← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 168

Sashe 13

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alluran ya yi mata kafin nan ya ɗebo kayan aiki, da kansa ya gyara ɓarnar da ya yi tare da duk abin da ya kamata. Bayan ya kammala ya tattare komai ya mayar, sannan ya je ya yi wanka, ya shirya cikin pajama ya dawo kusa da ita ya kwanta tare da jawota jikinsa ya rungume gam yana mai jin tsantsar farinciki tare da godiya ga Allah da ya sanya shi ne ya karɓi budurcin matarsa, dama idan baku manta ba, su da wuya ka sami mace virgin a wajensu, hakan tasa ya ji tsantsar farinciki na wuce misali, ji yake yi tamkar ya mayar da ita cikin cikinsa saboda so da kauna.

Haka suka kasance shi ma barci ya daukesa rungume da ita. Ba su suka farka ba sai da Josephine suka dawo can rana ya yi sanyi wuraren laasar. Josephine ɗin ce ta tashesu dan taga basu yi sallar la'asar ba ga rana na dab da faɗuwa, ita kuwa sallar la'asar ba abar wasa ba ce, Allah ya yi rantsuwa da sallar, duk halin da zaka shiga, kada ka taɓa barinta sai rana ta faɗi kayi ta. Wasu hadisai sun ce idan rana ta faɗi ma ko kayita ba'a karɓa, wasu kuma sun ce sai dai ka hakura gobe ka rama, annabi ya ce munafukai ne kawai suke bari sallar la'asar ta wucesu, dan sallah ce mai matukar muhimmanci, kada ku manta har rantsuwa da ita Allah ya yi, kunga kuwa ba abin wasa ba ce ita ɗin. Allah ka bamu ikon yinta a kan lokaci!!.

Da kuka gwaggo ta tashi mashi, sabon rarrashi ya sake farawa. Sam taki kula shi, sai tambayar lafiya take kuka Josephine take yi, amma bata samu amsa ba, dan shi ma Dr yana ta faman rarrashinta ba ta kan Josephine É—in yake yi ba.

Da kyar da suɗin goshi ya samu ta yi mashi shiru. Umarni ya yi wa Josephine ɗin a kan ta fita musu a ɗaki. Ba musu ta fita, dan ta san halin yayan nata sarai, yanzu zai iya saɓa mata kamanni.

Sai lallaɓa beautyn tasa yake yi, amma taki kula shi, da alama fushi take yi da shi. Da kyar ya lallaɓata ta yarda ya ɗauketa zuwa toilet dan su yi wanka. Bayan sun fito, da kansa ya saka mata kaya, sai kumbure kumburen kumatu take yi, yau babu zancen my Dr, my Dr ya yi aika aika, haushinsa ma take ji.........NI KUMA PRINCESS TEEMA MALTINA MAI SANYI NAKE SHA, YO ME YAFI RA'INA?🤔 SOYAYYA AI DA DAƊI KO? SU GWAGGO YAU DAI AN GA RIBAR SOYAYYA😂

Bayan sun yi sallah ne ya kawo mata lunch ɗaki da kansa, ƙin ci ta yi, da kyar ya lallaɓata ta sha tea kawai. Bayan ta sha komawa saman bed ta ce zata yi. Cikin hanzari ya dauketa zuwa saman bed ɗin. Haka suka kasance har tsawon kwana uku yana lallaɓata tare da jinyar kayarsa, ita kuwa sai wahalar da bawan Allah take yi.

A takaice dai wannan abin da ya shiga tsakanin, ba karamar son junansu ya kara musu ba, irin soyayyarnan da ake cewa a mutu a kan juna suke yi wa junansu, abin ba'a magana. Haka suka cigaba da rayuwa tsawon shakara ɗaya da rabi. A lokacin saura shekara ɗaya da rabi su kammala school, dan ma sun ɗaura master nasu ne, ai da ba'a haka ba, da sun jima da barin school ɗin. Ga shi karatu suke yi babu wasa, ga ilimi, dukkansu akwai kaifin ƙwaƙwalwa na wuce misali, tamkar su suka bawa kansu. (Ai dole TRIPLETS su kasance suna da basira, ba'a kasa suka tsinta ba, gado suka yi daga wajen iyaye!!)

Yanzu gwaggo kwata kwata ta dai'na samun labarin gida Nigeria, amma ko a jikinta, da alama ta mance da su ma bakiÉ—aya, abubuwa kuma sun faru da dama a gidan Dr Salman!.

Haka ta yi wa Dr William zanen tattoo mai shegen kyau a bayansa, shi ma ya zana mata a nata bayan, amma ta kasa kusa da mazaunanta, ya rubuta mata sunansa a wajen, ita ma ta rubuta mashi sunata a nasa bayan. Abin gwanin birgewa na wuce misali.

Babu wata matsala a tsakaninsu ko da sunan wasa. Suna rayuwar tsantsar farinciki tare da faranta ran juna. Rana tsaka ciki ya bayyana a jikin gwaggo. Nan fa bala'i ya tashi ya tsaya, nan fa Dr ya ce shi baya son ciki, baya son haihuwa, sai dai su zubar, sam shi bai shirya haihuwa yanzu ba, ita kuwa gwaggo ta ce mai rabata da cikin nan sai Allah Ubangijin da ya bata, shi kaÉ—ai ne zai iya kwatar kayansa. Ba yanda Dr bai yi ba, ta kafe sam wlh ba zata cire cikin ba, ai ba shegu bane, da ubansu, Æ´aÆ´an sunna ne! Dan haka dole ta haifesu kamar yanda aka haifeta ita ma!!. Shi kuma ya kafe ko da sonta ko babu sonta, ko da saninta, ko babu saninta, sai ya salwantar da cikin. Da ta fahimci hakan ne, sai ta dai'na bari suna kusantar juna, kwata kwata ta dai'na kula shi.

