28 · 0% Book details