← Book details Triplets Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 168

Sashe 81

Triplets Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya kammala tofa masu addu'ar ma sai da ya sake basu hot sumbata, sannan ya miƙe ya sauko kasa daga saman bed ɗin. Jibgegiyar duv nasa ya jango ya rufesu zuwa iya cikinsu, sannan ya ɗan kara masu gudun A.c kaɗan kafin ya wuce ya nufi cikin katafaren dressing room nasa, kada ku mance yanzu fa ya dawo ɗaularsa na Washington, ba irin gidansa na Naija bane, wannan dressing room nasa na nan ma kawai ta fi girman palournsu na Naija, Already kun san komai.

Kayansa ya fara shiryawa, sam bai gayawa Aseef a kan gobe zai wuce Nigeria ba, shammatarsu yake son yi ya tafi abinsa, idan ba hakan ya yi masu ba, ba zasu taɓa shiryawa da Aseef ba, dan sai Aseef ɗin ya ce zai bisa, shi kuma baya son hakan, a nan yake son barinsu, dan akwai gagarumin aikin da Areef yake yi mashi, aikine na sirri, kun san Areef fa sune sirri, to aiki ya haɗa shi da shi, yasan idan ya ce su je Naija a tare, to ba zai yi mashi aikin a kan lokaci kuma yanda ya kamata ba, saboda Jehan da Momma, zai biye masu su yi ta shirirta, shi ne yasa gara ya barsu a nan, shi kuma Aseef abin da yasa baya son su koma Naija a tare, dan baya son su baro Areef ɗin shi kaɗai a cikin gidan, ba zai ji daɗi ba, shi ne yasa zai bar mashi Aseef ya ɗebe mashi kewa kafin ya dawo.

Tsab ya shirya duk wani abin da zai buƙata, ya haɗa komai kafin ya fito izuwa saman bed ɗin, sun zo sun cika mashi bed, yau a bedroom nasa za su kwana, haka ya kwanta a kusa da su bayan ya yi addu'ar barci, tun bai kai ga tafiya ba har ya fara kewarsu, su ɗin jini ne da hanta bayin Allan, ko ina cikon QUADRUPLE ɗin nasu yake? Ya mutu ne ko yana raye? Allah masani sai kuma alƙalamina Ni PRINCESS TEEMA taku ta amana, dan haka mu kasance a tare kawai dan jin komai.

Yana kwanciya ba jimawa ya yi barci abinsa.

A gida Nigeria kuwa, washegari gwaggo ta gayawa Tga da akwai in da zai kai'su. Cikin girmamawa ya ce mata Lion ya gaya mashi tun jiya. Tun da Tga yake a rayuwarsa bai taɓa girmama wani in ma mace ko namiji bayan Lion da yake ogansa ba, sai a kan gwaggo, har cikin ransa yake jin Kaunar gwaggon, tun da ya ji cewa ita ce ainahin mahaifiyarsu Lion, daga nan ya ji yana mugu mugun respecting nata.

Shiryawa suka yi, gwaggo, mummyn Rimsha, Jehan, Akila, and Rimsha, TGA ya ɗaukesu a mota suka bar gidan, shi kuma daddyn Rimsha a yau ya bar kasar, dan Lion ya ce mashi ya zo Washington ya samu Areef da akwai abin da zasu yi a tare. (Sai shiryawa su his excellence kitimurmura Lion yake yi fa, kome su Areef suke sake shiryawa kuma?🤔 Namu ido ko my peoples?.)

Kai tsaye wani katafaren shop na gyaran gashi, lalle da kuma kitso gwaggo tasa Tga ya wuce da su. Ko da suka isa wajen yaki yarda ya jiransu a mota, har cikin wajen ya rakasu, dan ya tabbatar suna cikin lafiya da tsaro, ya tabbatar babu abin da ya samesu, dan haka sai ya bisu har ciki, sai kallon shi tsala tsalan Æ´an matan da suka zo wanke kai suke yi, manyan mata ne masu ji da class, Æ´aÆ´an manya, dan shop É—in bana yara bane, na manyan mata ne.

Shi kuwa Tga abin da kuka sani ne, kallo wannan ma babu wacce ta samu ya ɗaga idanu ya kalleta, dan shi bai ma san suna yi ba, ga fuskarsa tamkar ta shanu, ya wani murtuketa gam, babu alamar ya taɓa sanin menene murmushi ma, sak face ɗin Lion haka yake shi ma, abu ne da kuka rigada kuka sani.

Duk waɗan nan awannan da su Rimsha suka kwashe ana zuba masu zanen flowers na lalle mai bala'in kyau tare da gyaran gashi, duk yana tsaye bai ko motsa ba, kuma sam bai zauna ba, yana tsaye a matsayinsa na cikakken soja mai jini a jika, yana ta kula da su, dan Lion ya jaddada mashi a kan ya kula da su over, shi ne yasa yake ƙoƙarin jaddada hakan.

Sam Rimsha ta mance da cewa Lion baya son lalle, haka ta bari aka zuba mata zanensa ya fito reras, ya yi matukar kyau na wuce misali.

Ita gwaggo a tunaninta gabaÉ—aya TRIPLETS zasu zo a tare, shiyasa ta tattaro har da su Jehan É—in dukka dan ayi masu gyaran kai, bata san iya Lion ne kawai yake hanya ba.

