← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 168

Sashe 89

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hararar gwaggon ta yi kafin ta ce "Kawai dan ke baki jawa Dr William aji ba shi ne ni zaki hanani jan ajina? Dake da mummy duk naji tarihinku ai, ba wani jan aji da kuka yi, ita mummy tana gani daddyna kyakkywa ta ce shikenan zata bishi ita kam, kema Dr William yana É—an zuba maki kallon soyayya da waÉ—an nan blue eyes É—in nasa kawai kika ruÉ—e, ba wani jan aji kike biye mashi, to ni wlh a'a, sai na ja ajina dan ma kada ya renani, dole ya kalleni da daraja, sai na wahalar da shi". Ta kai karshen maganar zata mike ta fice daga É—akin, ko kunya bata ji ba, a gaban mahaifiyarsa take cewa sai ta wahalar da shi, duk wahalar da take bashi a yanzu bai isheta ba, ikirarin kara mashi wani ma take yi.

Rikota gwaggon ta yi tana salati, wai shin ya zasu yi da Jehan ne sukam? Yarinya ta ra'ina mutane? Wai jan aji take yi, lallai ma yarinyar nan.

Duk abin da ta faɗa a kunnuwar mummynta ta faɗa, dan mum ɗin ta shigo gaishe da gwaggo kenan ta ji suna maganar, shi ne ta tsaya a bakin kofa tana sauraronsu. Jin abin da Jehan ɗin ta faɗa ne yasa mum ɗin ta juya ta fasa shiga ɗakin, dan tasan mutun ɗaya ne a yanzu zai saita mata Jehan ɗin nan, tun farko gwaggon ce ta shagwaɓa ta, ta ɓatata, ta kuma sangarta, dan haka yazu basu isa su ce zasu tankwarata ba, Areef dai shi ne zai gyara mata zama ya dawo da ita a kan hanya tun da tana son shi, dan haka sai mum ɗin ta koma bedroom nata dan ta kira daddynsu ya haɗa ta Areef ɗin a waya tun da suna a tare, zata gaya mashi yadda zai yi mata magain Jehan ɗin ne, dan idan ba haka suka yi ba, Jehan fa ba zata gane me ake nufi da miji ba, already gwaggon ta ɓata komai.

(Gaskiya akwai cakwakiya kam, dole Areef ya saitata a kan hanya, idan ba haka ba zasu sha wahala.)

Sai misalin karfe 9:30 Lion da Tga suka dawo cikin gidan. Tga na yin parking a parking space babu ɓata lokaci Lion ɗin ya fito hannunsa na ruke da ledoji manya manya, Tga ɗin yaso ya karɓa mashi kayan, amma ya ce ya bar mashi abinsa, a haka suka nufi cikin gida.

Kai tsaye bedroom nasa ya nufa, bakinsa ɗauke da sallama ya shiga, gwaggo na bedroom nata, a saman bedside drawer ya ɗaura ledojin tare da zagayowa ya dawo ta ɗayar ɓangaren gadon, kusa da Rimshar kenan. Zama ya zo ya yi tare da zubawa face nata idanu yana kallon yadda ta kara uban haske kamar ba lafiya ba.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

Date: 7/5/2024

E26

A haka Gwaggon ta shigo ta same shi, magunguna da alluran ta fara É—auka dan ta yi aikinta, tun bata yi mashi magana ba ya tashi ya fice daga É—akin, dan yasan zata ce mashi ya fita ne, so is better for him da ya fita É—in ma.

Yana fita garden ya koma, dan ya zauna ya huta. Saman sofa mai zaman mutun uku ya kwanta tare da miƙe dogayen kyawawan fararen kafafunsa, a hankali ya lumshe dara daran idanuwansa, sai tariyo mashi komai ƙwaƙwalwarsa take yi mashi, wani irin yanayi yake jinsa a ciki, da haka barci ta ɗan sace shi, dama kunsan ita barci ba'a cin bashinta, idan ma kaci sai ka biya, so gara ma kawai lokacin yinta ka yi ta sai ya fimaka.