Amma fa abin ya yi mugun É—aure mata kai na cewa da Dr ya yi baya son haihuwa, ta san dai a baya yana yawan maganar yara, to how comes kuma sun sami cikin ya ce shi baya son yara? Ko dai dama a bayan ma yaran uncle's nasu kawai yake so ne? Abin ya sakata cikin tunani, wai baya son yara kwata kwata a rayuwarsa. Babbar magana!!.

(Ashe ba a kasa Lion ya tsinci tsanar yara ba! Kunga kuwa yanzu da Lion ya ce baya son yara ai bashi da laifi ko? Dan ɗan gado ne shi ɗin, ya gada komai tsab, har ma ya ninka mahaifin nasa zafi da tsauri. Lallai akwai cakwakiya, Lion baya son yara, ga shi ya kamu da son Rimsha, ko ya za su kare?🤔 Ni dai PRINCESS TEEMA ina da Maltina mai sanyi a fridge, idan suna bala'in da na ji ba zan iya jurewa ba, sai na kora maltina ta ta kwantar mani da hankali)

Wasa wasa faɗa ya yawaita a tsakaninsu har Dr ya fara ƙoƙarin illatata. Ganin zai iya illatata ita da abin da yake cikin cikin nata ne yasa ta fara ƙoƙarin barin gidan. A nan ne Josephine ta tambayeta me yake faruwa? Bata ɓoye mata komai ba, ta gaya mata, sosai Josephine ta sha kuka, dan ita tana matukar son gwaggo ta haifa musu yara, kullum tana addu'ar Allah ya bawa gwaggon ciki ta haifa musu twins, sai dai ita dama already tasan Dr William baya son yara, sam baya son hayaniya, ta san ba zai taɓa karɓar wannan ciki na gwaggon ba, dan kullum yana yawan faɗawa mum ɗinsu kafin ta mutu, yana gaya mata cewa shi da ya haifi yara, gwara ya mutu bai kula mata ba!!..... Yau ake yin ta kenan, tashin sense.

Haka Josephine ta yi ta bawa gwaggon hakuri a kan kada ta je ko'ina, In Sha Allah Dr zai sauko ya so cikin, amma ina wani muguwar tsana ma ya kara yi wa cikin na wuce misali.

Tsanar cikin ne ma har ya shafi ita ma gwaggon, ya tsaneta sosai. Daga karshe ma sai ya yi yunkurin kasheta ita da abin da yake cikin nata. A ranar Josephine ce ta tseratar da ita daga hannunsa, a in da ta gudu da ita izuwa É—aya daga cikin gidajen daddynsu, wato Jacob Roshan, suka bar Dr William uncle Herry sai TGA, ita dama Cherish bata san me yake faruwa ba.

A nan suka cigaba da rayuwa da gwaggon da ita Josephine É—in, dan ta ce wlh ba zata koma wajen Dr ba ita ma, zata zauna ta kula da gwaggon, baiwar Allah tana da tausayi sosai ga kirki na wuce misali. A lokacin Cherish tana kasarsu ta je hutu. Ita kuwa gwaggo bata je hutu ba, kuma ba'a nemeta a gida ba, dan a lokacin gidan nasu ya rushe bata sani ba, tana nan ta biyewa Dr ya kaita ya barota, da ba dan Josephine ba, da bata san in da zata sanya rayuwarta ba, da kila izuwa yanzu ma ta mutu. Allah sarki rayuwa kenan.

Hakika Gwaggo ta sha bakar azabar wahala na rabuwarta da Dr, tamkar ba zata yi rai ba, dan tana tsananin kaunarsa fiye da tunanin mai tunani. Shi kuwa yana can ko a jikinsa, sai ma sharholiyarsa da yake sha, da alama ya mance da ita ma, da alama fa dama ba sonta tsakani da Allah yake yi ba! Kawai ya yaudareta ne!. (Wata kila shiyasa su Lion basu jinsa sam sam a ransu🤔 to lokaci dai zai nuna mana komai, amma ni da ku duk mun san cewa alhaki kwaikwayo ne! Ga mutuwar su Jacob ma dai..hmmmm akwai abubuwa da yawan gaske, wlh wasu cakwakiyar idan aka ɓallo maku sai kun ji kanku ta buga!!)

PRINCESS TEEMA..✍️❤️

Da kyar tare da addu'a da taimakon Josephine gwaggo ta dawo dai'dai, da farko da ta ji wahala na soyayyar Dr dake neman hallakata, sai ta ce wa Josephine ta yarda zata zubar da cikin kawai ta koma wajen mijinta, dan ba zata iya yin nisa da shi ba. Kasancewar Josephine tana bala'in son yaran yasa ta yi ta rarrashinta tare da yi mata dabara har ta yarda ta bar ciki.

After some weeks

A haka Cherish ta dawo hutu ta same su, abin kwata kwata bai yi mata daÉ—i ba, duk sai ta ji ta tsani Dr sosai, ta kuma tsani maza fiye da tunanin mai tunani.

Zaune ta isko Gwaggon a cikin bedroom saman bed, kusa da ita ta zauna tare da fara bata hakuri. A kule gwaggon ta ce. "Cherish kin san me kike faÉ—a kuwa? Hakuri fa kika ce nayi? Wlh ba zan hakura ba, sai na É—auki fansan abin da Dr ya yi mini, wlh sai na kashe shi!".
Chapter 13 · 0% Book details