Haka suka gama abin da za su yi, suka je shopping suka yi sayayya, Lion yasa Imran ya biya kuÉ—i ta hanyar yi wa masu shops É—in transfer, sannan suka nufi gida, sai murna Rimsha take zabawa, baki yaki rufuwa, an zuba mata lalle kam kamar ba gobe.

Sai da suka koma gida ta shiga bedroom É—in na Noorish É—in nata dan ta yi wanka ta yi sallar azzahar, a nan ne ta tuna cewa Noorish baya son lalle, nan take hankalinta ya yi mummunar tashi na wuce misali, wani irin tukukin bakin ciki ta ji ya taso mata, kullum tana damunshi a waya akan yazo ta yi kewarsa, ya taso yana zuwa kuma ta je ta yi abin da zai bakanta mashi rai, sam bata ji daÉ—in hakan ba. Zama ta yi a saman bed ta murji kukanta iya son ranta, sai da ta ji kanta ya fara yi mata ciwo ne ta hakura, ga kan nata ya sha gyara na gasken gaske kuwa, sai wani kyalli curly hair nata yake zubawa, kamar ka sace ta ku gudu, ta yi kyau ne har ta gaji da kyau, dole ma Noorish ya ruÉ—e idan ya zo ya ganta.

Bayan ta gama murzan kukan ne ta miƙe ta nufi toilet, wanka ta yi tare da fitowa ta shirya, sannan ta yi sallah kafin ta fita zuwa kitchen ta ɗebo abinci, ta dawo cikin bedroom ɗin nasa ta zauna ta fara cin abincin nata, suma su Jehan abincin suke ci a bedroom na gwaggo.

Bayan ta ci ta yi nak, sai ta hau gyara mashi bedroom É—in babu kama hannun yaro, da ta kammala sai ta rufe ko'ina tare da zuba mashi air freshener irin wanda yafi kauna, ta bulbula son ranta, tana kammalawa ta wuce bedroom É—in mummynta.

Babu kowa a cikin ɗakin, dan haka sai ta dawo bedroom na gwaggo. A nan ta samesu dukkansu, mummynta da gwaggo suna a zaune a saman bedside drawers dake gefe da gefen bed ɗin, ita kuma Brr Naurat tana zaune a saman bed ɗin, Jehan ta tada kai da cinyar Brr Naurat, ita kuma Akila tana kwance a gefe guda tana aikin latsa waya, sai sakin uban murmushi take yi, da alama ita da Heartbeat nata suke chatting, dan minti minti sai kuga ta turo baki alamar kalmar shagwaɓa ya turo mata, sai magana Brr Naurat take yi mata, amma ina hankalinta na'a kan wayar, sai da mummyn Rimsha ta miƙe ta kwace wayar, sannan ne ta farga ashe ma a cikin mutane take.

Rufe fuska da hannunta ta yi tana dariya kasa kasa. "Akila sarkin soyayya ba". Cewar mummyn Rimsha, ta yi maganar cikin zolaya........ Hmmm Mummyn Rimsha fa bata san cewa Rimshar tattabara ce uwar soyayya ba, dan bata san yanda take birkitawa General of the army's kuma ɗan takarar shugaban kasa a yanzu lissafi ba ne, duk ta susutar da bawan Allah, ya fita waje ya yi wa mutane zarra, idan ya dawo gida kuma ya cigaba da biyewa Rimsha ya zama kamar wani ƙaramin yaro, oh Rimsha duniya ne wlh, mum tana cewa Akila sarkin soyayya, ai ga sarkin soyayya kam nan ta fito daga cikinta.

"Ku bani hankulanku waje guda". Cewar Brr Naurat. Nutsuwa suka yi tare da tattare mata hankulansu, Rimsha dake a tsaye ma Brr ta ce tazo ta zauna, dama magana za'ayi a kanta ai, dan ita ce mijinta yake hanyar dawowa yau, ita za'ayiwa nasiha, su Jehan dai zasu ji nata ne kawai kafin azo yi masu nasu idan mazansu zasu dawo.

Shiru suka nutsu kamar ba su ba, da Brr Naurat da gwaggo ne suka fara yi masu nasiha mai ratsa zuciya ta sanya zuciya yin laushi, sai da suka gaya masu girman Allah, suka tausasa masu zuciya, sannan suka fara gaya masu menene miji ma first, kafin suka gaya masu hakkokin miji da yake a kansu, daga karshe suka ɗaura da zancen biyayya, kada su kuskura su ɗaga muryoyinsu ya fi na mazajensu sauti, yin hakan ya kansa mace ta shiga tsinuwar Mala'ikun Allah ta'ala, kome zai yi masu su daure kada su ɗaga mashi murya, Allah baya barci yana ganin komai da yake faruwa, su kula sosai da mazajensu, su kasance masu sanyasu farinciki na wuce misali, su yi masu duk abin da suke so matuƙar bai saɓawa Allah ba, koda su basu so, to su daure su yi mashi biyayya, ranar gobe kiya zasu samu kaso mai tsoka a wajen Allah, zasu shiga rahmar Ubangiji a lokacin da ubangijin al'arshi ya sauko da rana dai'dai kawunan mutane, to a wannan lokaci Allah zai sanyasu cikin karkashin inuwar al'arshinsa, dan haka su dage sosai, su jure su yi hakuri, duniya ba madawwama bace, lahira ita ce madawwamiya, dan haka su nemi madawwamiyarsu ta yi kyau, kada su biyewa duniya lokaci kaɗan yake a gareta.
Chapter 81 · 0% Book details