After 15 days. (Bayan kwanaki shabiyar)

A tsawon kwanakin nan gabaÉ—aya ko motsawa Rimsha bata yi ba, sai dai duk da tana sume tana samun sauki dai'dai gwargwado, a yanzu jikin nata ya koma normal, temperature jikinta ya dai'dai ta, wannan uban haske da ta yi ma a yanzu ta É—an koma normal colornta, duk da ba gabaÉ—aya ba. Shi ma Lion a yanzu hankalinsa ya É—an kwanta, sai dai fa har Æ´ar rama ya yi, kyakkywar jajir É—in skin nasa ta É—an yi duhu, saboda ana zuba rana a Naija ba karya, damuna ta jima da tafiya, yanzu shirye shiryen azumi suke yi, saura watanni biyu a kama azumin, so fatarsa ta É—an yi duhu, ya rame saboda ciwon na Rimsha, ga shi har tsawon waÉ—an nan kwanaki 15 É—in bata ko motsa ba, a halin yanzu mummynta tasan me yake faruwa, sai dai bata É—aga hankalinta ba, dan tasan already dama da akwai wannan rana a rayuwar Æ´aÆ´an nata, Aseef yana wajen Sheikh Sultan, kullum suna manne da waya suna aikin da suka saba shi da Akila, kamar wasu chewing gum basu rabuwa.

Har wa yau abubuwa sai kara zafafa suke yi har suna tafasa a Washington, shi kuma Lion da ya tada tarzomar, hankalinsa a kwance yana Naija abinsa, ya baro su Areef da shan aiki, daddyn Rimsha ma yana can Washington ɗin already kun sani, takardan ɗan kasa Lion ya sanya ayi mashi, da kuma sauran abubuwa da suka shafi kasar, sam Lion yaki yarda ya haɗa hanya ko da ta waya ce da su His Excellence, sun buga sun raya, amma ina ya ce bashi da lokacinsu a yanzu, lokacin zama ya yi magana da su ta wuce, a yanzu primary election sai kara matsowa take yi, saura ƴan kwanaki, kun san yanayi na juyawa, haka shi ma watannin namu suke juyawa, so a yanzu kasar U.s tana shirye shiryen yin primary election ne, kuma Lion sai kara samun goyan bayan al'umma yake yi, shi kaɗai yasan kudurinsa idan ya ci wannan zaɓen, shi kaɗai yasan me yake shirya masu.

A waɗan nan kwanaki sha biyar ɗin dukka Jehan tana ta fama da rashin lafiya, ba komai ne ya haddasa mata hakan ba kuma face shareta da Areef ya yi, sai dai babu wanda yasan da dalilin rashin lafiyar tata, saboda dakiya irin nata, ta jure ta ɓoye abin a cikin zuciyarta, shi kuma Areef ɗin ya shareta ne bisa umarnin mummynta, ita ta gaya mashi ya jure ya daure ya shareta ko da na wata guda ne, dan idan ba haka ya yi ba, tabbas zaman aurensu zai bashi wahala, Jehan ba zata san mahimmancinsa ba, ba zata ɗauke shi da daraja ba duk da tana son shi, so yana da kyau ya fara koya mata hankali tun yanzu, a cewar mummyn nata kenan.

Ita kuwa Gwaggon duk hankalinta a tashe, ga Rimsha kwance kamar gawa tsawon kwanaki, ga Jehan ba lafiya, zazzaɓi mai zafi ne kamar zata mutu, ita gwaggo baiwar Allah bata san cewa ciwon Jehan Areef ne musabbabi ba, da ta sani ai da tuni ta sanya shi ya kira Jehan ɗin, dan kun dai san Jehan ta gidan ta ne, so yana da kyau ku fahimci duk abin da Jehan take yi ba fa laifinta bane, horon gwaggonce ita, komai ta yi dai'dai ne a wajen gwaggon nata, bata laifi, so kunga kuwa ai dole a samu matsala, idan baku manta ba tun farko, tun suna Abuja ita Rimsha ta fi shakuwa ne da mummynta, shiyasa ma tafi Jehan samun ilimin addini sosai, ita kuma Jehan tana manne ne da gwaggo, shiyasa ta fi Rimsha ilimin boko sosai, to idan baku manta ba tun ainahi suna da banbanci, dan gwaggo dai kowa yasan ƴar bokoce ta gasken gaske ma kuwa, kunga kuwa dole Jehan ta so boko sama da ilimin addini, dan ma dai an yi sa'a ita ma gwaggon akwai ilimin addinin ne, sai dai na bokon yafi yawa.

A takaice dai gwaggo bata san menene yake damun Jehan ba, sai faman tambayarta take yi menene matsalar, domin kuwa da ta yi mata test, results ɗin ya nuna mata cewa wannan zazzaɓi fa ba daga kwayar cuta Jehan ɗin ta same shi ba, zazzaɓi ne na damuwa da pressure ya yi mata yawa, anyi mata tambayar duniyar nan taki gaya masu menene yake damunta, dan a cewarta idan ta ce tana kewar mijinta ne ai ta zubar da mutuncinta. (E lallai baki dawo kan hanya ba Jehan, da sauranki.)
Chapter 89 · 0% Book details